chapter 8

1.1K 99 0
                                    

~😭SANADI NE😭~

~KHAIRAT UP~

~F.O.W~

~VOTE @ wattpad khairi_muhd~

  

           ~08~

"rabi'a ta rude tana jijjiga mahaifiyar ta tana tambayar me ya faru?"

"nima ban sani ba, kawai naga ta shigo a rude tana huci da ta mun wata tambaya kuma ta sume!"

"nan aka sata a mota aka yi asibiti da ita dake na kudi ne da gaggawa aka amshe su aka duba ta kawai ta firgita ne ta shiga shock amma nan da wasu en lokuta zata farka.!"

"kowa ya zauna jigum jiran tsamani sai a lokacin hajiya take wani hasashe wanda ta dade tana yin sa ta shiga fargaba lallai idan abunda take tunani ne ya faru to an tafka kuskure babba kuma an zalinci hauwa'u. hakan yasa ta mike tsam ta dau wayar ta waje ta fita ta kebe tana neman wata num."

"da farko wata baturiya ta dauka.
   _sir is ina meeting please call late!_

"mtsw ta saki tsaki ta ce  mata .
_ok tell him to call dix number back his sister has called._

"baturiyar ta ce
_yes ma'am i'll!_

"ta kashe wayar tana addu'oi a ranta yau zata ji takamaiman labarin umma da kuma waye mijinta."

"hour biyu umma tayi bata san wanda yake kanta ba. sai da magariba ta farka da salati a bakin ta. a hankali ta dinga bin en dakin da kallo tana san tuna abunda ya faru da ita dazun."

"hawaye ne suka saukar mata a fuska tana jin wani irin abu yana mata yawo a ranta ashe ba a banza take ma hajiya kallan sani ba to wai dama UMARU dan gata ne? me ya sa ya musu haka? me ribar sa na musu haka? yana ina? ya na raye yana rayuwar jindadi ko kuma ya mutu?"

"lallai yau za a tone ramin da ya dade a rufe."

"sannu umma! sannu!"

"idanun ta kawai tayi blinking tana jin wani iri a ranta. hakika kuka ma rahama ne!."

"likita aka kira ya kuma duba ta ya basu tabbacin ta warke dama damuwa ce da kuma firgici amma yanzu komai normal yake.suna iya ma tafiya gida!"

"koda suka koma gida bata nuna ma hajiya komi ba ."

"hajiya tana yake ta ce hauwa'u ki huta da safe mayi magana kina bukatr hutu yanzu."

"kai ta gyada mata."

"umma ki fada mun menene ya taba ki? me aka miki? shin banda ikon damuwa da damuwar ki umma na?"

"kanta ta shafa ta ce kar ki damu amsoshin tambayar ki lokacin bada su ya yi insha allah komai yazo karshe."

"umma ..."

"ki huta rabi'atu kin daina kukan maraici daga yau gobe zan fada miki komai na rayuwar mu!"

"dadi ya kama rabi tana murna ta ce allah ya kaimu da rai da lafiya."

"amin ki kwanta"

"to umma"

     ❣❣❣❣❣

"hajiya na lura kina da damuwa ki sanar dani koma menene?"

"hmm alhaji ina da damuwa kam ba er karama ba kuma, saboda an baro baya da kura abunda yake boye kuma yau za a  tone shi."

"ikon Allah amma me ke faruwa?"

"alhaji dama a kan hauwa'u ne"

"ohk umman yara?"

"eh"

"to to me ya faru ta miki wani abun ne?"

"ko daya sai ma mu da muka cutar da rayuwar ta muka zalince ta"

"subahanalahi garin yaya?"

"alhaji magana ce me tsawo wanda ni kaina ban san farkonta ba amma nasan karshenta..."

"kiran wayar ta ne ya dakatar da ita ta ga sunan wanda take nema tun da rana a kan wayar ta.
   UMAR"

"Ajiyar zuciya tayi ta dauka."

_umar_

_yaya dazu ance mun kin kira? ban samu sarari ba sai yanzu dana dawo gd_

_umar ka samu flight gobe ka biyo kazo 9ja it's urgent_

_lafiya yaya? wani abu?_

_eh babban abu ne ya faru kazo ka gani da idanka ka kuma jiye da kunnen ka_

_yaya gobe yayi kusa saina dau leave fa a gun aiki kuma ..._

_tunda sai kaji komai a waya to matar ka hauwa'u da ka gudu ka bari da er da aka haifa maka rabi'a sun zo garin nan neman ka har muka saba dasu_

_what tsaya yaya taya ma zata taho kano nema na bata san inda gidan mu yake ba?  ta haihu kuma? me ya dawo da ita?_

_kan ka ake ji nidai na fada maka tana gida na_

_yaya ki musu dabara mana ki maida ta garin su_

_umar kai wane irin mugu ne? mesa baka da tausayi da hankali? kana nufin mayaudari ne kai kasan ko hakkin ka a kansu?_

_yaya taya ma zan fara fada miki ba kala ta bace hauwa_

_kasan da haka ka aure ta? ka mata ciki?_

_gumi ya keto masa to yaya ya za ayi?_

_kai ka sani ni dai idan baka zo ba gobe to hajja zata san maganar nan dan zan kai mata su na fada mata matsayin su so think about it!_

_no zan yi kokarin zuwa kar ki fadawa hajja pls._

_dole zata sani saboda tasan hukuncin da zata yanke maka._

_yaya duk abin nan fa SANADI NE_

_yes SANDADI NE da kuma rainin wayo da yaudara irin ta maza ba_

_yaya ni fa dan'uwan ki ne mesa baza ki sideing dina ba?_

_saboda baka da gaskiya kai spirit din ka be taba tuhumar ka ba a kan abunda kayi ka auri mace, ta yarda da kai,ta maida kai miji ,ta daraja ka, ka gudu ka barta still tana maka addu'a me kyau tana kare ka tana cewa akwai dalilin da yasa ka tafi ko kuma baka da lafiya ne bata san a aibata ka amma kai umar ka yaudare ta wai she is nt ur type!_

_yaya lemme go and book the flight_

_tam_

"nan suka ajiye waya, "

"alhaji matar sa kawai yake kallo  dan ya kasa tsintar komai"

"aminatu kar ki fada mun umman rabi da rabi umar din mu suke nema? shi ne miji da uban da ya gudu ya bar matar sa da er sa?"

"kai ta gyada masa alamun eh shi ne."

"but why yayi haka? kuma when? and how?"

"alhaji ni kaina bn sani ba "

"allah ya kyauta."

"amin"


*to fa muje zuwa ku biyo er mutan ...dan jin sauran bayani da yadda za a warware mana asalin magana kuma me sanadin?*

*VOTE*

*COMMENT*

*SHARE*

  SANADI NEWhere stories live. Discover now