BETRAYED!

848 61 2
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP

F.O.W

       37_38

        Saida hajia ta bi rabi daki daga baya ta kuma zaunar da ita ta fahimtar da ita dunia da matsayin karya ga mutum da yadda take da rage daraja a gun wadanda suke ganin girman ta.

ki fada mun gasklyar lamari? kada muzo muna dana sani i dnt want to lost trust on u kin ji?.

tayi wuki2 da idanuwan ta cike da fargaba kodai ta fada mata gaskiya.? no u are close to ur success ki bari ki auri muhd tukuna in yaso kowa ma ya juya miki baya. makyn ae be saki ki ba wawuya , ae ze sake ki dole dan yanzu yasan kin tsane shi kuma zaki iya komai a kan rabuwa da shi. hajiya me ribar da zan ci idan na muku karya? bayan kun san ba hali na bane karyar.

Allah ya sauwaka kada ki damu kin ji ? ki kwantar da hankalin ki kina gama idda ki saki jiki ki fadi wanda kike so insha ALLAH indai halin sa sun mun zan aura miki and ki kara hakuri.

haba hajiya me sa kike bani a kan abunda ba ke kika mun ba? kina sawa ina jin kunya ne fa.

murmushin karfin hali tayi kawai ta fita a dakin.

duk da zuciyan ta na gargadin ta a kan abunda take hakan be hana ta karfafa ma kanta gwiwa ba a kan cewa she can do it and she deserve muhd.

kasancewar fushin da iyayen sa suke da shi hakan besa sun damu da sanin inda yake ba ko halin da yake ciki bare ma su san yana ina.

haka aka yi wata biyu a cikin wannan lokacin kuma wani ikon Allah duk sanda zata kira sa baya dauka saboda yasan ba komai a tsakanin su. hakan na bata ma rabi rai dan bayan en gidan babu wanda yasan cewa rabi da makyn basa tare! hatta umman ta ma.

rabi ta lura da sauye2 a jikin ta dan ta kara kiba ga wani mugun kwadayi da take ji a koda yaushe sai dai ta kasa gane hakan saboda damuwan ta daya ne muhd yaki daga wayar ta kennan plan dinta ya tashi a banza ?.

tunda ta tashi take san cin wainar fulawa da kyar ta fita falo ta samu iya a kitchen suka gaisa ta ce mata iya dan Allah wainar fulawa zaki taimaka mun da ita in zan samu mandako ma zanai dadi , iya ta kalle ta tana maimaita maganar ta kare mata kallo tsaf tsohuwar ta murmusa tace angama me sunan hajja za a miki.

cikin kankanin lokaci ta gama data wainar fulawar ta kai mata sannan ta koma ta dau hijab a tsakar gida suka hadu ita da hajia.

ah a iya ina kike saurin zuwa?

kasuwa dan ban ga ta zama ba.

kasuwa kuma da kan ki? ina iro yaje mana.

ae sakon dan me sunan hajja ne saboda tana san cin mandako kuma bamu da kayan a kusa dan albasar mu da kulli babu .

to mandako hajjan?

eh fa

to a dawo lafiya bara na karasa ciki.

to .

    a falo ta same tana cin wainar fulawa ta ce to hajja me ake ci ne?

hajiya wainar fulawa

to a ci lafiya.

ta shige ciki.

ita hajiyar bata ma kawo wani batun ciki ba a ranta dan a tunanin ta ba abunda ya faru tsakanin yaran ganin basu san juna.
sau da dama tana kiran layin makyn dan jikinta ya mata sanyi wayan bata shiga , ya daina zuwa ya daina musu waya se yanzu take ganin rashin adalcin da aka masa na kin sauraran sa shi ma dan sun yi makahon alkalanci dan basu ji ta shi ba duk ta damu _dama ance tsakanin d'a da uwa sai Allah_.

