chapter 11

1.1K 86 0
                                    

😭SANADI NE😭

KHAIRAT UP

F.O.W

vote@wattpad khairi_muhd

 

     _*shafin naku ne khairat up nvls 1,2*_


                   11

*malam kayi hakuri in har wani laifi na maka dan allah an tashi kuma kowa ya tafi gida nasan yaya tana jira na zan taya ta aiki ko da debo ruwa ne da yo icce be kamata na tsaya daga ni se kai ba nan ba birni bane kuma ba mutumci bane ta karasa hade da sauke ajiyar zuciya!*

*hakika ta na da nutsuwa wanda ya sa yaji ta masa a tunanin sa ko wani feelings ne kaf en matan da yake kulawa a garin basu da kamun kai da nutsuwa ko kadan wata ma har gunsa take zuwa da kanta wasu a hanya...*

_ta katse masa tunanin sa ta hanyar cewa_

*malam in tafi?*

*am yes jeki zan zo gidanku anjima. kaman ta ce a ina kasan gidan namu? ita dai mamaki malam umar yake bata sossai ta dinga tsaki haka taje gida!*

      *ke kuma a ina kika tsaya? um ina makaranta ne malamin mu ne ya tsaida mu. kaman ta tuhume ta sai kuma ta fasa ta ce se ki gyara gun can ki zo ki debo ruwa ki kuma dawo ki ci abinci wanki zaki mun yau .baiwar Allah to ta fada kawai ta yi shara da wanke2n safe da na aykn rana da akay ta dau bokiti ta tafi debo ruwa! a hanyar ta na dawowa malam umar ya dakatar da ita duk da ta firgita a ranta tace wae me yake nufi dani ne? ya fara gundurata wallahi. hauwa kulu me tagwayen suna kawo ruwan na daukan miki ba girman ki bane ina garin nan! mamaki ya cikata ta ce nagode amma mutane zasu yi magana kuma kai malami na ne.no ae ni na miki tayin kuma ra'ayi na ne kina da kamala kin gane ko? zata yi gaba saboda yana bata mata lokaci ya sha gaban ta haba ke kwa? me haka? ya dafa bokitin ta sakar mara da sauri sai yay murmushi. tare suka jera suka tafi yayin da kunya ta kamata ga mutane sun dame ta da kallo duk inda suka wuce se a kalle su duk ta tsargu ta tsure. haka suka je gidan su a kofar gida taga yayanta cikin taya bata kululu ga mamakin ta sai taji yayan ta na fadin madala mal.umaru ne?sai na datsi harshe na hade da runtse ido na nace kai wannan anya mutum ne bokiti ya miko mun ya koma gun yaya suka yi musabaha ya zauna kan tabarma.*

_hmm!dake ita zuciya tana san me kyautata mata cikin lokaci kalilan umaru ya sace zuciyata da dadin bakin sa da kulawar sa da kirkin sa da girmama dangina da yake yi hatta mata ya daina tsokanar su muka shaku sossai be taba fada mun komai a game dashi ba ban taba tambayar sa ba ni kuma!._

        _saida muka dauke shekara guda ni da umaru muna soyayya ya nemi aure na a gun en uwan baba na ganin me gari ne ya tsaya masa sai aka rasa me tambayar en uwan umaru! duk da masifa da bala'in da mairo ta dinga yi na cewa ita bata yarda ba da auran nan aure babu dangi, ba asali, ba a san shi ba yayana ya kwantar mata da hankali cewa me gari yasan shi kuma ya yarda dashi haka aka sa bikin mu wata biyu.komai an mun daidai ni gidana daki daya ne katotn da bandaki a waje da tsakar gida da zaure duk me gari ne ya bashi dan ya dauke shi a matsayin d'a sun shaku sossai. umaru mutum ne me iya kalami da haka ya sace zuciyoyin mu muka aminta da shi, yana da kulawa, da kwantar da kai da lallama baya fushi ga barkwanci da kyauta._

_duk da kalubale da na fuskanta a gida da waje na auran umaru hakan be hana zuciyata kaunar sa ba da zuciya daya wasu suce saboda kyau na aure sa wasu saboda kudi wasu saboda yana da mota na manta bay da asali ni ko saboda Allah nake san sa nake kaunar sa na yarda dashi wanda duk shi ne ya koya mun hakan.na yi masa mugun sabo da yarda duk da ana kawo mun maganganu a kan sa na kule2n en matan garin amma ban taba yarda ba ko na masa maganar makaranta ko dama na daina zuwa.wata na biyu na samu ciki wanda bana mantawa wata rana dadaddare muna hira dashi yake ce mun in na haifi mace sunan maman sa ze sa RABI'A a karo na farko da naji yay maganan dangin sa kennan. sai na ce masa kai ko a wane gari ka ke? yay murmushi yace kano kuma en uwana da iyayen duk suna nan da ran su. inda rabo zan hadaku in babu kuma...ya mike ya ce ina zuwa bari naje gun me gari dawo haka muka rabu nida shi_

