PAGE 16

191 23 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

PAGE;16

  Da murmushi mai sanyi dakuma birgewa na bud'e idanuna,na kalli window wanda rana ta bullo ta cikin sa,tunanin kalaman Al'ameen nakeyi masu saka min nutsuwa da farin ciki,musamman na jiya,domin a jiya ne na amince masa,nima na bayyana masa sirrin dake raina,baki da baki,hakika ba abinda yakai fira da masoyi dadi aduniya,gabadaya Ina jina wata different,kamar an canza ni completely saboda I'm totally in love with Al'ameen,wanda yagama zagaye jinin jikina,agaggauce nayi wanka kasancewar yau Thursday akwai school,na shirya cikin uniform dinmu masu kyau,alokuta da dama Al'ameen na cewa ni ce ke karama kayan kyau,kullum sai ya bayyana min baiwar kyan da Allah ya min,wasu lokutan nakan tuna kalaman yaya Hakeem agareni marasa dadi,abu kadan yace zai wanke mummunar fuskata da mari.

Na saki siririn tsaki tuno shi danayi,afalo na tarar da ummu tagama had'a breakfast tana saka turaren wuta mai dadin kamshi,na gaisheta sannan naci abincin muka tafi school.

Kallona Fareeda keyi tana mamakin murmushi danakeyi alokuta mabanbanta,tace"Tabbas kin fada abinda kike cewa Muna b'ata lokacin mu akai,gashi ma kamun daya miki yafi namu sau dari ".
Harara na zabga mata sannan nace"kyaji da munafurcinki bazakiji komai daga bakina ba"murmushi tayi kasancewar ta mai sanyi hali ba irina ba,kowa na jinjina karfin friendship dinmu kasancewar ta mai hakuri da sanyi nikuma akasin haka.
Shirun data min yasa banji dadin maganar dana fada ba,nace"sorry qawata,zan baki labarin amma sai mun hadu agida".
Murmushi tayi tace"sultana kenan me abubuwan ban mamaki".Daga haka bata kara cewa komai ba,na fahimci taji haushin maganar ne kamar yadda nima banji dadin fada mata ba,at first nayi hakan ne domin banason kowa yasan abinda ke tsakanina da Al'ameen har sai lokacin daya dace.

K'arfe biyu da rabi muka dawo gida agajiye,direct part din gwaggo natafi saboda ummu tafada min zata fita kuma sai dare zata dawo,kwanciya nayi a doguwar kujera Ina maida numfashi,gwaggo na kallona kasa kasa tace"lalaci yamiki yawa yar qaniya,maza huta ki gyarawa Hakeem d'aki gobe insha Allah zai dawo".

Zumburo baki nayi gaba batareda nace komai ba na kifa kaina cikin kujera Ina jin haushinsa na ratsa ni,ban taba ganin mutumin danayi despising kamar shiba,sai na miqe jiki ba kwari na dauki tsintsiya da Parker sai mop da ruwan omo,na dauki key inda gwaggo ta ajiye sannan na bud'e dakin,wani hadaddan kamshi ne yayi min sallama tamkar yaya Hakeem din na nan,yau ce rana ta farko dana fara shiga dakinsa Turquoise blue furniture's ne aciki masu bala'in kyau,komai a gyare atsare yake a dakin,saina fara cire zanin gadon na shimfida sabo,sannan nayi shara da mopping na wanke masa toilet Ina zunbura baki haushi gabadaya ya mamaye zuciyata,fitowa ta daga toilet naji qarar wayata,nasaki murmushin jin dadi ganin Al'ameen ne me kiran.

Fira mukeyi ina goge masa furniture's na koma varander zan gyara,cikeda mamaki nake kallon robar cin cin da meatpie din damukayi da nussy awurin,take naji wani bakin ciki ya tokare min wuya,nace ma Al'ameen "Ina zuwa"sannan na kashe wayar zuciyata namin zafi,natsani wulakanci arayuwata,Idan baze ciba ay saiya fada amma yayi mana asarar shi gabadaya,na buga tsaki sunfi goma sannan na dauki robar na ajiye agaban gwaggo tareda kalmashe hannayena akirji,ita kanta lamarin ya bata mamaki ta d'ago da sauri,sai kuma ta tab'e baki tace"lafiya?".

Nace"shiyasa tun farko ban so kika bashi ba,saboda nasan adadin tsanar daya min,ko abu na tab'a baya amfani dashi bare yaci abinda na girka,yanzu ya kyauta kenan?a varander fa na tsinto shi "na karashe maganar cikin bacin rai bayyanan ne.

"Abu ne kinyi shi ba fasali bare sha'awa,tayaya mutum zeci abu mara dadi?".
Raina Idan yayi dubu ya b'aci,nasan ban iya girki ba,bansan yadda akeyi ba,amma na iya snacks kwarai da gaske,domin duk wanda yaci sai ya nemi qari,daki na koma domin na lura bayansa gwaggo ta goya,na kwanta ina nazari mai zurfi,kamar amafarki mamana tafado min arai,take naji kaunar ganin ta Alokacin,saina miqe na nufi part dinta,a kitchen na tarar da ita tana juye ruwan zafi a flask,muryata nadan rawa nace"mama ".
Bata juyo ba kamar yadda nayi tunani,ta chigaba da sabgar gabanta,"Ina wuni mama "nafada akaro na biyu duk da inada tabbacin ba amsawa zatai ba,hawaye masu zafi suka zubo min,nakarasa daf da ita nace"dan Allah kimin magana"nafada akaro na uku,sai alokacin ta dago da fuskar ta takalle ni,kallon daya sa hantar cikina kadawa tace"fice min da gani sultana,bana son ganin fuskar ki,ki koma inda kika fito,wurin uwarki jameela".

SULTANA...Where stories live. Discover now