PAGE 8

330 21 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

PAGE:8

   Ya matso daf dani ya bud'e idanunsa cikeda mamaki yace"Sultana Meke damunki?"
Kasa cewa komai nayi yadda hakorana na sama ke had'ewa dana qasa suna bugar juna da sauri da sauri,na runtse idanu tareda dafe kirjina,kamar ana caka min wuqa haka nakeji,gawani zafi da yaji dayake min alokaci daya,hawaye masu zafin gaske ne ke zubo min,nauyi da ciwon da kirjina ke min bazan misaltu ba ,yanayin danake ciki yasa Hakeem kwalawa gwaggo kira ,afirgice tafito falon tana fadin"ubana kiran me kake min da tsohon daren nan?"

Kallonta yayi batareda yace komai ba ya daga hannunsa manuniya ya saita daidai inda nake kwance ina murqususu,kirjina kamar zai faso daga gangar jikina,gumi ya wanke min jiki saboda azabar zafin daya dauka,hankali tashe tace "Innalillahi wainna ilaihi raji'un "tafada tareda fita kiransu daddy duk da tsananin tsoron gwaggo.

Durqusawa yayi daidai inda nake ya dauki hulata dake gefe nayi wurgi da ita saboda azaba,da ita ya goge min gumi yana karanto duk adduar daya iya,azabar ciwo yasa na damqo hannunsa iya qarfina na matse Sosai tareda runtse idanu na, Allah kadai yasan wahalar danake sha alokacin,baice min komai ba,sannan Bai kwace hannun nashi ba,illa kallon mamaki daya ke jifana dasu mabanbanta,addua yacigaba da min yana shafawa asaman kaina da hannunshi,Sosai naji azabar danake ciki ta qaru,juya kai nake ahankali inason yin magana amma nakasa,shigowar iyayen mu yasa Hakeem miqewa yaja baya.

Daddy,baba da abba ne suka yo kaina da sauri,iyayena mata na min sannu a cikin voices dinsu mabanbanta,gyada kai kawai nake yi,daddy ne ya daukeni muka fita zuwa hospital,daddy ne ke driving da baba agaban motar,sai abba da ummu abaya,Ina kwance akan cinyar ummu wacce hawaye suka kasa daina zubo mata,suna digowa asaman fuskata.

Cikin minti talatin muka karasa UMC clinic,emergency aka kaini doctors suka fara bani taimakon gaggawa,hawaye masu dumi ne ke zuboma babana,he's just imagining pain din danake ciki,saide babu wanda zai iya fasalta halin danake ciki,dan koni bazan iya bayyana yadda nakeji ba saidai na misalta,ummu ce ta dafa shoulders dinsa assuring him everything will be fine,daddy na gefe yana yimasa nasiha,"cuta ba mutuwa bace,cuta kaddara ce kuma jarabawa,zamuyi duk abinda yakamata domin ganin tasamu kulawa,sannan yazama dole mu dage da addua domin sauki na wurin Allah".

gyada kai baba yayi yana gamsuwa da maganar daddy,hakika addua kawai nake buqata awannan lokacin.

A reception dr Annur yasamu su baba azaune,Saida ya gyara zaman stethoscope dindake saqale da wuyan sa sannan yace"ku sameni a office "ya karasa maganar yana Daidaita farin medicated glasses dinshi,jikinsa sanye dawasu jeans and shirt,sai farar labcoat daya saka.

Zare farin glasses dinshi yayi sannan ya fuskance su,"'yar ku nacikin damuwa dakuma firgici mai tsanani,kuma hakan babbar barazana ce agareta domin yafara taba zuciyar ta,abu kadan zai iya sa ta kamu da ciwon zuciya wanda a turance ake kiransa da myocardial infarction,dan haka ku kula Sosai da emotions dinta,Idan ba haka ba akwai babbar matsala".

Yacigaba "nayi mamakin ganin yadda zuciyarta ke bugawa ba abisa qa'ida ba,sannan Idan mukai la'akari da musabbabin ciwon zuciya sune tsananin damuwa,ciwon kirji mai tsanani wanda take fama dashi yanzu,ciwon wuya,ciwon baya,ciwon haqarqari,abnormal heart beats dakuma anxiety,inda muka cire wanda aka haifesu da ciwon"

"Yazama tilas ku cire damuwa daga babin rayuwar ta,domin tana gab da kamuwa da ciwon zuciya,ko baa fada ba kunsan illar ciwon yanada yawa,maganin kar ayi kada asoma,I'm emphasising on ku guji b'acin ranta da duk wani abu dazai sata damuwa,firgici da sauran su,zuwa jibi insha Allah zamuyi discharging din ta"

Kasa motsi baba yayi saboda tsantsar mamaki,ya maimaita kalmar ciwon zuciya sau babu adadi aransa,nazarinsa da lissafin sa ya dora kan  mizanin hankalinsa gameda sultana harma da Amal,

SULTANA...Where stories live. Discover now