PAGE 27-28

246 20 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.

                       PAGE:27-28

Muryar shi na rawa yake cewa"Ki dena kukan nan pls,domin bakisan illar daya ke ma zuciyar da babu komai acikin ta sai son ki da kaunar ki,tana jin kukan naki kamar zubar garwashi acikin ta".

Kamar dau kewar ruwa haka kuka nawa ya tsaya cak,sai nayi breaking hugg din tareda cupping face dinshi Ina kallo,ya zama tamkar ba Hakeem dinshi ba na asali,wannan Hakeem din is full of love,wani tsananin son shi da kuma tausayin shi ne yayi tasiri acikin zuciyah ta,na sa hannu na goge mishi hawayen ina girgiza mishi kai akan ya dai na,sai ya saukar da kanshi kasa yace"kiyi hakuri sultana akan dukkan abinda ya faru,sannan kisa aranki ALLAH ya zaba miki miji d'aya tamkar da dubu,wanda zai tsaya miki Idan kowa ya matsa daga gefenki,bazan d'ora daga hakan ba,amma asannu zaki fahimci irin mijin da kika yi gamdakatar dashi ".

Wani sanyi dakuma dadi ne ya mamaye zuciyah ta,bance komai ba domin kalamai sunyi min karanci wanda zasu bayyana yanayin danake ciki,yacigaba da cewa"Sultana nafara sonki tun bakisan wacece ke ba,Ina miki kauna mai tsanani da kuma zafi,sannan baze yiwu na furta miki kalmar so ba alokacin,sai na bari akan nafada miki Idan kin kammala secondary school,cikin rashin zato da tsammani naga kin fara soyayya, Allah kadai yasan Halin dana shiga a wannan lokacin,tsananin son dana ke miki ne yasa bana son wani abu ya riqa hada mu because I might loose control,ina cikin wannan yanayin Aliyu ya sanar dani yana son ki,hakan ba qaramin ciwo ya sanya zuciyah ta aciki ba,Ina ji Ina gani na hakura dake saboda baze yiwu ni da Aliyu mu so mace daya ba,we're brothers,lokacin da Al'ameen ya rasu nasamu wasu mixed feelings,amma na ba Aliyu dama akan bayyana miki son da yake miki,ban san meya hana shi Ba har ya bari dr shuraim ya shigo cikin rayuwarki,hakan ba karamin tashin hankali yasani ba,sai de babu wanda zan iya fadawa ainihin abinda ke damu na,na daina farin ciki da kuma walwala,lokacin da aka saka date din bikin ki da dr shuraim Allah ne kadai yasan halin dana shiga,shine na riqa zuwa umra Ina ziyartar dakin ALLAH,Ina me yin tawassuli da tsarkakakken sunayen sa guda 99,alokacin dana cire rai da samun ki,alokacin dana yi giving up da komai arayuwa ta,adaidai wannan lokacin ALLAH ya bani ke amatsayin mata ta,ban taba tsintar kaina acikin farin ciki irin na ranar ba,Ina tsananin sonki sultana,wacce bazan iya misal ta ta ba".

Gabadaya na manta a inda muke,sai na samu kaina da owning lips din shi,mun fi minti goma ahaka sannan nasamu kaina da cewa"Nagode ALLAH daya bani kai amatsayin miji wato uban 'ya'ya na,Hakika Ina alfahari da kasancewar ka miji agareni,d'aya tamkar da dubu,Idan Ina kuka ka share min hawaye na,yayinda nake cikin damuwa ka sani farin ciki,yayinda nake cikin fushi ka lallashe ni,Hakika kai na musamman ne agareni,saboda ka samar wa rayuwata kyakkyawan littafi wanda dinbin al'umma zasu so su karanta shi a duniyar masoya.".

Na karashe maganar tareda rungume shi iya karfina Ina jin son mijina na ratsa ni,kamar yayi tsalle saboda farin ciki,amma damuwar shi har yanzu ban furta mishi kalmar so ba,yace"akwai wasu kalamai dana ke son ji,wanda duk duniya mutum daya ce ta taba fada min".

Nace"wasu kalamai ne?sannan wa cece wannan data fada maka su ".saida ya kara sassauta murya sannan yace "Heekmah ce kawai ta taba fada min kalmar so".

Tsabar kishi da kuma kaunar shi ce ta miqar dani zaune,nace"sai kaje wurin ta tacigaba da fada maka".
Kamar zaiyi kuka yace"Haba my love,my heart in human form,my everything and more,kada ki min haka,sannan kisa aranki duk wata mace a bayanki take,ba cin fuska ba amma arashin kine na furta mata kalmar so..."hannuna na daga alamar dakatarwa sannan nace"ya ishe ni haka".yana ganin tsananin kishi asaman fuskata.Ina kokarin miqewa ya mayar dani yana kallona cikeda birgewa,yace"baby please I've been yearning for this a long time ago".

SULTANA...Where stories live. Discover now