PAGE 24

146 16 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

          Wattpad @Zaynab_yusuf

           Exquisite writer's forum.

                     PAGE;24

"Wanene Al'ameen?wanda bamu san dashi ba,sai ke da sultana?"Baba ya tambayi ummu yana kallon fuskarta,idanunta gabadaya sun rine saboda kuka,murya na rawa tace"shine wanda ya baiwa sultana jini a asibiti,tun daga wannan lokacin muke mutunci dashi yana kirana ya gaishe ni sannan yana tambayar Jikin sultana akowani lokaci har ta samu sauki".

"Tun daga wannan lokacin na fahimci tsananin sonta dayakeyi wanda baya iya boyewa kuma baya iya controlling,ya yimin magana akan zai turo magabatansa domin asan dashi,ni ce na dakatar dashi saboda nasan bazaku amince ba,kasancewar sultana a ss2 take sannan shekarunta goma sha shidda kawai,sai na bashi hakuri tareda mishi alqawarin shige masa gaba Idan sultana tayi candy,nasan zuwa lokacin ne zaku iya saurara ta kuma ku fahimce ni,Hakika na yadda da hankalin Al'ameen dakuma tarbiyyar sa,haka ne yasa har ya hadani da yar uwarshi,wato elder sister dinshi muke gaisawa time to time,ganin haka yasa na amince su riqa magana da sultana,nasan na tafka babban kuskure dana aikata hakan batareda kun sani ba,amma dan Allah kuyi hakuri,domin na dauki sultana kamar yar dana haifa,wacce zamu kashe mu binne batareda kowa ya sani ba,kamar yadda iyaye mata keyi alokuta mabanbanta ".

"Ban san haka outcome din zai kasance ba,da bazan taba yadda da alaqar su ba".
Cikeda fada dakuma tsantsar b'acin rai baba yace"kinyi kokari Jameela,kin bani kunyah ban taba tunanin haka daga gareki ba".

Daddy yace"aa Yusuf,kada kace haka,kada kayi judging Jameela akan ta aikata kuskure guda daya,kada ka manta alkhairan data mana arayuwa,na tabbatar zatai iya bakin kokarinta wurin kare rayuwar sultana daga fadawa cikin matsala".
In confirmation kowa ya daga kanshi sama,domin babu wanda yaji dadin maganar baba alokacin,daddy ne yacigaba da cewa"abinda ban fahimta ba shine ya akai abun ya faru?sannan ke sultana duk da karancin shekarunki na tabbatar kin fahimci wasu alamu na rashin gaskiya atattare dashi,babu yadda zaayi yazo ya dauke ki haka kawai batareda yamiki dadin baki ba,shiyasa yin shawara da magabata keda amfani arayuwa,sannan iyayenki maza yakamata musan dukkan halin dakike ciki,dan na tabbatar da Al'ameen din yasan mun sanshi babu yadda zaayi ya aikata haka".

"Hakika kun tafka babban kuskure,wanda ya shigo rayuwar sultana shigowar bazata,na dade ina ganin komai yatafi daidai acikin gidan nan,sannan ku iyaye mata kune zaku karfafa mana gwiwa akan lamarin gidan mu,wato sanar damu halin da yaran mu ke ciki alokacin damuka tafi neman abinci,amma babu wanda yayi hakan acikin ku,musamman Jameela data san da yaron acikin rayuwar sultana,sai yanzu da abu ya lalace sannan muka sani,Ina son amfani da wannan damar domin na jaddada gargadina akan ku gabadaya "sai ya miqe cikeda b'acin rai yacigaba da cewa"zan kafa dokoki masu tsauri acikin gidan nan wanda sukafi na baya,kuma duk wanda ya taka min doka will face the consequences,Jameela kinyi kuskure na shaida hakan,amma dole a miki hukunci,ki tafi gida kafin zuwan wani lokaci".

Hawaye masu zafi ne suka zubowa ummu,tace"ashirye nake dana karbi kowanni hukunci daga gareku domin na san ni me laifi ce".

Jikina na rawa na taso da sauri na rungume ummu Ina kuka mai tsanani,nace"daddy ba ruwan ummu,duk abinda ya faru nina ja ma kaina,kuma sannan it was a rape attempt..."

Tsawar da mama ta buga min ce tarufe min baki tace"sakarya kawai shashasha,mara hankali wacce batasan ciwon kanta ba,har yanzu kin kasa fahimtar abinda yake faruwa dake bayan anty ta dubaki ta gani,kin cuce ni sultana"takarashe maganar tana fashewa da kuka mai dalili.Mikewa ummu tayi jiki ba kwari,hawaye basu dena zubo mata ba tafara tafiya zata bar falon,gwaggo tace"dakata Jameela "tacigaba da cewa"bana jayayya da hukuncin daka yanke,amma wannan yayi tsauri dayawa,ya zaa yi ta tafi gida sai kace wata qaramar yarinya?tazauna dai zaifi sai anemo wani hukuncin amata".
Ammi tace"kwarai na aminta da maganar gwaggo,komawa gida dasunan yaji abin kunyah ne ballantana a irin shekarun mu ".

SULTANA...Where stories live. Discover now