PAGE 3-4

185 15 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO(2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.



PAGE:3-4





Washegari misalin k'arfe sha daya na safiyar lahadi Umar ya iso gidan,cikin shigarsa ta yan kauye sak, ya wadata fuskarshi da fake gashin baki dana gemu dakuma na gefe da gefe,kanshi sanye da wata sky blue hula wacce taga rayuwa,zaren da akayi hular sun zazzaro waje,ta baya ma ab'arke take,kayan jikinsa kadai zasu tabbatar maka da yana cikin talauci mai tsanani,wandan shadda yasaka dark green wacce tafara fari fari saboda tsabar kodewa,ya dora Farar rigar shadda wacce takoma milk color saboda tsufa,kamanninsa kadai ya isa ya baka tausayi Idan mutum mai karfin imani ne.

Hannunshi riqe da jakar viva,littattafan addini ne aciki,Al'qur'ani mai girma,sai fiqhu,tauheed,Arba'una Hadith,tajweed,seera dakuma hisnul muslim.Sai dari biyar dake aljihunsa,wayarshi nacikin jikinsa bayan ya kasheta gabadaya,lokacin daya shigo gidan su daddy na zaune a tsakar gida akan carpet na alfarma dan turkey mai matukar kyau da tsada.ya kishingida akan tumtum yana shan fura dayake shi ma'abocin ta ne,abba da baba na gefe suna shan fruit salad,Hakeem da Aliyu suma na gefe daya.

Daddy yace"dama akan business dinka ne Hakeem,dafarko nayi tunanin fada maka maganar kai kadai,Toh amma babu fa'idar aikata hakan,tunda family business ne Yakamata ace kowa yasan mai ake ciki,kudinka danake juyawa sun yi yawan gaske wanda ya zarta tunani na dakuma lissafi na,domin har yanzu ban kammala lissafin adadin dukiyarka ba acikin tamu wacce nakeson mufara warewa kafin azo mataki na gaba,mataki nagaba shine Idan zaka cigaba ne ko kuma zaka yi investing awani wurin wanda zaiyi daidai da aikinka,wanda kuma bazai shiga hakkin aikin ka ba".Cikeda mamaki abba ke kallon daddy,baba yace"Masha Allah, Allah ya kara arziki mai albarka".

Amin sukace gabadayan su daddy yacigaba da cewa"kamar yadda kowa ya sani,kuma ya shaida,Yusuf ya zubama yar shi hannun jari acikin kasuwancin mu,itama cikin hukuncin Allah kudinta na qara daraja,abinda yasa na tara ku anan shine Ina son awarema kowa kudinshi ne sai asake sabon lale".

Baba yace"gaskiya hakan zaifi,gara asan adadin kudin kowa tun kafin tafiya tayi nisa asamu matsala,domin kudi are evil,suna shiga tsakanin uwa da d'a dakuma uba da d'a"murmushi daddy yayi yace"abinda nake nufi kenan,munada records din komai kawai warewar zamuyi Insha Allah ".

Gaban Abba ne yafadi,wani abu ya tokare mishi wuya mai dacin gaske wanda yake neman ya toshe hanyar wucewarsa,ganin gabadaya shi atutar babu zai tashi aganinsa,wato daddy da baba sun hada baki sun saka ma'ya'yan su hannun jari acikin business sai wahalta musu yakeyi ba dare babu rana gashi yanzu za'a raba dukiya batareda danshi ya samu sisin kwabo ba,bama haka ba,abinda yafi damunshi shine dalilin daddy na tattago wannan maganar.

Daddy ne ya katse mishi tunani da fadin"nasan tunanin me kakeyi ahmadu,dan haka zan ba Aliyu kudi masu dadi,Idan yana so yasaka share a kampanina Toh,Idan kuma he's interested in some other business ne sai na bashi kudi yafara,sannan aduk aikin da akeyi a shago kowa nasamun rabonshi rabo mai tsoka,kai da yusuf ne kasonku ya dara na kowa acikin manager's dina,yayinda kason ku yayi daidai danawa dakuma Hakeem da sultana,ahmadu kar ka manta sanda na zo maka da wannan maganar,alokacin dazan saka kudaden Hakeem, nace ka kawo wani abu ni zan cika amma kak'i k'ememe,kana gani daga baya yusuf ya zuba kudin sultana amatsayin ta na mace,wanda dasu zata taimaki kanta dakuma 'ya'yanta nan gaba,it isn't too late,Idan zaayi sabon zubi saikayi kokarin zubawa ayan".

Murmushin yake Abba yayi yana tunanin inda zai bullowa lamarin,domin yanzu babban tashin hankalinsa shine ya deb'i kudade masu yawa ya zuba acikin wani online business,ance mishi a sati biyu kudin zasu ninka kansu,gashi yanzu sati uku tawuce,ga kuma babban lissafin da daddy keyi,wanda babu jimawa zai iso kan wannan kudaden.

SULTANA...Where stories live. Discover now