A abuja wata iriyar rayuwa suke yi me cike da so da kauna ga kwanciyr hankali, zazaffan so yake nuna mata da kulawa ita da cikinta.
Se lokacin ta tabbatar da cewa ya nzu ne ta fara soyayya lokacin da ta yi ba komai tayi ba shaquwa ce kawai.
Mummy na komawa gida ta fara fadan karya da gaskiya wa mahaifin su , nan take ya kira umar ya na tambayan meya faru?
Yaso ya boye masa sedai tsohon ya karyar masa da zuciya ta hanyr rokon sa ya fada masa gaskiya in har da gaske ne yana ganin girman sa da ganin sa a matsayin mahaifib sa shima kamar yadda yake ganin abbie.
Nan ya labarta masa komai hade da bashi hakuri cewa ya gaji ne da abubuwan da take masa dama saboda su ne yake raga mata yanzu kuma ya gaji dan abun ya koma kan ya'yan sa.
Nagode omar Allah ya maka albarka, ka yi hakuri ae shekara da shekaru nagode.
Nan suka ajiye wayar.
Hajiyarta ta ce , alhaji me ya faru?
Gata nan da girmanta ta zabi zaman zawarci ta ki zaman gidan mijinta nidai nasan tarbiyar ku ce wannan ba tawa ba ki zauna, ga ki ga uwarki da ubanki kuma wallahi keda jindadi kun raba hanya wallahi,mts shashasha kawai wadda bata san darajar kanta ba.
Hajiya ta bishi da kallo ta tabe baki saboda ya fada maka karya ne ka hau ka zauna a kai kake ta fifiko da tinkaho a kai lallai aiki ya same ka ke saki ranki kinji nan gidan uban ki ne me ake da wani omaru, zaki samu wanda ya fishi arxiki ma.
Tana kuka tace hajiya ina san omaru ina san yarana hajiya da girmana yau wai nike zawarci hajiya ki duba lamarin nan.
Hajiyar ta bita da kallon mamaki, ta mike se ki koma ae marar zuciya kawai in ya'yan kine ai zasu biyo ki dole basu usa su canja ki ba ki ma kwantar d hankalin ki.
Ita kadai tasan irin san da take ma omar Allah ya isa hajiya amina da rabi tsinannu se Allah ya kamaku alhakin aurena da kuka kashe mun.
**********************
Khusam sanda mummy ta kirasa gidan su yayi mamaki nan ya samu amal ita ma da tritsesen ciki a gaban ta.
Sister me ciki
Ta zumbura masa baki ni ko?
Eh din ke man karya nayi miki ne?
Ta yamutsa fuska.
Ina mummyn take?
Uhm tana cikin dakinta tana zuwa wai.
Granny fa?
Ta je part din grandpa.
Oh su granny manya masu miji
Suka sa dariya dukkan su.
Mummy ta fito suka gaisa.
Ta sauke ajiyan zuciya ta ce kun gsn ni a nan ko.
Eh mummy lafiya ko?
Uhm ina fa lafiya an mun bakin ciki an rabani da gidan aurena da mijina.
Subahanallahi, mummy me kike nufi ban gane ba?
Ta soma hawayen karya tana zaro maganganu ae kishiyata da diyarta da kuma yar baban ku amina sun kashe mini aure jiya.
Innallilahi wa inna illahir raju'un amal da khusam suke maimaitawa.
Mummy mutuwar aure kuma.
Eh amal
Meya sa?
Hassada mana amal.
Hassada ta maimaita kalmar
Eh hasada yay dai mummyn ku ta dawo bazawar ta fashe da kuka.
Shi dai khusam ya kasa ma magana mamaki yake yi kawai.
To mummy ALLAH ya kiyaye ya sa hakan shi yafi alheri.
Ta bude baki alheri khusam na shiga uku dan uban ka dama kaima dan adawata ne, baka kaunar zamana da uban ku to kuje na yade ma hauwa ku
Mummy me zance to? Sanda muke miki fada ba kya gani da kin bi umma da zaman lafiya da kun zauna lafiya muma da hankalin mu ya fi kwanciya amma ki ka ki bayan ita da zuciya daya take zaune da ke
Ubanka na ce khusam tashi tashi maza ka bar mun gidan ubana ai bana uban ka bane nagode tashi kaje duk abunda nake yi a kansu waye nake yi? Ba akan ku bane ba gata nake muku amma ba kwa gani.
Mummy kiyi hakuri kar ki fushi dani ba ina nufin bata miki rai bane ba aa ina nusar dake ne, in dai akan mu kika bata da mijin ki to muna baki hakuri mu bamu ce ana cutar mu ba daidai gwargwado daddy yana mana yana nuna mana kauna, se...
Khusam nace ka tashi ka tafi ko?
Ya mike yana kade rigarsa shi kennan mummy se anjima zan dawo miki da daddare sannan kin huce.
Anki a huce din dan uban ka bszan huce ba, shi dai fita yayi ya na dariya kicibis suka yi da grannyn shi.
Ah a megidana na kaina ina zuwa?
Gidana zani
To daga zuwa
Ai na dade kuma masu gidab sun koreni.
Ah kun raba halin kennan?
Ya kama haba halin me?
Ai nasan ka da wa'azi ne
Dariya yayi yace uhm lallai ma granny fadan gaskiya ai ba wa'azi bane ba.
Zanje gun grandpa naga kin samu kin barshi shi kadai bara naje mu gana
Se anjima
To se anjima.
Kema bayan uban naki zaki bi?
Uhm uhm ni ban ce komai ba.
Ta tsuke bakin ta bayan tace better.

YOU ARE READING
SANADI NE
Romancelabari ne a kan marainiya wadda mijinta ya gudu ya barta da ciki, har tsawan shekaru goma sha biyar da en doriya... keep following me.