    *sai umaru ya dora da cewa*

_da na fita daga gidan sena ji ina jin wani iri a zuciyata naji ni sakayau kamar bani ba duk wani nauyi na raina ya sauka kawai hajjata nake san gani. haka na je gun me gari na mika gaisuwa ta a gare shi, na fada masa ko ni waye kuma dan waye da adrishin gidan mu. yay dariya yana tsokanata ya ce yau kuma ka ga dama ka fada mun kai waye? dama na dade da sanin kai ba maraya bane kuma kai dan gata ne bazan matsa maka ka fada mun abunda yasa ka guji garin ku da gidan ku ba amma ina so ka sani ita duniya makaranta ce ko me yay zafi maganin sa Allah kuma Allah yna tare da masu hakuri kayi gagawar kowawa ka nemi yafiyar iyayen ka a kan daga musu hankali da kai na barin gida. ita kuma hauwa ka rike ta amana da gaskiya nasiha ce nake maka. nagode malam nagode haka muka rabu da shi._

    _da na fito se nake tunani ya ma aka yi na yarda nay aure? me aka mun na taho nan? me ya faru dani? me nagani a garin da matar da na aura? kai wannan ba kalata ba ce taje can ta karata daga nan gun mota ta na nufa na shiga na dau hanyar kano ban kuma komawa katsina ba_
_ni kuma ban kuma ganin sa ba sai yau haka na rude na damu na bazama neman sa har gun megari wanda ya fada mun eh yazo kuma tun dare ya tafi gd. wasa2 ba umaru ba labarin sa ba motar sa. hakan ya nuna mana cewa ya tafi kuma ya na sane amma ni ce wa nay akwai dalili zaka dawo da wuri ashe karya nay wa kaina nay raino cikina na haifa da taimakon yaya_
_na kusan haihuwa ne muka yi shawarar tuntubar megari a kan umaru kila ya sani cikin ikon Allah muna hanya muka ji cewa ae yanzun nan me gari ya fadi a bandaki a kan dutse rai yay halin sa. tashin hankali da ba a sa masa rana ranar nai kuka har na gode Allah gashi bn san inda zan nemo shi ba.daga karshe ne da naga rabi na samun matsala tana da manema an  ki auranta saboda ba a san dangin mahaifinta ba hakan tasa na yanke shawarar tahowa neman sa da kaina a birni kuma alhamdulilah muka fada hannu na gari ashe ma faduwa ce tazo daidai da zama dan dama nay zargin cewa hajiya nada alaka da umaru saboda kamar da suke sossai ashe zargi na gaskiya ne._

_falon yayi tsist kamar ba mutane illa shashekar kukan rabi da ke tashi hakika mahaifiyar ta mace ce me hakuri da juriya. mahaifinta fa?..._

_hajiya amina tay gyaran murya ta ce mu ma tunda umar ya tafi bamu damu ba kuma bama neman sa hatta matar sa ma. saidai Allah baya bacci kuma ba azalumin bawan sa ba ne ummi ta tambayi abba zata je rano gun er uwar ta ashe gun malama zata koma to rashin sa'a sai ta samu accident ta kakkarye hancin ta ma ya guntule a labarai aka nuna ta ana neman dangin ta shi ne mubarak ya gani yazo ya fada aka dauko ta da ta farka ta dinga kuka tana neman yafiyar hajja da ta abba ta fada mana duk abunda tayi da kuma cewa ita ce SANADIN gurbacewar rayuwar umar da kuma SANADIN barin sa gida da kuma cusa ma junan mu tsanar sa.hajja tay kuka abba ko saki ya rangada mata tana kuka ta fada mana inda ta birne layoyin asirin .ana ko tonowa da kwana biyu sai ga umar ya dawo ansha kuka da kuma jin ya rayuwa ta kasance bayan rabuwa._

_ya fada mana yana katsina a bugale but be fada mana yay aure ba. watan sa takwas abba ya sama masa ayki a nan abuja be dade ba aka dauke shi aiki a london a can aka haifi nasreen da kuma kayyum duk suna can ya jima be zo najeria ba sai yau dana kira sa ganin kin kasa sukuni._

_kennan da umma bata ga hotan ka ba a gidan nan har abada baza mu kuma ganin ka ba? bazaka san ni ba? bazaka ji tausayin da tuna hallaci da mutanen garin bugaje suka maka ba? baza ka tausaya wa matar ka ba da ka bari da ciki ba ka ci amanar me gari da baffa na da yardar da suka maka? umma hakika idan haka uba yake nagode wa Allah da na aminta kuma na saba banda UBA ke ce komai nawa dama nasan ni marainiya ce alhamdulilah da hakan daga yau na cire a raina cewa ina da UBA 😭_

       _hajiya ta ce kar ki fadi haka hajjata duk abunda ya faru SANADI NE_

_na yarda SANADI NE amma da akwai HALI. kina ji ya fada umma ta ba kalar sa ba ce_

_karo na farko da umar ya ji kunya a rayuwar sa da ya san cewa hauwa'u ta na masa wannan mugun san da be mata haka ba. yau er sa ke cewa tana dana sanin shi UBAN ta ne_

      _umma ta mu je mu hada kayan mu muma mu koma kauyen mu inda muke da masoyan mu na tsakni da Allah sai dai hajiya ina rokon alfarma duk da mu ba tsaran ku ba ne 😭 ku biyo mu garin mu ku fada ma kowa ku dangi na ne a san nima ina da asali kuma ni zan fada musu mahaifi na ya mutu..._

    _gaba daya suka daga kan su cike da firgici da tashin hankali suka sauke a kan rabi'atu harda uban gayyar ta na gama fada kuma ta mike ta ja hannun umman ta suka shiga dakin su rungume juna suka yi suka fashe da kuka me ban tausayi!_

        muje zuwa!

  SANADI NEWhere stories live. Discover now