sanye yake cikin wani mlik din yard yana ayki a laptop din sa ya tara kasunba wadda ta amshi fuskar ta, ya yi er kiba kuma yay haske duk wanda ya gan sa ze tunanin cewa bashi da wata damuwa ne amma kasan ransa yana cike da kewar hajiyar sa da kuma matar sa dan ita zuciya ae bata da 'kashi yana san kiran su yana tsoron abunda ze biyo baya koda yaushe yana tunanin mesa rab'a ta yi haka ta canja kyawawan hallayen ta zuwa munana yadda ta kasance ta iya shirga irin wannan karyar duk da ya dau fushi da ita wani bangare na zuciyar sa yana jin kaunar ta a ran sa kullum adduar sa ya samu rabi ta so shi dan kam shi yana kaunar ta da zuciya d'aya shi yasa ya bata lokaci ta sauka daga fushin da take dashi ko ta fada masu ainin magana idan ko ya gano cewa ba yin kanta bane zuga ta a ke dorata a hanya ake to ze koya wanda ya shiga rayuwan sa hankali se ya dau mataki.

❣❣❣❣❣❣

Wata uku da sati biyu ne wani abun mamaki ya faru a gidan hajiya amina.

       rabi ta sauko daga step tana jin wani irin jiri dama ta gama shiri ne zata gaida umman ta da hajja da abbie daga nan zata je ta fadawa mummy yadda abubuwa ke tafiya.

tunda ta sauko hajiya take bin ta da ido dan kuwa doguwar riga ce a jikin ta budaddiya amma hakan be hana cikin ta dagowa ba dan kadan ya mata kyau dan har wani haske ta kara.

          zo nan mama na

tsugunawa tay a gaban ta .

aa tashi daga tsuguno zo kusa dani ta nuna mata gefan ta.

hajja kina da damuwa ne?

aa hajiya banda damuwa fa me kika gani.

naga kin sauya ne

wallahi nima haka hajiya.

when kika ga al'adan ki last?

sai lokacin tayi dan jim kadan ta ce tun da muka yi aure da ya makyn.

wata uku kennan da en sati?

uhm

to mesa baki fada ba?

ae na manta ban da kula ba fa hajiya wallahi saboda dana daina dadi na dinga ji fa dan na huta da ciwon ciki

dariya ma ta bawa hajiya ita kam ta ce to jeki ran litinin zamu je asibiti a duba ki.

to hajiya Allah ya kaimu.

ameen ki gaida su kuma kar ki dade.

to da wuri zan dawo

youwa kuma ki kula kada ki fada ma umman ki da su hajja abunda ake ciki so nake sai na fada musu da kaina at the right time.

to.
Bata jima ba ta karasa gidan sedai har zata shiga gun umman ta tukuna ta fasa ta nufi part din mummy.

tay sallama ba a amsa mata ba hakan yasa kawai ta shiga gidan ko a falo bata samu kowa ba hakan yasa ta dan zauna kan kujera kusan minta hudu taji shiru harta samu ta na duba charts a wayar ta taji alamun kaman dariya daga dakin dake kusa da kitchen hakan ya bata daman mikewa duk da tana jin ta wani iri tamkar marar lafiya duk jikijm ta ya mata sanyi hakan nan gaban ta ke faduwa fat fat tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ta karasa jikin kofar sedai dakatawa tayi tana jin wasu irin maganganu da muryoyi ana shewa kuma ta hango mummy a tsakiya da aunty sahura kanwar mummy da wata kawar ta fadila.

hankalinta yay mugun tashi taji kanta ya wani sara mata bata iya motsawa daga gun ba tsabar kidima da ta yi hawaye ne kawai ke mata zarya a kumatun ta tana kuka.

d'akin aka bud'e kaduwa mummyn tayi ta dan zabura ta mike ta wayance *RABI'A* saukar yaushe? kin dade ne?.

kanta kawai take jijigawa tana ja da baya ta ma kasa magana a guje ta juya ta fita sedai bata karasa ba kafarta ta goce ta fada kan step din dake jikin kofar fita daga gidan wata iriyar kara ta saki wanda ya jawo hankalin mutanen gidan mummy na ganin haka ta koma ciki da sauri bata fito ba seda taga en gdn sun firfito snnan ta fito lokacin ta suma jini na bin kafarta tana dafe da cikinta.

a kidime aka dauke ta aka tafi asibiti da ita ana jimamin abun.

_naso na rubuta fiye da haka sedai hakan be samu ba ku maneji da wannan._

*teamsanadine#*

  SANADI NEWhere stories live. Discover now