PAGE 6

303 25 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺

https://chat.whatsapp.com/BLdx9bHgeXYLao2QAjarGc
(Guguwar zamani fan page for more updates)

PAGE;6

Haka rayuwa tacigaba da tafiya dasu ,ta hanyar  dasuke tafiya suna haduwa da tudu dakuma gangare,rayuwa gabadayanta trial and test ce,hakuri dakuma jijircewa da addua ne ya zamto makamin wasu daga cikin su,ita zuciyah wata tsoka ce ajikin dan adam wacce Idan ta gyaru to dukkan sauran jiki ya gyaru,Idan kuma ta baci to dukkan jiki ya baci,Idan akayi amfani da wannan maganar zaa iya cewa zuciya ce sarauniyar gabaki daya jikin mutum,wacce kuma awani alokuta da dama tana mulkinta ne  akan son kai musamman Idan aka samu cewa shi mamallakim zuciyar baya iya juyata,ya sakar mata ragamar yin abinda take so.

Shekara daya dana kara cikin rayuwata ,shekara ce wacce ta kafa babban jigo acikin rayuwata wanda bazan iya bada labarina batareda na saka taba...rayuwa ta agidan mu ta waccen shekarar ta banbanta data yanzu,sede alaqar dake tsakanina da mama data qara nisa kamar yadda sama taiwa kasa nisa,hakan baya rasa nasaba da sona da anty jameela keyi tamkar ita ta tsugunna ta haife ni, take mu'amalanta ta cikeda kauna,juriya,hakuri dakuma kyautatawa,tana takatsantsan da dukkan abinda zai bata min rai,ta mayarda ni shalele abar kaunarta acikin kowacce dakika ta rana,wannn soyayyahr datake nuna min yasa zuciyar baba saukowa daga fushin da ya hau,ya kaunaceta,cikin qanqanin lokaci mama ta zama yar kallo,wannan lamarin ne ya zamto mafari kuma tushen kaddarar rayuwata....

Mistake din mama nafarko shine ta manta Lokacin da kake  uwa kana canzawa da kimanta abubuwan da Baka gani ba a da. Lokacin daka zama uwa dole ne kayi ƙoƙari ka inganta kowace rana.

Kwakwalwarta kalau take bare ace lalura ke hanata bamu kulawa,ita bata ma san cewa kuskure take aikatawa ba,A nazarin ta da lissafin ta koda yaushe ita ce farko kafin d'anta,shiyasa take gabatar da farin cikinta kafin na d'anta,kulawa wadda ke karkata zukata ga nuna tausayi da damuwa ga mai bayar da ita bata shiga tsakanin mu ,wannan sakacin nata ne ya zama babban kalubale dakuma jarabawa acikin rayuwata.

——
duk wata mace tanada kishi,sedai kowacce mace akoi salon yadda take tafiyar da nata kishin ,Tabbas kishi halas ne,yake Ammi kiyi kishi irin na matan Annabi,kiyi kishin daya halasta,kiyi kishi irin na masu hankali,kiyi kishin da za'a gane cewa lallai ke mace ce,sannan kiyi kishi irin namasu ilimi,kiji aranki bazaki iya cutar da matar mijinki ba haka kuma kisa aranki bazata iya cutar dake ba,dukkan ku abun halitta ne wanda babu wanda ya isa ya cutar dawani,bazata iya miki komai ba haka zalika kema baki isa kimata abinda Allah bai qaddara faruwar Saba,sawa aranki nacewa bazaki cutar da ita ba shine zai kubutar dake agaban mahaliccinki,Amatsayinki na mutum mai hankalin yin nazari kafin ki gabatar da kowani abu yana da muhimmanci ki nazarceta sannnan kiyi tunanin wanne irin zama yakamata kiyi da ita,ki lura da wacce irin fuska take mu'amalantar ki kafin ki dora tubalin zama da ita.ba'a nunawa  kishiya kishi afili,duk yadda kike da kishi kiyi kokarin danneshi agabanta,domin idan tagane kinada kishi mai zafi zata samu wata dama ne ta dalilin wannan kishin naki,ki kama kanki awajenta,keda kanki ki girmama kanki to itama zata girmama ki,baa sakewa da kishiya gabadaya kuma baa daure mata fuska gabadaya tsaka tsakiya dai,kizama mai mutunta kanki amma kada ki rainata,sannan kisan irin hiran dazakiyi da ita,Ammi bakida lokacin gulmar kishiyar ki saboda babu abinda gulmar zata amfanar dake sai daukan zunubi dakuma bata lokacinki abanza,ita wacece dazaki tsaya kina gulmarta?"

Numfashi mai Nauyi Ya gumsu tasaki takuma cewa"Na rantse dawanda raina ke hannunshi kika riqe abinda nafada miki  sai kin zauna da ita lafiya,bazaki gushe ba har sai kinga canji acikin rayuwarki "

Ajiyar zuciyah Ammi ta sauke tana tuna nasihar ya gumsu sanda abu hakeem ya kara aure wata uku dasuka wuce,har yanzu ta kasa sabawa da new normal dinta,har yanzu zuciyar ta namata ciwo tun ranar da aka daura ma abu hakeem aure da macen da ba ita ba,dama haka zafin kishi yake da radadi?Dama haka maman sultana taji sanda mijinta zai kara aure?Dama haka mata ke ji alokuta mabanbanta idan mijinsu zai kara aure?tabbas mata na namijin kokari arayuwa,ta lumshe idanu hawaye masu zafi na zubo mata,har yanzu takasa sabawa da rashin abu hakeem akusada ita akowani lokaci...ashe dama duk cika baki takeyi a lokacin baya,lokacin da take roqonshi akan aikata hakan,ashe dama Shirme takeyi?tsananin tunani,dakuma damuwar meze je ya dawo ne yake addabar ta,duk da confirmation dinda abu hakeem ke bata acikin kowacce daqiqa ta rana,kalmar hakuri ta dauka tasa acikin zuciyarta,ta tsananta addua da tsayuwar dare,hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba.

——
    Masu iya magana nacewa hali zanen dutse ne,kamar yadda raayi ya zamto riga,kowa da kalar tasa, canza halayyar dan adam na da matukar wahala,sannan duk wanda ke muamalantar ka ta sigar dabatada dace ba yasani,rayuwar Zainab data mamanta bata canza ba,saima sabon salon data dauko,bakin ciki ne cikeda zuciyar Zainab,wata hudu dasuka wuce ne tasamu sassaucin halin datake ciki,school dinda tafara ce take dauke mata hankali alokuta da dama,ta zuba mishi ido ne taga iya gudun ruwanshi,domin duk inda mutum yakai ga rashin kirki akwai ranar nadama.

K'arfe uku da rabi Zainab ta kutsa kai cikin gidan bayan mai gadi ya bud'e mata gate,gida ne mai girman gaske dauke da parts hudu aciki,part din farko wanda yafi kowanne daukar hankali shine na gwaggo,ta gefensa shine na Zainab,ta dayan gefen part din Ammi ne da kishiyar ta Anty,suna opposite da part din maman sultana da Anty jameela,kowani part Idan ka shiga zaka tarar da corridor,acikinsa akwai kofofi guda biyu,acikin kowacce kofa akwai qaton falo,dining,kitchen,3 bedrooms dakuma 3 toilets...part din Ammi dana gwaggo ne suka banbanta dana saura,3 bedrooms ne a part din gwaggo,kitchen sai parlo da toilets,yayinda part din Ammi ke dauke da 2parlors,4bedrooms,4 toilets,kitchen,dining dakuma store...zumunci wani halataccen mu'amala ce daya dakko usuli tun halittun farko,yana da muhimmanci da alheri acikin sa,wannan dalilin yasa daddy Wato abu hakeem yanke shawarar zama gida daya da yan uwanshi domin inganta dakuma gyara rayuwar junansu,ta haka ne zasu zama tsintsiya madaurinki daya,sannan 'ya'yansu su samu kusanci da juna yadda ya kamata.

✍🏼By Zaynab Yusuf
guguwar zamani is a must read sannan free book ne,just share domin wasu su qaru dashi,kuskuren danayi Allah ya yafe min,my inbox is open for corrections,comments and advert,just slide into my PC.)

SULTANA...Where stories live. Discover now