chapter 12

1.2K 82 0
                                    

😭SANADI NE😭

KHAIRAT UP

F.O.W

Vote@wattpad khairi_muhd

             12

"umma mu tafi gidan mu umma ki manta da shi dan shi ba adali bane baya san mu saboda mu ba en gayu bane ba mu en kauye ne! mu koma cikin en kauye en uwan mu dama bamu sa zaman birni a ka ba dama inna mairo ta fadi gaskiya da take cewa guduwa yayi ya bar mu da halin mu ba wani uzuri da ya same sa. umma daga yau kin daina kuka a kan shi nima na daina tambayar sa muyi rayuwar mu daga ni sai ke sai baffa nah."

"umma ta shafa kan  rabi ta share hawayen ta ta ce ba komai duniya ce rayuwa ce allah yana tare da masu hakuri."

"can falo kuwa nasreen ce ta kafe daddyn ta da idanuwan ta da kyar ta ce masa daddy dama muna da er uwa? dama ka taba aure? saboda me ka gudu ka bar su? daddy mu muna tunanin daddyn mu good man ne me san iyalin shi me adalci ashe..."

"hajiya ta daka mata tsawa shut up nasreen!"

"oh  am sorry, na manta fadar gaskiya laifi ne kuyi hakuri"

"hajiya ta ce umar me mafita?"

"yaya ina san diyata kuma ban yi tunanin cewa an haife ta ba kar ta tafi ta barni ki tsaida ta dan Allah zan yi making up akan abunda na mata zan bata time dina da kulawa ta da soyayya ta kar ki bari ta tafi"

"umar bazan iya hanasu tafiya ba saboda suna cikin fushi yanzu ka kyale su suje daga baya zan koma na lallaba su na san sun sauko daga fushin in yaso ko hajja ce se muje da ita nasan zata san yadda zata yi."

"su tafi fa kika ce kin ji abunda ta fada fa na mutu a gurin ta wai."

"duk fushi ne ka kwantar da hankalin ka zamu samu solution."

"shi kennan!"
"dakin su khadijat ta raka nasreen ta zauna a kan gwiwowin ta tana hawaye ta dafa hannun rabi tana kuka"
     _tun lokacin da na ga hotan ki a wayar yah na naji ina matukar kaunar ki kika shiga raina lokaci daya ki ka mamaye ni ashe saboda jini guda ne yake yawo a jikin mu ,ni ban san me step sister ba ko step mother but ni nasan muhimancin reletionship dan Allah kiyi hakuri kar ki tafi ki barni kullum ina jin ina ma nima ina da ya kamar yadda khadyjat take da aunty ayshat ashe2 ban sani ba ina da beautiful sister with pure heart,and cool nature! pls be with us.😭_

   "tausayin er'uwar ta ya kamata ko ba komai ba ruwanta da abinda mahaifin ta ya mata da mahaifiyarta kuma ita sheda ce nasreen bata kyamace ta bah wasu hawaye suka zubo mata taji wani abu ya tsaya mata yanzu fa KHUSAM dinta WANTA ne kuma UBAN SU daya ta lumshe idanun ta kawai ta rungume er'uwar ta suka saki kukan gaba daya."

       "hajiya ta shigo ta ce umman yara ku fito muje drivern ya karaso."

       "to hajiya gamu nan"

"sister zan biku nima"

"kai kawai ta gyada mata"

"aka fitar da kayan su aka sa a booth haka ma nasreen dan daru ta tada seta bisu she dnt care ko a daji sistern ta take zata zauna kamar yadda sistern ta ita ma ta rayu dasu."

"duk abunda ake umar na jikin taga yana kallan su yana ji kaman ya bisu amma ba hali yayar ta hana sa."

    "rabi zata shiga mota ta hango mahaifin ta suka ma juna kuri da ido,tay maza ta sauke ganin ta dan zata iya karaya motar ta shige ta kulle."

      "tafiya ce aka yi ta kamar kurame ba yadda aka tsara ta ba. kowa da abunda yake tsarawa a ransa kowa da damuwan sa ."

     "da yamma suka sauka a garin su rabi, wanda su kan su en garin se ya canja musu a haka suka karasa gidan su. malam mamman na waje a kan tabarma ya ga mota ta doso kofar gidan sa da mamaki ya ma motar kuri,ganin da gaske nan suka doso se ya mike ya tsaya a tsaye yana jiran yaga su waye."

"motar na  tsayawa yaga kanwar sa da diyarta wani dadi ya ziyarci zuciyar sa ya karasa da sauri"

"lale lale kulu, rabi, ku ne? ashe dama ina da rabon kuma ganin ku a duniya? "

"yaya ya gidan? "

"alhamdulilahi!"

"mu shiga daga ciki muna tare da baki ne"

"to to bismillah muje"

"ya musu iso har cikin gidan."

"mairo ta yi shara gidan fes kuma dama tsafta akidar mairo ce ita kanta a tsaftace take  tana hura wuta bayan ta kuma da goyo taji sallama."

"juyawa tayi ta amsa!"

"ah ah ah lale kulu, rabi yau kune? marhaba ku shigo mutanen birni."

"tabarma ta shimfida musu katuwa aka ayka yaro ya siyo pure water me sany!."

"nan kulu ta fadawa yayan ta taimakon da su hajiya suka mata.da kuma cewa en'uwan umaru ne babbar yar sa ce ma wannan."

"cike da mamaki ya ce to madala abu yayi kyau kam da fatan komai lafiya?"

"lafiya lau."

"wannan ma kanwar rabi ce "

"ayyo inji mairo suna kama kam ina shi umarun?"

"a nan ne tay shiru ta kasa bada amsa"

"sai malam ne ya ce sa huta ko?"

"eh kuma haka ne"

"umma tace yaya an samu rabo ashe"

"wallahi shekarar da ta wuce muka samu me sunan malam(mahaifin su hauwa)"

"allah ya raya shi"

"amin"

"umma da kanta ta tashi ta dora ma hajiya ruwan wanka tayi suma duk suka yi."

"ta kuma tuka musu tuwan shinkafa da miyar kubewa danya."

"ayko suka ci dakin kulu aka gyara tas aka sa turaren wuta yana kamshi a nan en birni suka kwana!"

  SANADI NEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt