chapter 30

1K 69 2
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP

F.O.W

    vote @wattpad khairi_muhd

            30

kwana biyu dai makyn na jinyar rabi saidai akwai abunda ke damun sa duk abunda ake bata masa magana, bata kula sa, bata maida kai ga alamuran sa, idan magana ya mata se dai ta gyada kanta kawai , zata masa girki ta ajiye masa.

satin su daya da aure suka fara shirin komawa makaranta kasancewar zasu yi test da exams kuma an dan wuce su a lectures.

ran lahadi makyn ya zo ya same ta a dakin ta daga ita se towel, ta na shafa mai wajan karfe shidda da rabi tana niyan ma hanzartawa saboda tayi sallar magrib.

oh yi hakuri ya fada ya juya kaman ze fita , ya ce mata dama ki shirya zamu je unguwa kar ki damu da dora abinci."

"kai kawai ta gyada masa.

ya fice a sukwane idan da akwai abund ya tsana to shi ne rashin jin muryar ta amma ba komai time ne.

wata arab gwon ta dauko blue ta saka ta fesa turaruka masu sanyin kamshi ta dauko ribbom ta daure gashinta ya tsaya kyam a kanta tamkar wadda tay acuci maza , ta daura wani agogon gucci shi ma blue da dankunne blue , ta dauko wet lips ta dora a kan pink lips din ta sai ya zama tamkar tasa pink din jambaki, ta zizara kwalli hade da shafa powder light daidai kalar ta ,mayafin ta dauko ta yafa tayi rolling da shi wanda ya mata ainihin kyau ita kanta ta ma kanta kyau hakan yasa ta dau wayar ta, ta shiga camera ta dinga selfie da killer smile dinta.

yana jikin kofa yana kallan ta dariya ma ta bashi yadda take ta duban kyanta a madubi kuma hakika tayi kyau sossai da sossai har seda zuciyar sa ta raya masa da ya shiga dakin kai tsaye ya taya ta daukar hotan a wayar sa.duk da yasan abu ne me wuya amma ze daure tunda shi din namiji ne.

ganin sa tay kawai a gaban ta sanye da shadda blue light da aikin dark blue a jiki ya daura rolex hular sa me kyau da tsada damanga ita kanta tasan yayi kyau ainun wanda bata ma san ta shagala a kallan sa ba har se da ya hura mata iska a fuska tay firgit ta dauke kanta ta duka kasa. murmushi ya sauke mata hade da kamo waist din ta ya hada da nasa hakan yasa ta dago idanun ta da sauri ta kara musu girma ta hanyar zaro masa su daidai lokacin ya saki camerar sa ya dauke su a hoto kuma yay kyau kasancewar duk suna kallan junan su da ita da shi pic din ya bada irin wow din nan.

guda uku ya kara musu daga bisani ya ce muje ko saboda lokaci ta yi gaba a gun da takalmanta suke ta tsaya ta dauko blue din flat takalmi ta saka a ransa ya ce "flawless".

motar sa suka shiga suka tafi ya kunna wakar celendion yana bi a hankali wakar na ratsa shi. ita kam game ta kunna tana yi yayin da sanyin ac da kuma kamshin turaren su ya bada wani sanyin kamshi.

a wani resturent suka tsaya. wayar sa ya dauko ya kira wata number. ya kun karaso? ok muma ga mu nan a waje lemme park.

gyara parking dinsa yayi , ya ce mata ta fito.

jerawa suka yi tare ba karamin kyau da burge mutane suka yi ba.

yana hango su ya nufi inda suke suka zauna aka gagaisa mamaki ma rabi take ganin su nas, da deejat da mazajen su wato ma an kawo ta ne dan a fama mata ciwonta? rainin wayo da kyar ta saki fuska suka gaisa tana yaken dole. kowa yay odering din abinci aka kawo musu da lemuka da ruwa maru sanyi ga gasasasun kaji da nama ga hadadiyar fried rice, salad, da kuma shawarma aka cika musu table ana ta hira bayan sun gama cin abincin su ne makyn ya sa aka kawo ice cream a matsayin desert . cikin amaren da angwayen ya cika fam da abinci daga nan gun wasu kujeru suka je suka zauna ana ta hirar ya bayan rabuwa yadda su khadyjat suke ta hira abun su ne ya sosawa makyn rai ganin shi matar sa bata ma shi take ba hankalin ta du na kan muhd da nas idanta ya yi ja ya cika da hawaye ta mike da sauri ta ce excuse me! ta bar gun jikin wata mota ta tsaya ta saki kuka me karfi tana jin wani irin kishi na ciyo ta why zuciya me yasa zaki so wanda be dace da ke ba? me sa zaki so mijin kanwar ki? mesa kike kishi da ita?  why ? me sa? innalillahi wa ina illa hir raju'un dafa ta makyn yayi ta juyo tana digar hawaye ya ce me ya faru? mesa kike kuka? me aka miki? rabi anya kina tsoran ALLAH KUWA? ta maida idanun ta kan fuskarta bata fasa kukan ba. yes anya kin san me aure da darajar aure zan dau komai amma banda ganin kina dakon soyayyar wani a zuciyar ki duk abunda kike ina gani kuma na sani har halin ko in kulan da kike mun duk na daure na jure na shanye rabi'at ki daure ki manta da muhd ki so ni.

