chapter 10

1.2K 77 1
                                    

😭SANADI NE😭

KHAIRAT UP

F.O.W

votn@wattpad khairi_muhd

       *_shafin naki ne asy khalil me ...🤣 an baki kyauta._*

            10

   _umma dama kin san shi? waye shi?_

_hawaye daya na bin daya a fuskar umman ta ce rabi wannan shi ne wanda na yarda da shi,na bashi lokaci na da rayuwa ta ashe mayaudari ne kin dade kina tambaya ta mahaifin ki._

_haka ne um...m...a kadai ki ce mun wannan shi ne mahaifina._

_hakkun umar shi ne mahaifin ki wanda ya guje mu wanda be san da ke ba ma a duniya._

_innalillahi wa inna illahir raju'un ta dinga maimaitawa ta dafe kirjin ta ya salam me ke faruwa dani? murnar ganin mahaifina zan yi ko kuma kuka?_

_daddy wai me take fada? ka san su dama?_

_nasreen it's a long story_

_hajiya ta ce dasu kuyi hakuri ku zauna tukuna muyi magana a tsanake._

_haka en gida gaba daya suka zauna yayin da hajiya ta ce hakika umar yayi ba daidai ba amma ina neman alfarmar a yi abun nan cikin lumana da fahimtar juna._

_daddyn londan ya fara da cewa..._

     ASALIN LABARI!

*Mahaifin mu alhaji muhammad nura dan kasuwa ne yana harkar kasuwanci ta ko wanne fanni kuma yana da nasibi a kan kasuwancin. gashi dan boko kuma proffesar ne a jami'ar bayero.kuma yana da ilimi na addini.asalin sa dan garin agadz ne sedai zama ya dawo da iyayen sa garin kano.dan ko a garin aka haife sa da kannen sa mata guda biyu namiji daya. (aunty zainab,aunty asiya,aunty maryam sai baffan mu surajo. mahaifina ya je garin su wani lokaci tare da mahaifin sa wanda ake kira abiy a nan ya hada shi aure da er aminin sa saboda shi ne babba a gidan. sunan mahaifiyar mu (RABI'A) Allah ya zuba mata kyau ga ilimi mace me nagarta da kirki da sanin ya kamata bata daukan raini da wulakancin kowa daka yi zata tsawatar maka ko waye kai hakan yasa kishiyar ta (zaliha) bata mata wargi dan hajjar mu na mata kwarjini.mu goma sha daya ne a gun mahaifin mu. en dakin mu mu biyar ne (yaya amina,yaya idris,yaya aysha,yaya mubarak,seni karamun su kuma mara jin su. a daya dakin su shidada ne duk mata ne (yaya rukkaya,yaya abida,yaya hafsa,umaima,asma'u,habiba) hakan be ma ummi dadi ba ganin ya'yanta duk mata ne duk da haka gidan mu be rabu ba kan mu a hade yake kasancewar hajja ta jajirce ta tsaya akan gidan da kyau.yayuna duk suka yi aure ya zama ni kadai ne a gaban su sai mahaifina ya dauki san duniya ya dora mun ni ne party,clubing,san mata,sedai ban taba yin zina dasu ba ashe ummi ce ta mun asiri na kangare saboda ta kasa samun galaba akan en uwana sai a kaina ga gatan da kowa ke nuna mun.hajja ta na jin takaicin wannan hali nawa da kyar na gama master's dina.a lokacin da na samu na hada karatuna sai hajja ta bawa mahaifina shawarar ya mun aure kila na nutsu dan har taba na soma sha. haka ummi tay ruwa tay tsaki ta hadani da er yarta (maimuna)uwargida na kennan da farko ashe sata tayi ta aure ni ta rabani da gidan mu da dangina na kuma zama abun ki ga kowa sai su sa na sake ta.ni kuma ina santa shekarar mu daya muka samu rabo wato khusam (NURA) ummi tay ta masifa a kan me zata bari mu haihu tare ta dai bata hakuri ta kuma fada mata ita fa tana san mijin ta gaskiya ta fasa deal din duka ne kawai bata yi wa maimuna ba sai ta nuna mata ba komai gun malaminta ta koma ta ce a mun asiri kawai na bar garin gaba daya na ji na tsani garin da dangina da kowa nawa na kowa rayuwar wahala da kaskanci kuma en gidan suma su tsane ni su manta dani a daina tunawa dani. yace an gama ya bada magani ya kuma ce a bani a ruwa ko lemo na sha har na tsawan kwana uku to fa zata ga yadda ayki ze ci. haka ko akai a lemon da nake sha take zuba mun da kanta sai ta shigo bangare na dana dawo har tsawn lokacin da aka yanke mata.washe gari na bar gida na hada kaya na na kuma dau kudi na yi wa en gida tatas na ce ba ruwa na da kowa kar wanda ya neme ni suma basu hanani ba.Haka na dau mota ta na tafi katsina na sauka a garin bugaji. to kunji SANADIN NE ya rabo ni da gida.*
*a garin bugaji na sauka a gidan me gari aka mun tarba me kyau sannan ya tambaye ni asali na niko na sharara masa karya. nan ya ban daki a wajen gidan sa washe gari aka kaing wata sakandari aka bani aikin malanta englishi. SANADIN HADUWA TA DA HAUWA'U kennan. makarantar da nake koyarwa ita din daliba ta ce me kwazo. a lokacin ma na manta da wata mata ta da wani nawa na zama marayan karfi da yaji ba wanda na damu da nd tuna ko na kula .*
_ya dan dakata da bayanin sa yana kallan yayar sa da take hawaye da sauran en gun da suke hawaye duk sai yaji ya kasa cigaba da bada labarin ya sauke ganin sa kasa yay shiru cikin sarkewar murya ya ce hauwa'u ki karasa.dan sai kin fi kowa iya fadar sanadin auren mu nida ke._

_duk da jikin ta ya mutu hakan be hana ta kasa magana ba sai kuma tausayin sa ya kamata da kuma tunanin dama ashe yana da mata harda da? gaskiya ne kishiyar uwa ba uwa ba ce naka sai naka._

*ni suna na HAUWA'U MUSTAPHA haifafiyar garin katsina a kauyen bugaji mahaifina madinki ne mu biyu ne rak a gun iyayen mu daga wana malam mamman sai ni duk da bamu da hali hakan be sa mun nemi wani abu mun rasa ba dan innar mu har aikatau take dan ta ciyar damu me kyau. kuma ina zuwa makaranta arabi da boko.yaya na malam mamam yana mugun kaunata yana ji dani. mahaifi na ya kai yaya na almajiran ta a cikin garin katsina ina da ya haddato alqurani me girma da kuma sauran littatafai. kuma ya gada sana'ar dinki a gun mahaifin mu. ina da aji uku a firamari mahaifiya ta ta rasu ba ciwo ba komai kawai wa'adi yayi. mun yi kukan rashi ni da wana da mahaifina. yaya na da shekara ashirin da bakwai ne a lokacin sai baba na ya matsa masa kan yay aure shi kuma yace ya bar masa zabi haka ya samu aminin sa mal.nazifi ya ce masa ya na neman mata wa dan wajan sa mal.nazifi ya ce ga er guri na maryo na bashi halak malak su zo su tatauna a tsakanin su . fatan mu Allah ya sanya alheri. haka babana ya fada masa yadda suka yi da aminin sa ba a dau lokaci ba aka gama komai aka kawo amarya dakin inna aka gyara mata aka zuba mata jeren ta da kayan daki ni kuma na koma dakin tsakar gida kusa da kofar fita dake gidan kauye fili fetal katoto me dakuna biyu a ciki da bandaki daya mara rufi da tsakar gida ba kitchen dama se dai ayi a wannan filin. dakin yaya kuma da ke waje a soro sai baba na ya koma ciki. mairo irin matan nan mafada ta abu kadan ta dinga mita da jaraba kenan da bala'i ga habaici. ni dai bana kula ta kuma ina taya ta aiki bata taba ce mun kaza na ce aa ba sai dai to. dan ni bana san damuwa ko kadan kuma bana san fada ko a dinga cacar baki dani ni sai na wuni ma ban yi magana ba ina da sanyi sossai. kawa ta daya ce talatuwa wanda muna gama firamari aka mata aure ta tare a gidan ta da ke funtuwa. dga ita ban kuma yin kawa ba. shekarar su yaya biyu da aure mairo ta haifi dan ta namiji sedai kwanan sa uku ya koma.lokacin ina aji daya a sakandiri wanda wana ya tsaya tsayin daka na cigaba.a shekarar baba na yay tafiya a hanyar su ta dawowa yay hatsari nan muka zama marayu gaba da baya. komai wana yake mun ya dauken komai duk da cewa matar sa na jin haushin hakan sau nawa ta so a mun aure yaki ya ce kulu karatu zata yi. to ta ga karshe biran da takardar ma ta tsofe a gidan ka jika ka sha.*
*a wannan lokacin ne umaru ya fara koyar wa a makarantar mu yana koya mana englishi.dan gayu ne na gaske ga iya koyar wa yana da barkwanci da en matan makarantar musaman ma en manyan ajin ss,2,3 ni ina js 3,lokacin koda ya shigo yi mana darasi hankali kawai nake maida wa in ya gama na yi gum ba wadda nake kulawa harkar gaba na kawai nake yi ni kam.shi kuma ashe yana lura dani kuma na burge sa dan bana masa cusa kai hasali ma kallo be ishe ni ba. baya gabana hakan ya dada sawa ya ji wani abu na fisgar sa gare ni. ashe yana lura da takuna daga makaranta se gida bana yawo ko wasan da ake bana yi ba saurayin da nake kulawa duk da ina da mane ma.se da ya gama nazarta ta tsaf sannan wata rana ya tsaida ni da aka tashi daga makaranta na tsorata na dauka ma ko wani laifi na masa na tsure ina tsugune a gaban sa ban ce masa uffan ba sai ma idanuwa na da suka cika taf da hawaye suna shirin zubowa.*
*_hey hauwa me aka miki zaki kuka? kinga magana zan miki dama_*

*na kuma tsurewa ya akay yasan suna na? ba amsa sai nay shiru!*

_muje zuwa!_
_manage!_

  SANADI NEWhere stories live. Discover now