PAGE 15

193 22 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

PAGE:15

     Kallo d'aya naiwa Al'ameen na ajiye kaina agefe Ina jin kunyar sa na ratsani,kalamansa ne suke dawo min wanda suka samu wurin zama acikin zuciyata,suka shigeta matuka har take son qara karanta ire iren kalaman,murmushi mai sanyi da taushi ya saki yace"beauty kunyah ko?"dimples din gefen fuskarsa na lotsawa,wanda yakara ma fuskar tashi kyau Sosai,komai nashi cikeda sanyi dakuma tsari yakeyi,"d'ago ki kalleni "yakara fada akaro na biyu,wasa da fingers dina nafara nakasa d'agowa bare na kallesa,gabadaya bakin tsiwar sai ya mutu alokacin,bai gajiya ba yakara cewa"kaini wurin ummu tunda bazaki min magana ba".

Batareda nace Komai ba najuya shikuma ya take min baya muka tafi,fitowar yaya Hakeem ce ta d'aga min hankali ganin ya nufo mu gadan gadan,ga mamakina kuma naga ya shiga part din Ammi adai dai lokacin damuka shiga na ummu,tana zaune afalo hannunta riqe da counter tana lazimi.

Ya zauna akasa cikeda girmamawa ya gaisheta sannan yamata gaisuwa,harara ta watso min tace"hado mishi abin motsa baki".kitchen nashiga na dauki tray madaidaici na zuba bottle water da drink sai cincin da danbun nama agefe,Ina ajiye wa ummu takoma daki,sai alokacin ya dago yana kare min kallo,mai cikeda burgewa da zallar kauna ta,Irin kaunar danake jin labarinta a novels,wacce nake iya gani shimfide asaman fuskar shi,yace"zauna mana,kin tsaya kamar wata soja"murmushi nayi araina ina nazari,akwai shi da tsokana,saide ambatar soja dayayi ce ya b'ata maganar,domin yaya Hakeem ne ya fado min arai,agefen shi na zauna shikuma yacigaba da kallona yana fadin"Ina tsananin kaunar ki beauty,kauna mara fasaltuwa,duk da nasan this isn't the right time daya kamata na bayyana miki sirrin dake zuciyata,but I don't have other option,domin sonki ya gigita tunani na yahana ni sukuni,banida tunanin daya wuce naki,banida maganar data wuce taki,nafada kogin kaunarki wanda har na mutu bazan tab'a escaping ba,sanki yayi min mugun kamun da bazan iya boye shi akoina ba sannan akowani lokaci,Ina jinki acikin jijiyata,jinina dakuma tsokata,Ina miki so na gaskiya da hakika,sonki ne fitilar dake haskaka zuciyah ta yayinda tafada cikin duhu matsananci"saiya durqusa agaba na yacigaba da fadin"ki tallafi rayuwata,ki ji qaina ki amshi kyautar zuciyata kishayar da ita zumar soyayyar ki,pls beauty".

Daskarewa nayi azaune Ina mamakin Al'ameen matuka,banyi tunanin zai iya fadamin haka baki da baki ba,sai na lumshe idanu Ina jin dadin kalamansa na ratsa duk wani sassa na jikina,ahankali tamkar wacce bazatayi magana ba nace"I'll get back to you,give me some time".

Yace"bazan takura miki ba beauty,duk hukuncin dakika yanke ni me yin biyayya ne agaresa,zan kasance me jin maganar ki iya wuya"yafada domin yana da yaqinin yakusa cinye match din,tarkon kaunarshi daya d'ana mata na gab da kamata.

Ajjiyar zuciya naji ya sauke mai karfi yacigaba da cewa"alhamdulillah. Masha Allah. Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan kyakykyawar sura.Beauty Allah yayi miki kyau, ki gode masa, fuskar ki da suffar ki mai kyau ce sosai. Kuma yanayin yadda kike ta faman gyaran hijab dinki da yadda kika makale a tsaye ya saka naji a raina cewa kyawun ki ba'a physical kadai ya tsaya ba, har cikin zuciyarki ke kyakykyawa ce. Ni Al'ameen naga Maryam wato sultana kuma ina sonta, har cikin ruhina ina son ki. Na yaba da komai da idanuwa na suka gani, ina kuma neman alfarmar ki bani dama in gama sanin abinda ban sani ba kema kuma ki san duk abinda kike bukatar sani daga gare ni, that's in abinda kika gani physical yayi miki..."

