PAGE 5

366 30 0
                                    

Guguwar Zamani🌺🌺🌺

Guguwar Zamani free book ne,just share domin wasu su qaru dashi,kuskuren danayi Allah ya yafe min,my inbox is open for corrections,comments and advert,just slide into my PC.
https://chat.whatsapp.com/BLdx9bHgeXYLao2QAjarGc
(Guguwar Zamani fan page for more updates)

PAGE;5

Yace"Ina matukar ganin girmanki Maryam,babu abinda bazan iya miki ba arayuwa,amma wannan alfarmar taki tayi min tsauri dayawa,bazan iya had'a soyayyar ki dawata ba,tun farkon haduwar mu har zuwa auren mu,zuwa yanzu da Allah ya albarkace mu da yara 3 ban qara kallon wata mace ta siffar Soyayyah ba,you're my one and true love ummu hakeem".

Yakarasa maganar yana riqo hannunta wanda yasha maroon din lalle,cikeda birgewa yake kallon hannun yana murzawa ahankali yana jiran amsar ta,ajiyar zuciyah ta sauke mai nauyi tana kallon fuskar mijinta cikeda tsananin sonshi,tana kaunar mijinta kauna mai cikeda girmamawa,mutuntawa dakuma darajawa,zata so su Cigaba da gina rayuwarsu kamar yadda suka faro,sai de hakan bamai yiwuwa bane,dole ta daure takuma jajirce domin ganin ta musanta zargin da gwaggo ke mata acikin kowacce daqiqa na rana,hakkin tane tazama glue din dazai gyara tsakanin ta da uwar mijinta dakuma tsakanin mijinta da mahaifiyarshi,zatai hakan ne domin wanzuwar farin ciki acikin rayuwar su.

Murya na rawa tace"Abu hakeem kasan mene ne burina?".
Kallonta yayi nawani lokaci sannan yace "ni ne burinki ummu hakeem,kasancewa ta mijinki shine burinki na biyu,mu kasance tare har karshen rayuwarmu shine burinki na uku".
D'aga kai tayi hawaye masu zafi na zubo mata tace"hakika banida burin daya wuce kasancewa tare dakai abu hakeem,saboda tsananin son danake maka wanda akullum yake karuwa,son gyara tsakanina da gwaggo,dakuma gyara tsakaninku shine  burina kuma Ina fatan zaka fahimce ni".

Lumshe idanu yayi yakasa cewa komai,zuciyar sa na lugud'en daka,ya tabbatar ta gama yanke hukuncinta,domin yasan matarshi farin sani,yasan tsananin kishinta,abinda zai sa ta yanke wannan hukuncin ba qarami bane,yasan takurawar gwaggo ce ta jawo hakan,yace"ba dole sai ke dakanki zaki kwance daurin zaton da gwaggo tamiki ba,kibawa lokaci damarsa domin ya warware komai ta hanyar da bamuyi tunani ba,amma dole sai Kinyi hakuri kin kuma jajirce,domin baka zuwa matakin nasara batareda hakuri ba,nasan kin yi iya bakin kokarinki, Allah ya baki lada"

Janye jikinta tayi ta tsugunna akan gwiwarta,hawaye masu tsananin zafi da sauri na zubo mata,tace"dan Allah abu hakeem grant my wish,nagaji da abubuwan dasuke faruwa,zuciyata na bukatar hutu,kaine kadai keda ikon share min hawayena,kar ka zuba min kasa a idanu...".

Sosai Ammi ta shayar dashi mamakin gaske,wani irin yanayi ya tsinci kanshi wanda be taba shiga irin sa ba,yace "kada ki tursasani yin abinda banyi niyya ba,dan haka mubar maganar nan banason ki kara yinta "ya Cigaba"bazan gaji da Baki hakuri akan abinda gwaggo ke miki ba,amma yazama dole na fada miki wani abu dabaki sani ba,badan komai gwaggo ke san na qara aure ba sai dan ta muzguna miki,sannan qarin aurena bazai sa ta soki ba,dan haka na kashe maganar nan banason qara jinta ".d'agota yayi ta zauna a mazauninta na farko,idanuwansu ya sark'e dana juna kowa na saka abubuwan kala daban daban,Shigowar Asal ce ta sa Ammi sauke ajiyar zuciyah tana kallon Yarinyar mai kama da babanta,da gudu takarasa cikin dakin tareda d'anewa jikin baban tana qyalqyala dariya,murmushi sukai alokaci daya Ammi tace"ke da wa?"
"Nida gwaggo "tafada tareda rufe fuska alamar kunyah,murmushi Ammi tayi ta miqe tana jin sanyi aranta,hakika dukkan tsanani yana tareda sauki,ta ga hakan kuma ta shaida,domin gwaggo ta isa zama misali agareta,gwaggo bata santa amma tana son 'ya'yanta Sosai,sannan gabadaya jikokinta nada special place acikin zuciyata,tana tsananin sonsu da kaunar su.

———-
   Zaune nake a front seat na primary 3 ana mana social studies,amma gabadaya hankalina baya ajin,ya karkata izuwa gidanmu wanda zaifi kyau na kirashi da sansanin yaqi,zuciyata cikeda takaici dakuma bakin cikin qarin aure da baba zaiyi,ganin yadda mama ta daga hankalinta Sosai,hawayen danake kokarin dakatarwa sukai nasarar zubo min,saina kife kaina akan desk ina sauke ajiyar zuciyah,I just want the best for my parent,matsalar su na affecting dina ta yadda basa zato,qawata Aydah ce ta dora hannunta agadon bayana sannan tace"ki miqe kada mr lawal ya ganki"maganar datayi yajawo hankalinsa zuwa garemu,da fada yace"sultana Yusuf sit up".jikina na rawa na dago ina kallonshi da dara daran idanuna,yace"stand up"miqewa nayi jiki na na rawa yace"what's value?"kasa bashi ansa nayi haka ya kara ci fadan sa yagama,k'arfe biyu daidai aka tashe mu,class dinsu Amal naje na riqo hannunta sannan muka kama hanyar zuwa gida,tundaga tsakar gidan muke jin hayaniyar mama sai fada takeyi,zama mukai a compound hawaye na racing daga idanuna,bayan kimanin 10mins tafito tsakar gidan tana huci,ganin mu ya qara bata mata rai,da fushi take fadin"dan ubanki shine kika zauna anan?"
"Yanzu muka dawo"nafada bakina na rawa,tsaki tayi ta shiga kitchen nayi saurin shiga falo inda baba ke zaune,ya dafe kanshi mai tsananin sara mishi,yana danasanin amincewa gwaggo,domin shi kadai yasan tashin hankalin dayake ciki,kallon mu dakuma kasancewar mu 'ya'yanshi ke sashi murmushi awannan lokacin.
Batareda yace komai ba ya rungume mu alokaci daya yana sauke ajiyar zuciyah masu nauyi,kalamai ne sukai masa nauyi Sosai,ya lumshe idanu yana jin kaunar mu na ratsa jininsa,jijiyarsa dakuma tsokar sa,kiran da mama ke min yasa shi breaking hugg din yana sakar min murmushi, natashi jiki ba kwari na tafi,abakin kofar kitchen din na tsaya,kallon data watso min yasa nayi saurin saukar da ido na kasa jikina yafara rawa alamar tsananin tsoro

SULTANA...Where stories live. Discover now