PAGE 14

215 21 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

PAGE:14

"Bakida hankali ko?"yafada yana gyara tsayuwarsa batareda ya kalli fuskata ba,hasalima gefe yake kallo tamkar ba dani yake ba,yakuma fadin"zan gyara miki zama acikin gidan nan,mara kunya fitsararra,c'mon get inside kafin na dauke mummunar fuskar ki da mari"yakarashe maganar yana me d'aga hannu sama,Sosai tsananin tsoronsa yayi tasiri acikin zuciyata,idanu na suka firfito waje amma naki nuna zallar tsoro afili duk da zuciyah ta cike take da fargaba,da mamaki yake kallon gefena sede har yanzu bai kalli fuskata ba,qin motsawar danayi ce ta bashi mamaki dakuma haushi mara fasaltuwa,baya son raini ko kadan,baya son ayima wani bare ayi mishi akaran kanshi,atake idanunsa sukayi jajir ya dago su tareda sakawa cikin nawa,da tsananin firgici nafara ja baya ganin yanayinsa Ya canza gabadaya,tamkar yana filin daga Ko kuma filin yaqi,sai de kafin nayi motsin kirki kaina yafara juyawa,Sosai zuciyah ta ke bugawa da tsananin karfi,na dafe ta da hannun hagu na dafa bango dana dama,bai kara kallon inda nake ba yay gaba abinshi yana nazarin yadda zai yi maganinta ta cikin ruwan sanyi da dukkan yaran gidan gabadaya,part din gwaggo ya nufa yabarni riqe da zuciyata wacce abu kadan ke sata tsananin bugawa ba abisa qa'ida ba,sunan Allah nafara ambata Ina runtse idanu domin samun rislama acikinta,Ina jin haushin yaya hakeem na ratsa ni acikin jijiyata,jinina dakuma tsokata,sannan Ina jinjina girman tsanar dayayi min wacce har takai ya tsallake ya tafi cikin halin daya barni,bayan shine musabbabi kuma sanadi,ikon Allah ne yahana ciwo na tashi,jiki ba kwari nakoma part din ummu raina a jagule,a kitchen na tarar da ita tana girki,sai na tsaya Ina kallon yadda take had'a komai cikin tsari,kamshin girkin ya karad'e part din gabadaya,with admiration nake kallonta domin ba abinda na iya girkawa sai indomie,suyar dankali da kwai sai doya,alokuta mabanbanta Ina ma ummu maganar son koyon girkin amma saita ce Ba yanzu ba,yanzu lokacin karatu ne dan haka na Maida hankalina garesa sai lokacin data ware yayi sannan na koyi girki,shiyasa ko albasa bana yanka mata sede nayita kallonta cikeda burgewa.

Waiwayowa tayi fuskar ta dauke da murmushi tace"daga Ina haka?"Na bata rai Sosai nace"daga baya "dayake haka muke kiran wajen,tace"yin me?Fushin me kikeyi?"

Tura baki nayi nace"nida waccan mafadacin ne "nafada cikeda tsantsar tsiwa,riqe baki ummu tayi tace"bari yajiki ba ruwana"bubbuga kafa na tafi inayi Ina fadin"yakama din,anfada mishi tsoronshi nakeji?"nafada Ina karyata hakan acikin raina,tsananin rashin tsoro ne da tsiwa yasani fadan hakan,wanka nayi na shirya cikin black jeans da pink top,English wears ne kayana akoda yaushe cikin sasu nake,black turban nasa wanda yayi min kyau Sosai,nai applying powder da pink lipstick,saida nayi clicking pics sannan na fita falo lokacin ummu na jere flasks akan dining,kujera najawo na bud'e daya daga cikin flask din,fried rice ce ta asali wacce tasha veggies da spices,dayan flask din pepper chicken ce sai coleslaw agefe dayasha hadi na musamman,komai kadan nazuba daidai cikina nafara ci cikeda nustuwa Ina danna waya,message dinda ya shigo ne yasa na ajiye spoon din hannu na babu shiri.nafara karantawa cikeda zakuwar sanin abinda ya k'unsa.

"So ne asalin rayuwa sultana,sannan kuma abinda yake sarrafa ragamar dokin rayuwa abisa hanya managarciya,so ne tekun dake gangarowa daga ruhi zuwa sassa daban daban na jiki wanda ke fesar da shauki a nahiyar qalbi,so ne maganin daya ke warkar da zuciyar data shiga garari,zuciyata nacikin garari,soyayyar Guguwar Zamani ta jefani cikin taskun rayuwa,ki tallafi zuciyar da batada mataimaki sai ke kadai afadin duniya,tun sanda Nafara nagninki kwance agadon asibiti,lokacin Kina tsananin ciwo,naji sonki yashiga raina,ya mamaye jinin dake gundana a sassan jikina dakuma bargona,tun daga wannan lokacin rayuwata ta canza,the leaves has become more greener,you brought so much light & happiness to the darkness of my life,nayi tunanin nabar komai nacikin duniyar nan tun rasuwar Aisha ,I exhausted everything,zuciyata takoma tamkar filin da babu komai acikinsa,sai kuma na hadu dake,tun daga farkon haduwar mu nayi realising ke din ta dabance,but nakasa yarda da hakan ina fada MA kaina hakan baze faru ba,bt you changed me from the inside,ayanzu bazan iya rayuwar da babu ke acikin ta ba,sannan inada yaqinin zan riqe soyayyarki dakuma amana tamkar yadda zan kare raina,dan Allah ki bani dama nazo nafada miki yadda nake jinki araina,ido da ido,baki da baki,yadda zaki fi fahimta ,ki yadda da kalamai na sannan ki taimaka ki agajeni ki amince da maganar dana zo miki da ita,Ina jiran amsa,pls try and reply me"ya dasa aya bayan ya hada wannan emojin 🙏🙏.

SULTANA...Where stories live. Discover now