Kasaitaccen murmushi na sauke batareda nace komai ba na tsiyaya mishi ruwa da drink acikin dogon glass cups,nace "Bismillah "kasa kasa take kallon yadda yake cin komai cikeda tsari,ba zato taji ya jefo mata tambaya"dogon damuka hadu a gate ne yaya Hakeem din naku?".

Na waro idanu waje nakalleshi nace"naku dai,dariya yayi yace"namishi gaisuwa bai amsa ba,gaskiya akwai d'aga kai,koda yake dama soja bashida wasa".samun kaina nayi da jin haushin yaya Hakeem ya mamaye zuciyata,nace"bawani rashin kirki ne,bashida kirki ko kadan"na kara fada Ina pouting bakina,kallona yacigaba dayi batareda yace komai ba,saukar da kaina nayi kasa fahimtar abinda yakeyi,sai ya girgiza kai ya miqe "zan wuce beauty,kya fada ma ummu na wuce,taso ki rakani "kamar yadda muka shigo haka muka fita.

A bedroom ya tarar da Ammi tana gyara kwanciyar Abbas d'an anty Maryam,ya zauna agefenta tareda riqo hannayenta yana sakin murmushi,tace"hakeem naji dadin ganinka "tafada kwalla naciko mata,"zanyi kewar ka Sosai Idan ka koma school dama Nurain ne ke d'ebe min kewarka lokacin dayake raye,dan ma yanzu a final year kuke,Idan da rai dakuma lafiya cikin watanni kadan zaku kammala ".

Yace"karki damu Ammi na,Insha Allah komai zai zo mana da sauki,hakika munyi babban rashi,amma namiki alqawarin dorawa akan abinda Nurain yake miki har izuwa karshen rayuwata".

Murmushi mai cikeda sanyi tayi tace"Hakeem kenan,burina daya shine ka gama sch dinnan lafiya kasamu aiki sannan kayi aure,musamu jikoki da wuri".kawar da maganar yayi tahanyar miqewa yafita gabadaya yarasa Abinda ke mishi dadi,sam bai taba yin budurwa ba,bai taba ganin wacce ta burgesa saba sannan be san ya zaiyi budurwar ba(readers ku dora hakeem kan hanya😉😂).

Da sauri ya fito daga part din Ammi hankalinshi gabadaya nakan wani abun,ganinmu yasashi rage saurin sa batareda ya kalleni ba,saida ya qarema Al'ameen Kallo tsaf kamar wanda zai mishi magana saikuma ya kad'a kai ya wuce,na sauke sassanyar ajiyar zuciyah,domin duk azatona da tsammani na magana zai ma Al'ameen,shi kanshi Al'ameen din sai naga yashiga taitayinsa ganin dayaiwa hakeem,muna zuwa gate na dawo Ina kallon part din gwaggo cikeda fargaba,ban san Meyasa nakejin tsoron ganin dayayi mana ba.

Washegari yakama rana ta uku da Rasuwar Nurain,tun safe aka fara abincin sadaka dakuma addu'oi kala daban daban,aranar ne 'yan yola suka tafi banda anty salma wacce zata kara kwanaki takoma kafin bikinta.

Gabadaya yinin ranar da ciwon kai mai tsanani Hakeem yayi sa, kansa ya dauki caji ga damuwa mara fasaltuwa wacce ke nuqurqusar sa,adaddafe yashiga falon gwaggo lokacin babu Kowa aciki,ya wuce dakinsa ya kwanta asaman gado yana sauke ajiyar zuciyah masu nauyi,yanzu daga shi sai Asal suka ragewa iyayensu dan haka ya dauki alqawarin kula da Asal ta yadda basa zato da tsammani kasancewar sa dan uwanta d'aya tilo aduniya,saikuma tunanin Ammi da daddy,ya Mike ya watsa ruwa yana jin saukin ciwon kan.

