PAGE 9-10

151 15 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.

                  PAGE:9-10

    Cikeda tsantsar damuwa yake driving har ya karasa gidan su sultana,sai ya tsaya abakin gate zuciyar shi na dukan goma goma,gabadaya tunaninsa ya tsaya cak,kiran wayarsa da akayi ne yasa shi kallon wayar akaikaice,sai kuma yayi saurin dagawa ganin Jidda ce ke kira,da fada yace"Ina kikaje batareda izini na ba?".

Ranta gabadaya ab'ace yake tun gabatowar bikin musamman yadda dr shuraim ke rawar kai gameda auren,sai taji wani takaici ya rufe ta,tace"gidan yaya bilqis naje "tafada atakaice tana jin haushin sa mai tsanani.

Yace"shine dan wulakanci baki fada min ba?"da mamaki ta maimaita kalmar "wulakanci?"saita runtse idanu tana lissafa sababbin halayen dr shuraim saboda zai kara aure,tace"nagode da duk abubuwan daka ke min,da maganganun daka ke fada min marasa dadi saboda zakayi sabon aure,wato yanzu nazama kwallon mangora mara amfani wacce kake alla alla ka yar,duk wanda yayi nagari kanshi,kuma bazan daina fada maka ba,Wallahi tallahi bazan dauki rashin adalci ba,aduk sanda naga hakan consider our marriage over"tana gama fadin haka ta kashe wayar hawaye masu zafi na zubo mata cikin rashin kakkautawa,wani bangare na zuciyarta yace"c'mon kukan me kikeyi?kuka saboda za amiki kishiya?awani dalili kike asarar hawayenki saboda wata kishiya?ki goge hawayenki ki jajirce,Idan yana kwatanta adalci azauna lafiya Idan kuma baya kwantatawa kowa ya kama gabanshi,tunda har shi ya iya miki kishiya Duk da yana sonki meyasa ke baza ki nuna abin bai dameki ba?saita share hawayenta ta shiga bedroom tana tunani yadda zaman nasu zai kasance agida daya.

Da karamin mamaki yakalli yadda jidda ta kashe kiran,sai yayi kwafa sannan ya danna horn,domin sai alokacin yasamu courage din shigowa gidan mu,kiran wayata yayi lokacin na fito daga wanka Ina shafa mai,da dan murmushi na daga wayar,yace"nazo".shine kawai abinda yafada ya kashe wayar.

Da kallon mamaki na bi wayar batareda nayi tunanin komai ba na zura doguwar rigata mai kyau nayi rolling da matching color veil,perps na fesa masu sanyin kamshi sannan nafita tsakar gida,fuskarshi kadai ta isa ta shaida min akwai matsala domin ahade take kamar hadarin gabas.

Kamar rakumi da akala yake bina har muka shiga falon ummu,zan wuce kitchen na hado mishi abin motsa baki sai yayi saurin tsayar dani,"dawo magana zamuyi mai muhimmanci,"atake gabana yayi tsananin faduwa,amma na dake na dawo na zauna ina kallon idanun shi wanda sukayi jajir,baice komai ba ya miqo min wayarshi nakarba,idanuna suka ci karo da message din daya kusa fito da zuciyata waje.

"Ango kasha kamshi,ko kuma nace angon bazawara,Idan bakada labari,sultana da kake gani ba yarinyar arziki bace,tagama tambad'ewar ta awaje,tagama lalacewa da mazan banza ,zakafi yadda dani alokacin data zamto taka,saika tabbatar da kanka,wataqil ma ta shigo gidan ka da tsarabar juna biyu".

Hawaye na zubo min na kalleshi shima kallona yakeyi yana kallon reactions dina,sai alokacin ya karbi wayar ya bud'e wani tareda miqo min,hannuna na rawa na karba,Ina karantawa Ina kuka saboda tsananin tashin hankali.

"Sai murna kake kana rawar kai zaka auri sultana ko?sultana ragowar Al'ameen wacce ya gama amfani da ita alokuta mabanbanta,dakuma sauran samari bila adadin,don't make the mistake of getting married to her,saboda zakayi dana sani mara amfani,domin Idan ka aureta kaida farin ciki kunyi hannun riga,sannan baza kaso ka auri fasika ba wacce tagama iskanci awaje,bade zaa ce bamu fada ba".

Wannan message din yafi min ciwo domin har da sako marigayi Al'ameen aciki,wanda nakeda tabbacin ba halinsa bane kawai anyi amfani da shi ne saboda a lalata min rayuwa,kuka nakeyi mara sauti domin Tabbas dr shuraim yafara yarda da messages din,sai ya qara karbar wayar akaro na uku ya budo wani message din ya miqo min,tamkar bazan karba ba naji sautin muryarshi ta daki dodon kunne na"karba mana"yafada yana kara turo wayar gabana.

SULTANA...Where stories live. Discover now