PAGE 7-8

156 14 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.



                     PAGE:7-8

  Ahankali ta bud'e idanunta dasukai mata nauyi,hawaye basu daina fita daga idanun ba,ga wani azababben ciwon kai daya saukar mata,akan fuskar mama tafara sauke ganinta,saita yi saurin janye fuskarta gefe tareda fashewa dawani mahaukacin kuka,ga wata azababbiyar kunyar mama dafa saukar mata alokaci daya,Farhan dake gefen mama tace"tafarka alhamdulillah"tafada tana rungume mama iya karfinta.

Sosai abinda ya faru ya sosa ran mama matuka,domin taji zafin sakin da kabeer yayima kareema har uku,babu wata hanya ta sulhu dole ta bar cikin rayuwarshi,Saida ta riqo hannunta sannan tace"kiyi hakuri Kareema,ki karbi kaddara aduk yanayin data zo miki,sannan kiyi murna hakan tafaru tun kinada sauran lokaci aduniya,wanda zaki roqi yafiyar ubangiji,abinda kika manta alokacin baya shine bakayin alheri ka lalace,kuma bakayin sharri kagama lafiya,taki tayi kyau,dan haka shawarar dazan baki itace ki koma ga Allah"ta sauke ajiyar zuciyah sannan tace "Allah ya jikan rai yasa ta huta".

Afirgice Kareema ta miqe tazaune tana kara fashewa da kuka mai ban tausayi,"Innalillahi wainna ilaihi raji'un,Wayyo Allah hajiya".Sosai Farhan ke kuka itama tana lissafa yadda rayuwarsu zata kasance,jiki ba kwari mama takoma dakinta cikeda zullumin abinda yafaru.

Kiran Mami tayi lokacin tana zaune ta rafka uban tagumi,bakomai ke damun ta ba sai halin da Aliyu ke ciki,qarar wayarta ce ta katse mata tunanin,ganin kiran mama yasata sakin karamin murmushi tace "Barka da rana mama na fatan Kina lafiya?"

Tace"lafiya kalau alhamdulillah,anjima zamuzo gidanki da kabeer Insha Allah ".da tsantsar mamaki Mami tace"yaya kabeer fa kika ce".

Tace"kwarai dagaske,Ina farin cikin sanar dake yayanku ya dawo hayyacinsa,yafito daga cikin duhun asirin da kareema ke mishi,harma ya saketa saki uku,ga mamanta ta rasu,abin ya cakud'e mata,tana cikin tashin hankali mai tsanani ".

Ajiyar zuciyah mai sanyi Mami ta sauke tace"alhamdulillah,hakika Allah mai jibantar lamarin bawanshi ne,sannan mai amsa adduar bayinsa ne,gashi adduar mu ta amsu alokacin da bamuyi zato da tsammani ba,naji dadin wannan maganar Sosai "takarashe tana goge hawayen dake zubo mata,sallama sukayi lokacin Aliyu ya shigo part din,ganin hawaye a idanun Mami yasashi saurin karasowa har yana cin karo da takalmin ta,agabanta yazauna yana girgiza mata kai yace"Meya faru mamina?".

Ya tambaya kamar zai fashe da kuka,tace"yaya kabeer ya dawo kan hanya,asirin da kareema ke mishi shekara da shekaru ya karye,har ma ya saketa,hawayen farin ciki nakeyi,sunce anjima zasu zo".Murmushi Aliyu yayi yace"alhamdulillah,dama karshen azzalumi nadama,".

Sallamar daddy ce tasa Aliyu saurin miqewa,Mami tajawo mayafinta dake gefe tayi saurin rufawa,kallo daya zakama fuskar daddy kaga tsantsar b'acin rai dayake ciki,sai baba dake bayanshi shima fuskarshi cikeda takaici.

Daddy yace"Zainab kira min ahmadu "gaban tane yayi mummunar faduwa,jiki ba kwari tashiga bedroom din shi,atsaye ta tarar dashi yana safa da marwa,da dukkan alamu yaji shigowar su daddy,tace"daddy na magana".

Runtse idanu yayi batareda yace komai ba yafito falon yana kallon yayan nashi wanda ke cikin b'acin rai mai girma ,saida suka zauna suka fuskanci juna sannan daddy yace"miliyan hamsin ta b'ace akarkashin ka,tayaya hakan tafaru?sannan kada ka tsara min magana babu yadda zaayi asamu lost din miliyan hamsin,fada min mekai da wannan kudaden?".

Ya jefa mishi tambayar,cikeda dakewa yace"nayi amfani dasu nazuba hannun jari awani business,wanda nakeda tabbacin kudin zasu ninka kansu nan gaba"yafada yana kallon both of them,shiru sukayi nawani lokaci,daddy yace"fine,consider yourself out acikin rabon shago,duk abinda aka samu zan sanar dakai,Idan kasonka na shago yafi haka zan baka sauran kudin,kudin basu kai ba kuma Shikenan "ya miqe suka bar falon ahmadu yabisu da rakiyar idanu cikeda tashin hankali,hawaye ne ke zubowa Mami da Aliyu bakomai ke sata kukan ba sai rashin samun miji na gari dakuma uba nagari ga su Aliyu.

SULTANA...Where stories live. Discover now