PAGE 25

161 15 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

         Wattpad @Zaynab_yusuf

          Exquisite writer's forum.

 
                PAGE;25

Safa da marwa Aliyu keyi tsakanin reception da emergency,Hankalin shi yayi matukar tashi ganin yadda numfashi na ke sama yana sauka da karfi,hawaye masu zafi na sauko masa cikin rashin kakkautawa,jikinsa har rawa yakeyi saboda yadda zuciyarshi ke zillo yana jiran abinda doctors zasu fada gameda ciwona.

Hakeem ne ya miqe yana kallon Aliyu wanda yakasa zaune yakasa tsaye,saida yakarasa dab dashi sannan yadafa kafadar Aliyu yace"take heart,Insha Allah zata samu sauki,I can only imagine yadda kakeji acikin zuciyarka,duk da bansan yadda ciwon masoyi yake acikin zuciya ba,amma na tabbatar ba abu bane mai sauki,idan kayi hakuri kuma ka fawwala Allah lamuranka sai kaga komai yazo maka cikin sauki dakuma tsari".

Murmushi Aliyu yayi wanda ya bayyana tsananin bakin cikin dayake ciki,yanajin tamkar ya cire zuciyarshi ya yar saboda yadda take mishi zafi dakuma quna alokaci daya,yace"tabbas saide kayi imagining irin pain din danake ciki,sannan bazan yi fatan ka shiga irinsa ba,domin zuciyata nacikin k'unci mai tsanani,na farko shine fyad'en da akai wa sultana,wanda nakejin zafinsa araina mai radadi ,saide tausayin ta dakuma sonta ne yakara tasiri acikin zuciyata,domin Ina kaunar sultana kauna mai tsanani,wacce zan iya zama da ita acikin kowani hali,acikin kowani yanayi,Ina sonta ahaka kuma zan cigaba da sonta har karshen rayuwata"ya numfasa sannan yacigaba da fadin"sai kuma ciwon ta daya tashi yanzu,wanda nake tsoro dakuma fargaba akanshi,kada ya canza salo kasancewar heartbreak ne musabbabin tashinsa ".

Kallon mamaki kawai Hakeem ke jifan Aliyu dashi,yayi qaramin murmushi tareda jijjiga kai,badan ya aminta da maganar Aliyu ba,bakuma dan ya yadda ba,sai dan kawai adasa digon aya akan maganar (full stop).
Kan seat yakoma ya zauna yana dora nazarinsa kan mizanin hankali,domin rasuwar Al'ameen ta qara bayyana cewar akwai wanda ke musu Saran b'oye,sannan akwai b'oyayyen al'amari wanda zai iya cutar dasu acikin kowani lokaci,yazama tilas kuma yazama dole su dauki mataki akan wannan lamarin,amma tayaya zasu daukin matakin?bayan basuda wata hujja akan kowa?babu wanda ya tab'a nuna musu qiyayyar su afili bare suce suna zargin wani,tashin hankali kenan!yafada yana furzar da zazzafar iska daga bakinshi,ya lissafa gabadaya mak'otansu babu abinda ya tab'a shiga tsakaninsu na fad'a,hasalima basu taba samun matsala ba,Toh waye keda hannu acikin wannan lamarin?waye ke musu Saran b'oye?waye ke cutar dasu cuta mafi muni?wannan tunanin ne ya tsiya yar da ruwan kan Hakeem gabadaya,domin duk iya gane mara gaskiya dakuma iya takunsa wurin gano mara gaskiya yakasa hasashen waye zai iya aikata hakan.

A reception suka ci karo da wani matashin saurayi mai tsananin kyau da cikar Kamala,jikinsa sanya da shadda milk color se faman kyalli take da maiko,labcourt ce ya dora asaman kayan sai stethoscope dake maqale da wuyansa,Daidaita glasses din dake fuskarsa yayi yana meyima Aliyu duban tsanaki kafin yace"Young man relax,she'll be fine"yadda yayi maganar yasanya Aliyu sauke ajiyar zuciyah kafin yace"pls dr try your best".yana shiga emergency room din yake fadin"trust me".

Minti bayan minti Aliyu ke lekawa emergency hall din,dawowar shi takarshe ce tasa Hakeem cewa"ka shiga ka duba ta,Ina ganin hakan zai fi"Miqewa yayi jiki babu kwari yakoma inda nake,ya mirda handle din kofar tareda tura kanshi ciki,atake sanyin Ac ta dakeshi ya lumshe idanu yana kallona kwance a sick bed,ya sauke ajiyar zuciyah ganin pulse dina na tafiya daidai ,alokacin Dr Sameer ya Daidaita drip din daya sanya min yana kallon fuska ta cikeda birgewa lamarin daya sa Aliyu Suman tsaye kenan,domin da dukkan alamu Dr Sameer baisan da shigowar tasa ba,hadiye wani qullutu yayi daya tokare masa wuya ya dafa dr Sameer wanda ya d'imauta daganina,saida ya sauke wata Ajiyar zuciyah sannan yakai hannunsa saman farin glasses dinshi ya Daidaita shi kafin yakai duba ga fuskar Aliyu wacce take ahad'e tamkar hadarin gabas,hakika koda Dr Sameer ke na miji seda yasha jinin jikinsa,domin kallo ne wanda babu alamar wasa acikinsa Aliyu ke watso mishi ,asannu Dr Sameer yasoma tafiya yana fadin"zata farka nan da 1 hour"yachigaba da cewa"make sure ka siyo wannan drugs din kafin ta tashi "yakarashe maganar yana me miqawa Aliyu prescribed drugs din yafita yana mamakin Matukar kwarjinin Aliyu.

SULTANA...Where stories live. Discover now