PAGE 9

270 21 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺

By Zaynab Yusuf ✍🏼

Guguwar Zamani free book ne,just share domin wasu su qaru dashi.

PAGE;9

    K'arfe bakwai da Rabi na dare Ammi tagama shiryawa cikin dogon hijab dinta onion pink color,finger dinta daya saqale da counter,dayan hannun riqeda waya dakuma Asal,gefenta Hakeem ne da Nurain,a part din gwaggo suka tarar da daddy yana zaune ya dora kafarsa kan kujera,gwaggo na kujerar dake opposite dashi tana yatsine fuska alamar abinda suke tattaunawa bai kwanta mata ba.

Zama Ammi tayi akasan kujerar da daddy yake,ta gaishe da gwaggo kanta akasa,shigowar Mami,Aliyu da ayan ne ya dauke ma gwaggo hankali daga amsa gaisuwar tata,ta saki murmushin ganin su Mami tana fadin"hala wani aikin ya tsaida ke?"

Tacigaba "koda yake antyn su ma bata karaso ba,wannan mata kwai sanyin jiki,tana abu kamar ba jini ajikinta,nide mukhtar tashi mutafi saboda nariga nayima sultana alqawarin acan zan kwana"

Murmushi yayi batareda yace komai ba ya miqe suka fita tsakar gida, daddy ne ke driving sai gwaggo agaba,Ammi da Anty dasu hakeem na baya,motar abba kuma da gashi sai mami,mama,Aliyu,Ayan dakuma Amal.

Fitowata kenan daga wanka suka shigo,ummu ce ta taimaka min na shirya cikin wata navy blue din doguwar riga yar turkey,nasa turban dina navy blue as well sannan na zauna Ina gaishe su one by one sukuma suna min ya jiki dakuma fatan samun sauki cikin gaggawa,duk da kana ganina Kasan sauki ya samu alhamdulillah.

Bangaren cousins dina na kalla sunata sakar min murmushi,Amal ce ta rungumeni alokacin hawaye na zubomata,Amal is my sister and absolute best friend,banda kamarta a rayuwa,rungumeta nayi Sosai ina shafa bayanta ahankali assuring her komai zai wuce,sai alokacin muka hada idanu da Hakeem wanda ya saukar da kanshi qasa tun shigowarsu,idanu na zuba mishi Ina masa kallon tsanaki,sanye yake dawasu yardi navy blue kalar kayana,Ina mamaki koda yake na miji yafi kowa agidan kyau,sai kuma na kalli Aliyu wanda ke gefenshi yana sakar min murmushi,alokaci daya naji kamar banyi nazari daidai ba,kallon Aliyu danayi naga gabadaya kyan hakeem danake gani ya ragu Sosai.

Hour daya sukayi daddy ya miqe yana fadin"zamu tafi saboda school din yara,gobe ma Hakeem zai koma yakamata a kwanta da wuri"kallon daddy nayi sannan na kalli hakeem wanda har yanzu kanshi ke sunquye akasa,feelings guda biyu ne mabanbanta suka zo min, Bangare daya bai damu ba,dayan bangaren kuma kamar yanaso ya damu da tafiyar,kawar da tunanin nayi araina gabadaya.

Lokacin dazasu tafi ne hawaye masu zafi suka zubo min,saboda nayi tunanin mama zata rungumeni Sosai ta lallasheni, ta kwantar min da hankali sannan tayi min nasiha kamar yadda Ammi da Mami sukayi,idan aka cire ummu a lissafin wacce nake gani Tamkar itace mahaifiya ta,hannu ummu tasa ta goge min hawayen tana fadin"gobe insha Zaa sallameki dear,dan Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki,ko bakya so natafi ne?"

Ta tambaya tana tsare ni da idanu,kallon gwaggo nayi wacce ta wurgo min harara nace"aa kije ki huta,sakillahu bil jannah ummu na"nafada Ina rungume ta iya karfina,saida jikin kowa yayi sanyi alokacin harda mama wacce taji kamar wani abu ya tsoketa daga tsakiyar kanta zuwa tafin kafarta,yau ce rana ta farko data fara shiga wannan yanayin.

Rakiyar idanu namusu cikeda kewar yan uwana,saina dora kaina akan cinyar gwaggo Ina maida Numfashi,tace"bafa pillow kika samu ba sai faman  tumurmushe Ni kikeyi"
Dariya da mamaki suka kamani nace"kai gwaggo ko minti daya banyiba fa,amma sai nayi hours akan ta ummu bata taba min complain ba Allah sarki ummu na".

Saida ta ture kaina gefe sannan tace"banbancin mu kenan,ita saboda ta burge takeyi da kuma ganin ido,nikuma babu wanda zanyi abu saboda yagani yakuma yaba,dawani qaton kanki kamar na jinjirin jaki ".

SULTANA...Where stories live. Discover now