Paracetamol yasha sannan ya kwanta wani wahalallan bacci ya dauke sa,washegari da sassafe ya farka kasancewar aranar zai koma makaranta,ba ason ranshi ba ya shirya lokacin k'arfe tara na safe,part din Ammi yashiga yasame su afalo ita da antynsu dakuma anty Maryam,fira sukeyi saide Ammi bata fiye sa baki ba,kallo daya ya mata yaga ta rame Sosai,domin ta saka damuwar rasuwar Nurain aranta,bedroom dinta ya shiga batareda yace komai ba saita miqe tabi bayansa,sanda ta shiga yana zaune akasan carpet yana kallon hanyar fita,zama tai akusa dashi tana fadin" Allah ya kaika lafiya ya dawo min dakai lafiya, Allah ya tsare ya kiyaye hanya, Allah ya albarkaci rayuwarka ya dafa maka, Allah yabaka sa'ar karatu my able soja"takarashe tana sakin murmushi me sanyi,yace"Amin ammi na nagode Sosai "daga haka ya fito dama already an gama shirya kayanshi cikin mota,part din gwaggo ya koma zai dauki back pack,ya fito hannun sa riqe da waya nikuma na shigo da gudu Ina kyalkyala dariya muka ci karo dashi wayar ta fadi ta tarwatse alokacin,jikina yafara rawa ganin yadda yake fitar da numfashi sama sama masu nauyi,nayi saurin durkusa wa na dora hannuna saman wayar shima alokacin ya dora nasa,wani electrification mukaji gabadayan mu alokacin,kowanne yaja baya da sauri ni Ina kallon fuskarshi shikuma yana kallon gefe,nayi saurin miqewa zan wuce ya miqe ya take min dogon mayafin dana yafa,ikon Allah ne yasa ban fadi ba na juyo da sauri Ina kallonshi batareda yace komai ba ya fice daga falon gabadaya nikuma na bishi da rakiyar idanu.Dad'i tafiyar shi tamin sosai wacce ta bayyana asaman fuskata.

K'arfe dayan rana hakeem yakarasa kaduna da tunani kala daban daban,ya zare simcard dinshi ya cillar da wayar ta window yana jin haushin halayyar Sultana ta rashin kamun kai da nustuwa,dan sangarta har saurayi suka barta tayi batareda sun kwab'e ta ba ko kuma sun hanata,ga wani rawar kai na musamman datake fama dashi,duk laifin iyayen su ne dasuka zuba mata ido gudun tashin ciwonta alokuta mabanbanta,yaja siririn tsaki yana ayyana yadda zai gyara mata zama Idan ya dawo,domin baze dauki halin rashin kamin kai ba musamman ga 'ya mace kuma 'yar gidansu.

Da misalin k'arfe takwas na dare lokacin muna kallon Jodha and akbar nida ummu,nace"akwai maganar danake son muyi "
Tace"Ina jinki sulty ".Saida na gyara zama sannan nace"akan Al'ameen ne...."sai kuma nayi shiru ina jin nauyin ta dakuma kunyar ta,tayi karamar dariya tace""Naji dadin haka sulty, Allah ya tabbatar da alheri acikin relationship dinku,Ina bayanki dari bisa dari ".

Da murmushi me sanyi na kwanta Ina jin dadi na ratsa ni,ahankali  soyayyar Al'ameen tashiga zuciyata dakuma rayuwata gabadaya,wata irin kauna mai zafi nake ma Al'ameen wacce ta shiga cikin jijiyata,jinina dakuma tsokata,adaidai wannan lokacin kundin kaddarata ya bud'o min sabon shafi na rayuwata,shafin daya sha banban da saura,wanda bazan so koda maqiyina ya shigesa ba....

SULTANA...Where stories live. Discover now