PAGE 15-16

189 19 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.



                PAGE:15-16

   Kuka nayi mai tsaho dakuma yawa,wanda yake k'arya zuciyar mai sauraro,kuka biyu nayi mabanbanta nafarko shine na idanu wa na biyu kuma na zuciya,kaina na juyawa kamar zai fad'i na miqe jikina nawani irin rawa,dakyar na maida kaina bedroom din dasuka kaini,cikeda jarumta na jawo rigar abaya nasaka sannan na koma kan gadon na kwanta Ina rawar sanyi,kukan dana keyi ba mai sauti bane amma hawaye nata zarya abisa kuncina,na damqe hannuna tareda furzar da zazzafar iska,Sosai jikina yadauki zafi na ban mamaki gashi ni kadai ce agidan babu kowa bare a taimaka min da magani.

Kiran sallar magrib ne ya miqar dani tsaye,atake kafafuwana suka lankwashe na fadi kasa babu shiri,kafata ta bugu da katakon gado na runtse idanu ina sakin kuka mai sauti,nafi mintuna goma ahaka sannan na miqe na shiga toilet,dakyar na iya daura alwala na zauna akan sallaya nayi sallar azaune,har lokacin hawaye basu daina zuba daga idanu ba.

Sai na fara Tunani mara zurfi,yanzu da agida ne da tuni an bani magani nasha,gashi yanzu sun aura min mugu wanda ko qeyarshi ban gani ba bare ya siyo min,haka na rarrafa na koma kan gadon na kwanta Ina cigaba da kuka mai dalili.

Kiran sallar isha ne ya sake miqar dani na gabatar da ita dakyar kasancewar yadda ciwon yayi galaba akaina,ko iya komawa kan gadon banyiba na kwanta akan sallayar Ina maida numfashi sama sama,hawaye masu zafin gaske na zubo min ta gefen idanu na.

Ina cikin wannan yanayin wani wahalallan bacci ya daukeni,ban farka ba sai gaban nin asuba,ciwon kan ya ragu amma zazzabin na nan,ga wani weakness na musamman data dirar min,na bud'e idanuna na dora akan hadaddan agogon dake side drawer dina,cikeda mamaki naga quarter to 5 kasancewar bulb akunne yake,na miqe zaune ahankali Ina karema dakin kallo,daga gefena naga an ajiye leda mai girma,yunwar dana keji ce tasa na bud'e ledar,abinci ne mai rai da lafiya,fried rice da grilled chicken sai coleslaw,bottle water dakuma drinks.

Cikeda nustuwa nake cin abincin ba dan yana min dadi ba sam,sai dan yunwar dake nuqurqusata,na sha ishasshen ruwa sannan na gabatar da alawa nayi ra'akatul fajr.Ina nan zaune Ina addu'oi har lokacin sallah yayi nayi sannan na hau gado na kwanta ciwon kan jiya da zazzafan zazzabin na kara saukar min babu sauki.

Tabangaren yaya Hakeem sai past na 10 dare ya dawo,kasancewar ya yi parking daga wancan gidan kuma sun Daidaita da mai gidan,koda ya shigo dakin farko na qasa ya yada zango,abincin daya siyo ya hau sama dashi yana da tabbacin acan suka ajiyeta,

Dakin farko yafara shiga wanda yasha sky blue royals,ya tsaya yana kallon dakin dakuma gidan in general,hakika daddy ya kashe Kudin ban mamaki,a next bedroom yaganni yashe asaman sallaya ina bacci,sai ya ajiye min abincin yafita daga daki batareda nasani ba,ya koma daya daga cikin bedrooms din kasa ya gama komai na al'adar rayuwarshi sannan yaci abinci ya kwanta yana ganin gabadaya abin wani banbarakwai,kodan ba Heekman shi bace?kodan baya son sultana ne shiyasa kwata kwata abin yazame mishi sai ahankali,yana zaman zamanshi an aura mishi matsala,yafada tareda sakin tsaki bacci ya dauke shi.

Bayan yayi sallar asubah ne yaji shigowar mail cikin wayarshi,koda ya duba daga office ne suke congratulating dinshi, an bashi 2weeks break,sannan zasu hada mishi kwarya kwaryar dinner shida madam,yasaki siririn tsaki domin shi baiga amfanin hutun dasuka bashi ba,he'll just feel bored at home,ga kuma bakin cikin dayake kwasa na gani na.

Wani baccin ya dauke shi mai dadi sai past 10 yafarka,saida yayi wanka ya shirya cikin wasu comfy home wears sannan yayi musu order,lokacin ciwo na neman hallaka ni domin dakyar nake jawo Numfashina,zuciyata nawani irin bugu kamar yadda takeyi aduk lokacin da ciwo na zai tashi.

SULTANA...Where stories live. Discover now