TENSION

922 59 0
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP

F.O.W

Vote@wattpad khairi_muhd

           32_33

makyn be samu dawowa ba sai bayan sallar isha'i a tunanin sa ta karanta sakon sa saboda haka yana expecting ganin chanji a tattare da ita.
   salamu alaikum
wa'alaikum salam

ta amsa masa sama2 saidai jikin sa ya mai sanyi ganin yanayin gidan da kuma ita kan ta matar gidan.

rabi'a me yake damun ki? kina hauka ne?

hauka ta tambaye sa ae ka fada mun kalma me sauki da dadin ji ae gwara ka fada mun kalma mafi muni a kan wannan.

wai ke me yake damun ki why are u doing all this.? me na miki all i know is that i love u wholehearthly me sa ba za ki repaying ba da kaunar da nake miki.

so? kauna? ni zan maka? ae kasan cewa na fi karfin ka ni bana son ka bana kaunar ka , wallahi zaman da nake da kai zaman dole ne da takura ka sauwaka min ni mutum daya nake so muhammad.

rabi'a ki mun shiru kina ji na ko idan kina haukan ki to ki daina sa wa da ni idan kina...

be yi aune ba ta cakumi kwalar sa ta ce makyn ahmad matukar kai din dan halak ne ka sauwaka mun ka sake ni! ka sake ni na ce.

mamaki da bacin rai suka kama makyn ya ji wani dum a kirjin sa yana jin wani irin bakin ciki, anya ko ba aljannu ne a kan yarinyar nan ba?

kokarin zaunar da ita yake a kan kujera ta ki fafur tana masa harara hade da zazzaga masa bala'i da ruwan rashin kunya kawai kallan ta ya tsayi.

wannan ba tarbiyar ki ba ce kuma ba halin ki ba ne kada ki dau akida da rayuwan da ba taki ba kin ji ko ki nutsu muyi magana.

da kyar ta zauna a kan hand din kujera tana hawayen takaici.

me sa ki ke so na sake ki?

saboda bana san zama da kai

to me sa?

saboda bana son ka

duk da yaji wani iri hakan ya daure ya kuma ce da ita mesa to ba kya so na?

saboda akwai wanda nake so nake kauna na kuma ma alkawarin kai na na saba dashi,na shaqu da shi,...

ok amma kin san hakan da kike haramun ne?

na sani shi yasa nake san ka sake ni na kuma gun sa.

murmushin takaici ya yi kawai ya najin ran sa na masa suya ya ce ok kin manta wanda kike so din yayi aure ko

eh na sani

kuma kanwar ki yake aure ko?

eh

to taya zaki aure sa in na sake ki?

ta masa shiru bata da amsa.

ae ko na sake ki ba aure a tsakanin ku matsawar tana da rai.

to naji kawai ni ka sake ni bana san ka.

mikewa yayi yana kallan sama ya ce zaki iya fadawa iyayen mu hakan?

zan iya!

ok shirya muje

to ta fada tana tashi da sauri harda hadawa da gudu2.

da sauri ya dau mukulin motar sa yay waje ya kulle kofar. tashin mota kawai taji ta fito da gudu tana buga kofar amma ta kasa budewa ta kulla a ranta idan ya dawo seta karta masa rashin mutunci da wulakanci.

  SANADI NEWhere stories live. Discover now