PAGE:1

1.6K 60 1
                                    

GUGUWAR ZAMANI...🌺🌺🌺

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼



Bismillahir Rahmanir Rahim

PAGE:01



Kowani dan adam na dauke da kundin qaddara,wasu kundin kaddararsu na dauke da shafuka masu matukar firgitarwa dakuma jarabawa kala daban daban,kundin kaddarar Zainab tasha banbam da saura,domin cikinta babu komai face bakin cikin rayuwa mara gushewa,Sannan tawuce tunanin duk wani mai tunani,da'ace tanada iko da tuntuni ta goge wahalar datake ciki acikin kundin qaddararta sannan ta nesanta kanta daga al'ummar data fito.

Ta jima tana kallon naira darin da ahmadu ya jefeta da ita,hawaye na racing daga idanunta,ta rasa gane awani gurbi zata saka halayyar ahmadu,rashin so ne ko kuma tsantsar qiyayya yake mata itada'ya'yanta?ta jima tana tunani sannan ta miqe ta dauki darin tana juyata,zuciyarta na tafarfasa,Hijab dinta dake saqale ajikin igiya ta saka,tunani yasha kanta kawai jefa kafa take har ta qarasa shagon shazali,miqa masa darin tayi batareda tace komai ba,zuwa ynxu yasan abunda taje buqata dakuma adadinsu,garin kwakin 80 da sugarn ashirin..ya miqa mata ta karba hawayen baqin ciki na zubo mata,yanzu wannan shine abincinta dana 'yayanta biyu na yau,what sort of life is this?what wrong has she done?she hs been a good person all her life,a good daughter,a better wife and an amazing mother to her kids.share hawayen tayi ta daga kafa domin she's quite sure her kids are back from sch,so she guessed right suna matsakaicin tsakar gidansu azaune,elder one na koya ma qaramin karatu,basu lura da shigowarta ba,ita kuma saita jingina da bango tana kallon su yayinda wasu zafafan hawaye ke sauka daga idanunta,ahaka rayuwar 'ya'yanta zata chigaba da kasancewa?cikin halin rashin kula,rashin cima mai kyau,dakuma rashin ilimi tsayayye?sai ahmadu ya gadama yake biya musu kudin PTA,halayyarsa gareta tamkar kisa ne batareda d'igon jini ba,ya kashe fitilar farin cikin rayuwarta,runtse idanunta tayi Ahankali zuciyarta nace mata"be strong,kodan 'yayanki".

saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga tsukakken kitchen dinta ta wanke garin ta zuba acikin kwano da spoons 2 sannan tafito,zama tayi akusa dasu tana sakin murmushi,da murna sukace"sannu da aiki Mami".tace"kune da sannu,gashi kunsha rana,Bismillah kuci abinci".murmushi babban yayi batareda yace komai ba domin he knows where their prob lies,he knows exactly what they're going through,he knows the kinda Dad they have at this tender age of his.Cin garin sukai hankali kwance suka kora da ruwa.

Suna shirin zuwa islamia Ahmadu yay sallama cikin gidan da voice nashi mai saka yaro mara ji nutsuwa,mai saka yaro mai nutsuwa maida hankali,mai saka babba shakkarsa matuka...zubewa sukai a gabansa "Sannu da zuwa baba".,yace"yawwa,har anyi shirin islamia?to maza ku tafi"yafada trying to initiate something else,dasaurinsu suka tafi shikuma yabi Inda Zainab dake tsaye da kallon tara saura kwata yace"Nalura rashin mutunci gaba kika samasa ba baya ba,har kinkai matsayin da zan shigo kikasa min Sannu?".

Tsura mishi idanu tayi for some minutes sannan tace"ka wuce dukkan wani matsayi agareni ada,amma baa yanzu ba dakai watsi da haqqin mu,ka wofantar da rayuwarmu,taya zan ga matsayin ka bayan kai bakada buri saina tozarta rayuwata?taya zan riqa tunawa da matsayinka awurina bayan ka watsar da nawa matsayin?taya zan cigaba da faranta maka bayan kai baka damu danawa farin cikin ba?".

Hawaye masu dumi ne ke saukowa daga idanunta,

"Kaji tsoron Allah ahmadu,kasani dani da yaranmu amana ne awurinka,sannan yayanmu ababan kiwo ne agaremu,Akwai ranar da zamu ma Allah bayanin irin kiwon da mukai musu,laifin me mukai maka?idan ni baka tausayina ai kaji tausayin 'ya'yanka,idan baka sona ai kaso 'Yayanka,Idan baka kaunata ai ka kaunaci 'Yayanka,amma ka rufe ido kayi fatali da rayuwarmu,kabarmu cikin qunci da matsin Rayuwa yayinda kake shoshalewarka awaje son ranka,kaji tsoron ranar da baki bazaiyi magana ba ahmadu....."tafashe dawani gigitaccen kuka mai taba zuciyar mai sauraro da imani,kuka take of two different types,nafarko kukan rayuwar datake ciki,na biyu kuma kukan rayuwar daza cigaba dayi.

SULTANA...Where stories live. Discover now