chapter 23

926 68 1
                                    

😭SANADI NE!😭

KHAIRAT UP

F.O.W

vote@wattpad khairi_muhd.


            23

"Da me ki ka dauka?"

"na dauka hajiya zata ce kar ka kuma mu'amala da kai ne."

"ya waro idanuwan sa waje amma dai baki da kirki,zaton da zaki mun kennan."

"hahaha,Allah baka hakuri nawan."

"uhm ok zan tafi sai anjima "

"tam mu jima lafiya ka gaida mum din mu."

"zata ji."

"haka ta koma cikin gida ta shiga dakin su tana cike da jindadi, ta fada kan gado."

"ke lafiya?"

"baza ki gane ba ae am so happy wallahi."

"da aka yi me?"

"yah muhd da hajiya sun daidaita kan su."

"masha Allah naji dadi kam."

"nima haka."

"ke wai haka kike san muhammad din nan?"

"ke yadda ba kya tsamani khady ina san sa sossai yadda zan iya fadawa cikin duhu idan ya bar ni i really adore him."

"to in fa ya yaudare ki? ko idanuwan ki basu gane miki daidai ba a kan abunda ki ke ganin shi ne daidai. Ni a gani na kina da yarda da wuri,kin maida hankalin ki a kan muhd sossai and naga kamar ya fara shiga alamuran rayuwar ki kin canja gaba daya."

"ta bata rai ta ce khady kada ki jawo abunda ze shiga tsakanin mu nida ke idan bazaki fadi alheri a kan tarraya ta da yah muhd ba ki yi mun shiru bana san bakin fata maimakon ki mun addu'a sai kina aibata mun masoyi na kada ki kuma."

"uhm ! rabi'a kennan na fada miki kin canja and kada ki bari soyayya ta rufe miki ido komai ki ka gani na rayuwa akwai SANADIN SA. ..."

"to ke ba kya ganin haduwa ta da yah muhd SANADI NE?"

"um kiyi hakuri na daina Allah ya sanya alheri"

"ta murmusa ko ke fa ?har na ji dadi."

"nan suka cigaba da hira a tsakanin su."

❣❣❣❣❣❣

"yadda yake motsa bakin sa zaka rantse cewa ba magana yake ba amma maganar yake yi a tsanake da nutsuwa cike da tauna harshe wajan magana da kuma auna dadin ta a gun wanda yake furtawa maganar."

"cike da gamsuwa ta murmusa masa hade da shafa kan sa tana jin wani shauqi dake tsakanin da da kuma uwa. a hankali ta ce um naji dadi sossai kuma ina muku addu'ar Allah ya sa albarka a al'amarin kuma saidai ina san kaje gun nas din anjima ku gama magana a tsakanin ku kaji ko?"

"insha Allah hakan za a yi hajiya zanje da magariba."

"to shi kennan na gode da wannan farin cikin da Allah yasa ka zamo silar samun sa a gare ni."

"Allah maka albarka makyn Allah ya baka masu maka biyayya kai ma"

"ameen"
"Da daddare ya shirya cikin wani yardi fari da aykn kalar  gold a jikin dinkin ya sa hula daidai ta tsaya masa cak a kan sumar sa. ya dau key din motar sa ya fito yana zuba kamshi tamkar wanda za shi liyafa. yana saukowa daga step aka kira wayar sa,ya dauka yana magana a tsanake be yi aune ba yaji ya ci karo da mutum a matukar kidime ya daga manyan idanuwan sa wanda suka kasance farare kal ya sauke su kan kyakyawar fuskarta ganin ta'asar da ta masa ya daga mata hankali ta gatsa harshen ta da kaga idanuwan ta kaga zallar tashin hankali a ciki. daga bayan ta taji muryar khady ta na ce ae wallahi sai na kama ki se kin biya ni... ta katse maganar ta ganin abunda ta aikata ai da gudu ta koma inda ta fito ita ma jikin ta na kyarma ta ce uhm ...am...em... ha...kayi hakuri ban sani ba wallahi am..."

"a hankali ya ja doguwar ajiyar zuciya yana jin wani iri,juyawa tayi zata gudu ya jawota ta fada jikin sa numfashin su na gauraya da na juna idanuwan su suka yi locking cikin na juna kusan minti hudu suna a haka ya hada ta da bango ga hannun sa da ya matse mata dantsen hannun ta taji zafi sossai tayi rau2 da idanuwan ta hawaye na neman hanyar fitowa ya dora dan yatsan sa a lebban sa alamun tayi shiru."

"dan Allah kayi hakuri zan wanke maka"

"ae da gudu ko baki fada ba sai kin wanke mun su tunda ku idan kuna shirmen ku ba kwa sanin me ku ke yi and ki tabbatar kin wanke mun fes wannan bakin ya fitar mun a kaya na "

"a hankali harshen ta na rawa ta ce to."

"jan ta yay da karfi ta ce awwn be ko kalleta ba ya hankada ta cikin bedroom din sa ta gama tsurewa."

"me ze kawo ta nan ta matsa ta hadiyi yawu makwat"

"a nutse ya juya ya fada wani gun a cikin dakin, wasu kayan ya dauko kal da su ya cire wadan can ya dunkunkune su ya fito ya wurga mata su a fuska ki wanke su da kyau."

"ita tama manta da abunda ya kawo ta dakin saboda ta shagala da kallan sa ganin yama fi dazu kyau a ranta ta ce wai shi mesa komai nasa daban ne."

"tsawa ya daka mata get out mayya kin kafe ni da idanuwa ta kurwata tafi karfin taki."

"bata ma san sanda ta ce masa *yayyan mayya* saida ta fada ta tuna wanda ta fadawa hakan."

"juyowa yayi ya kalle ta ya hade girar sama da kasa ya sha mur ya ce _OUT_ sum2 ta fita daga dakin da kayan tana tsaki ta kwace ma khadija bakin lalen a banza wannan dan zafin kan ya mata asarar sa.mtsw"

"dakin su ta koma tana kunkuni ta zauna ragawaf kan kujera ta na sakin tsaki."

"hajjajju ya kuka kare da ya makyn?"

"tsaki tay ta nuna mata rigar ta kuma ce wanke masa zan yi wai."

"haha Allah kara miki ae mugunta kika mun da kin yi hakuri in na sa kema na sa miki ke wutar ciki kika gudu ko ae gashi nan kin gani."

"to ni ban ma san ta inda zan fara wankin ba bakin lalle ne fa."

"ki zuba haifo ya jiku"

"Allah ko?"

"eh man kawai ayi haka in yaso kome tafanjamafanjam"

"suka sa dariya dukka hade da cewa lallai kam su wanki manya."

muje zuwa fan's

  SANADI NEWhere stories live. Discover now