bazan iya ba bazan iya san ka ba ni zuciya ta wanin ka take so me sa ku ka kasa ganewa? me sa kuka ruguza mun rayuwa kuka cuce ni? mesa ? ni bana san ka kuma bazan taba kaunar ka... bata karasa ba ya sauke mata wasu maruka guda 2 a fuska hagu da dama wanda hausawa kan ce barin makauniya.
dafe kuncin ta tayi dan ko marin ya shige ta kuma in bata yi karya ba ba a taba mata irin marin ba a rayuwar ta ba tunda tazo duniya.

kin maida ni shashasha? ni sa'an wasan ki ne? kada kiga ina san ki kice zaki raina ni? ni nafi karfin ki wulakanta ni a kan so ni namiji ne namijin ma tsayayye duk ranar da kika kuma mun maganar wani wallahi sena miki fiye da haka na lallaba ki , na biki a sannu , na sa miki ido , na gwada hankalin ki, amma kin kasa saduda ki kwantar da hankalin ki mu zauna lafiya da zucia daya, kin kasa bani dama na nuna miki tawa salan kaunar fine na ji na yarda i dnt care again.Ya wuce fuu kamar iska ciki ya koma a zaffafe ran sa na masa kuna ya bi su da wani irin lallatacan kallo tamkar su ne masu laifin ya dauko wallet din kudin sa ya ajiye musu kudi ya suri mukulin motar sa ya fice tamkar iska.

kowa ya koma kallan kowa.

a wajen da ya barta ya dawo ya same ta ya dak mata tsawa wuce muje da rawar jiki ta tafi ta bisa ya bude mata ta shiga.

a fusace yaja motar da karfi ya halba motar kan titi.

kuka take wiwi ya daka mata wata tsawar idan baki rufe mun baki ba saina watsaki waje daga cikin motar nan stupid ni zaki nunawa danyan kai, ni zaki tozarta? in kin so ni ba kya kaunar Allah da annabi.

ay seda rabi tay dana sanin furucin ta dan taga fushi irin wanda bata taba gani ba a rayuwar ta kuma bata taba zaton makyn mafad'aci ba ne se yau seta tsuke bakin ta , ta daina kukan sai hawaye dj take kawai.

zuciyar sa banda tafasa ba abunda take ransa gaba daya a dagule yake wani irin tukuki yake ji a ran sa ya ma rasa a ina yake tamkar ba a duniyar yake ba haka yake ji.

yana tsayawa ya ce OUT da karfi jikin ta na rawa ta bude ta fita dan tsoran sa ma take ji gani take ze iya mata dukan tsiya.

tana fita ya saki wani irin kuka a kan sitiyarin kukan da ya manta ma yadda ake yin sa kalma daya ke masa yawo a rai bana san ka bana kaunar ka wanin ka nake so ya doka hannun sa kan sitiyarin da karfi.
me sa ba kya sona rabi? me aibuna? da me muhd ya fini? me sa? me na miki? da kin san irin san da nake miki da baki mun haka ba a rayuwa rabi'atu why? ina san ki , ina kaunar ki, ina kishin ki, ina san kulawar ki amma... kusan hour guda yay a motar ya kasa tabuka komai yama kasa komawa ciki dan in ba saukowa yay ba ze iya mata duka.

tana shiga ta fada kan kujera ta cure gu daya ta saki kuka tana jin haushin kanta da tasan bata kyauta ba damuwarta daya kar ya ma kan sa lahani haka take tunani lallai zuciya bata da kashi.

kamar a zabure shi ya mike ya fito ya dubi hannun sa ya ce i slapped her  ya doka hannun jikin glass din mudubin motar sa. ji ka ke tass jini na zuba a hannun.

ciki ya nufa ya na me jin haushin kan sa

yadda taga hannun seda ta tsorata ta rude jikin ta na rawa ta mike hade da rufe bakin ta tana kuka...

  SANADI NEWhere stories live. Discover now