BOOK 2 PAGE 1-2

179 14 1
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

                    (BOOK 2)

        Exquisite writer's forum.

                   PAGE;1-2



       Bismillahr Rahmanir Rahim.





     Kafin ya ankara shima ya ji saukar dusten agoshinsa,atake wutar jikinsa ta dauke domin ba karamin bugu akai mishi ba,ya runtse idanu tareda sakin hijabin mutumin ya gudu cikeda sassarfa domin shima yaji jiki,dafe kanshi Hakeem yayi wanda jini ke fita kadan kadan,ya kuma dafe qeyarsa yana kallon hanyar da aka bi,tabbas hanyar part din mami ce,kenan abba ne dukda bai bud'e fuskar ba,zuciyar shi tagama tabbatar mishi akan abba ne keda sa hannu acikin matsalar,sai ya miqe ya koma part din gwaggo yana tunanin yadda Abban ke wasa da hankalinshi,wato fito dashi yakeyi domin yamishi illa,ya girgiza kai tareda lumshe idanu bacci barawo ya saceshi.

Washegari k'arfe goma na safe ya farka da tunanin abin da ya faru jiya,sosai lamarin ya tsaya mishi akirji yana jin haushin abba mai tsanani,yana kuma kara damtsen kama abba dumu dumu tahanyar da baiyi zato ba dakuma tsammani,domin yanzu baida wata hujja mai kwari data nuna abban ne keda sa hannu,amma he's no 1 suspect kuma jikinshi nabashi abba nacikin wannan badakalar dumu dumu,Idan ma cultism yakeyi wacce riba yake samu wacce bai samunta a kasuwa?sannan shi bai yazama wani shahararran mai kudi ba,Toh menene dalilin shi na aikata hakan?sannan mecece matsalar shi?Ganin baida amsoshin tambayarshi yasashi miqewa ya shiga toilet ya watsa ruwa,ya shirya cikin wasu white top da black jeans masu matukar kyau wanda suka dace da fair complexion dinsa,sai da yagama fesa perps masu dadin kamshi da son kasancewa da wanda ya mallakesa,wayarshi dake haske ya kalla,sunan Umar ne ya bayyana asaman screen din,sai da takusa katsewa sannan ya daga,yace"tun jiya nake neman layinka bata shiga".

Ta daya bangaren Umar yace"haka Heekmah ke fada min,simcard dina keda matsala".

Hakeem yace"dama wani aiki na kawo maka amatsayin ka na dan sanda wanda ya kware akan aikinshi,aikin ba iren iren ayyukan dakuka saba ta'amalli dasu bane,domin sunada birkita tunanin mai tunani su barshi acikin kokonto dakuma waswasi,aikin ne daya ke buqatar full attention dakuma over smartness,aiki ne dayake buqatar ariqa analysing every single scenario of it,it's not a normal problem domin inada tabbacin ana amfani da aljanu acikinsa,amma zuciyah ta tafi karkata akan sihiri ne".

Shiru Umar yayi nawani lokaci sannan yace"nafahim ci inda ka dosa,saide Ina son kafada min ainihin abubuwan dasuke faruwa da kuma no 1 suspect dinku,da kuma sauran suspect din da hankalinka bai kwanta dasu ba".

Miqewa tsaye Hakeem yayi ya je gaban windows dinshi ya daga curtains din yana kallon gefe da gefe sannan yafara fadin"kamar yadda kasani daddy shine babban dan gwaggo wato mahaifina da Nurain da Asal,sai baban sultana baba yusuf sai kuma abba baban su Aliyu,wanda shine no 1 suspect dina a cikin wannan matsalar,problem din cikin gidane amma lamarin ya zarta hankali,abinda yafara faruwa itace rashin lafiyar sultana,tabbas bata asibiti bace kamar yadda drs suka fada da dama,sai rasuwar qanina Nurain wacce gawarshi tayi kama da wacce akaiwa lahani da gangan,sannan gobarar damukayi data kusa durkusar da dukiyar daddy ,acikinta ne Qanwata Asal tasamu wani iri ciwo wanda ke kama dana sultana,sai kuma rasuwar Al'ameen wacce gawarshi iri daya data Nurain,dakuma gaba da gaba danayi da culprit din jiya da daddare har yayi nasarar fasa min kai da dutse bayan na kaucewa sarar wuqa".

Umar yace"kwarai aikin nan yanada wahala kuma yana bukatar lissafi akowacce gaba kafin a aiwatar da abu,sannan kayi mistake daka bari aka fahimci kasan da abinda ke faruwa,har ma suna wasa da intelligence dinka,suna amfani da wannan damar suna kiranka kai kuma kana fita,kamar dai suna maka kida ne kana taka musu rawa,domin ba tayyada zaayi ya cigaba da kulla sharri bayan yasan Kasan dashi,ana dauke maka hankali ne adaidai lokacin da ake Cigaba da kulla makirci,amma kayi kokari sosai sojan sama,saide wannan aikin namu ne na police".

SULTANA...Where stories live. Discover now