PAGE 21-22

234 23 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.



                    PAGE:21-22

   Yafi seconds hamsin yana kallon fuskata,nikuma nayi kasa da idanu na tareda kawar da kaina gefe,baice komai ba ya tayar da motar yafara driving waqar Michael Jackson "You are not alone "tana tashi acikin motar.

Ahankali cikeda taushi yake miming "That you are not alone,I am here with you,Though you're far away,I am here to stay,But you are not alone,I am here with you,Though we're far apart

You're always in my heart,But you are not alone".

Kasa kasa nake kallonshi yana bin waqar hankali kwance,yacigaba da bin waqar wacce nake jin kamar da ni yake"Just the other night, I thought I heard you cry,Asking me to come

And hold you in my arms,I can hear your prayers,Your burdens I will bear

But first I need your hand,Then forever can begin".

Sosai na dago fuskata na zuba mishi dara daran idanu na ina kallonshi,mamaki yake bani mara fasaltuwa,saina tsinta maganar shi a sama,yace"kallon na miye?"

Nace"wani kallo?"ina kawar da fuskata gefe,yace"gashi nan Kina yi kuwa".

Na tab'e baki sannan nace"sai kace wani kai?".

Dakatawa yayi kadan ya kalleni sannan yace"aa ban kaiki ba".

Na samu kaina da cewa"kaifa mr kallo ne ".

Kamar zai yi dariya saiya fasa,amma kwarai na bashi dariya,yace"ke kuma mrs kallo".

Nace"ta ya akayi na zama Mrs kallo?".

Saida ya kara tausasa murya sannan yace"tunda nazama mr kallo kema kin zama Mrs kallo."

Sai alokacin da d'ago da abinda yake nufi,bance komai ba nacigaba da kallon hanya Ina tunani mara zurfi akanshi.

Shine yakara cewa"Anjima Kamal da Asmau zasuzo ".

A lokaci daya na juyo nace"da rana ko dare?".

Yace"ni ban sani ba,but why are you asking?".

Ahankali kamar bazanyi magana ba nace"saboda abinci".

Sai ya tsaida motar tareda juyowa ya fuskance ni,yace"dama kece ke yin girki?".

Na girgiza kai alamar a'a yace"Toh meyasa kika ce haka akaron farko?".

Nan ma shiru nayi bance mishi komai ba,sai ya tada motar muka cigaba da tafiya kowa da tunanin dake ranshi har muka karasa gida.

Na sauko daga motar ahankali lokacin har ya bud'e booth yafara ciro kayan,na duk'a zan dauka naga ya riqe min hannu,sai nayi saurin miqewa tsaye Na dora idanu na akan fuskar shi,shima ni yake kallo kafin yace"this is my work,allow me to do it".

Sosai yaya Hakeem ke matukar bani mamaki,mutum ne mai tsananin kula dakuma tausayi,haka na shiga ciki bayan ya bud'e kofar na zauna afalo,Ina kallonshi yagama shigowa da kayan gabadaya sannan ya fara bud'e su,and I felt really uncomfortable.

Sai na miqe na karasa inda yake,yace min"karki damu je ki huta,you're meant to ".

Saina girgiza mishi kai alamar a'a,sannan nace"let me help you ".

Ya ce"pls ki koma ki zauna".

Sai na gyara tsayuwata nace"Meyasa?"

Samun kanshi yayi da cewa"saboda banason kisha wahala".

SULTANA...Where stories live. Discover now