PAGE 11

246 20 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺

By
Zaynab Yusuf ✍🏼



PAGE:11

    Shigar mu gida kenan kaina yafara juyawa up side down,wani abu mai nauyi ya takore min kirji,na runtse idona ahankali,bazan iya fasalta yanayin danake ciki ba,komai na jikina yayi min matukar nauyi,cikeda dauriya dakuma jarumta wanda kowa yayi min shaidar su na fito daga motar tareda jingina agefe bayan na rufe kofar,taku hudu zuwa biyar nayi naji anyi sama dani nai wata irin mummunar faduwa takai,atake jini mai tsanani yafara zuba.

Cikeda tsantsar tashin hankali iyayena da 'yanuwana sukayo kaina,ummu ce ke jijjiga ni hawaye masu zafi na zubo mata take cewa"Innalillahi wainna ilaihi raji'un "Wannan kalmar kowa nagidan ke ambata a voices dinsu mabanbanta,Suman tsaye babana yayi hawaye masu zafi na zubo masa,wannan wacce irin qaddara ce take zuwar min acikin kowacce daqiqa na rana?Kuka gabadaya 'yan uwana sukeyi ganin halin danake ciki,daddy ne ya yi jarumtar dauka ta ya mayar cikin mota,ummu,Ammi dakuma baba sukayi hanzarin shiga muka bar gidan da gudun gaske.

Gudu Sosai daddy ke yi,mafi yawanci motoci ne ke basa hanya yana ratsawa yana wucewa,hakan yasa cikin qanqanin lokaci muka karasa Aminu kano teaching hospital,emergency aka kaini lokacin na dade da sumewa ban san inda kaina yake ba,ummu wacce ke bani labarin tace tunda nafara ciwo wannan ne mafarin ciwona masu hatsarin gaske,doctors shida ne akaina suna kokarin shawo kan matsalar,sedai Duk yadda suke tunanin problem din yafi haka,kokarin tsayar da fitowar jinin sukeyi amma hakan ya garara,cikin qanqanin lokaci jikina yayi wani irin fari lamarin daya firgita kowa nawurin,da sauri nurses sukaje wurinsu ummu wacce ke kuka mara sauti,Ammi ta jingina kanta da bango mai matukar ciwo,babana ya hada kai da gwiwa yana fitar da numfashi da sauri da sauri,daddy ne tsaye ya kalmashe hannu akan kirjinsa yana nazari dakuma lissafi,zuwan nurse din yasa su miqewa da sauri tana tambayar jinin waye acikinsu daidai dana sultana?dadddy ne yace "muje"domin shine ke bani jini a lokuta mabanbanta,hakika abinda Allah ya kaddara ne ke faruwa,domin ancire rai dani,hatta doctors din jikinsu yayi sanyi,tabbas dukkan tsanani yana tare da sauki sannan addua na iya canza kaddara,a reception din emergency babana ya yi sujjada yana kuka yana fadin "ya Allah ka tashi kafadun sultana ,ya Allah ka zaba mata abinda yafi alheri acikin rayuwar ta,ya Allah ka jiqan wannan baiwa taka,ya Allah kabata lafiya da dukkan musulmai baki daya,Ya Allah kai riqo da hannayenta,ya Allah ka dafa mata,Ya Allah batada sauran mataimaki sai kai ya Allah,Ya Allah ease her suffering and grand her what's best for her,ya hayyu ya qayyum"ya karashe adduar hawaye me zafi na zubo mishi.

Ammi ce tafita daga reception din duk da tsananin ciwon kan dake damunta,har bakin gate ta karasa inda masu buqata suke,kudin dake hannunta dubu biyar ne daidai,yan dari bibbiyu,haka tariqa rabawa almajira da sauran masu buqata,bakunansu mabanbanta na yimin adduar samun lafiya,hakika sadaka maganin musiba ce,sannan idan abu zai faru da mai yawaita sadaka yakan zomasa da saukin gaske,jiki ba kwari takoma ciki time din daddy ya dawo reception din hannunshi na dama riqe dana Hagu ya zauna tareda dafa babana cikin karyewar zuciya yake fadin"zata samu lafiya bi'izinillah, Allah zai tashi kafadun sultana Insha Allah,this too shall pass".kasancewar daddy da babana masu matukar son 'Ya'ya.

Lokacin Ina duniyar da nake jiran ikon Allah madaukakin sarki,mabuwayi gagara misali,mai yin yadda yaso alokacin dayaso,nikaina nafitar da rai da samun lafiya,nafitar da rai da rayuwa,Ashe dama ni ba mai tsahon kwana bace aduniya?ashe dama shirme kawai nakeyi Bansan nakusa komawa ga mahaliccina ba,wata irin bugawa zuciyah ta tayi wacce ta gigita tunanin doctors,aduk tunanin su ta buga gabadaya,aduk tunaninsu na kwanta dama,aduk tunaninsu I was gone...

Allahu sami'un du'a ne,Allah mai amsa adduar bayinsa ne,Allah mai jinkan bayinsa ne sannan Allah mai rahama ne ga bayinsa,alokacin da kowa yafitar da rai dani,alokacin da ni kaina nacire rai da rayuwa,adaidai lokacin Allah ya kawo min sauki cikin rashin zato da tsammani jinin dake zuba ya tsaya cak,da mamaki doctors din suka Cigaba dabani taimakon daya dace.

SULTANA...Where stories live. Discover now