PAGE 20

201 18 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wattpad @ Zaynab_yusuf

PAGE:20

Ahankali ya bud'e idanunshi wanda sukai mishi matukar nauyi,hakan baya rasa nasaba da gajiyar daya kwaso jiya na shirye shiryen graduation dakuma passing out dinsu da zaayi the next day,ya lumshe idanu tareda miqewa zaune yana jin wani irin feelings na daban,zuciyar shi wasai yanemi damuwar dake damunshi ya rasa awannan lokaci,qaramin murmushi ya saki sanda ya tuna wayarsu da Heekmah adaren jiya,yadda taki yadda tamishi magana ne ya burgesa beyond her imagination,hakika yana son mace mai class,wacce take aiwatar da lamuranta cikeda tsari dakuma lissafi,wacce take magana daddaya tamkar bazatayi ba,wacce murmushinta zai tamto tamkar sabon abu awurinsa dayake muradin gani akowacce dakika na cikin rayuwar shi,ga uwa uba salon maganar ta wacce ta tsaya cak abirnin zuciyarshi,yadda ta lankwasa harshe dakuma yadda ta yi maganar atakaice ne yakuma birgesa,hakika yarinya ta hada qualities dinda yakeda muradi gameda 'ya mace..gaisuwarta ce tazamto tamkar zinari Ko kuma sinadarin zinari mai walkiya a zuciyarshi akoda yaushe,ya girgiza kai sannan ya sauka daga gadon yana mamakin kanshi,is he really Hakeem?mai dakewa da daure fuska?mara shiga sabgar mutane bare yayi tunaninsu?sai gashi tunanin Heekmah ya zamto abu nafarko acikin ranshi,toilet ya shiga ya watsa ruwa still tunanin Heekmah na nukurkusar zuciyarshi,yana bege dakuma muradin jin voice dinta wanda yasashi kallon kanshi a mirror,yana karantar kanshi,shi da kanshi yake baiwa kanshi mamaki,domin tunanin Heekmah ya sanya annurin fuskarshi bayyana.Cikin wani sky blue jeans da white shirt ya shirya ,yayi bala'in kyau kasancewar Hakeem na cikin jerin maza masu kyan gaske,ga size wanda kowacce mace keda burin samu,yana cikin fesa perps yaji shigowar call,saida yagama fesawa sannan yakalli wayar yana sakin karamin murmushi ganin sunan Ammi ya bayyana akan screen,ya daga"amincin Allah ya tabbata agareki jannatid duniya,barka da war haka".

Ta daya bangaren ta lumshe idanu tana jin dadin kalamansa,tace"tareda kai dan albarka fatan kana lafiya"
Zama yayi agefen gado yana kallon dogayen fingers dinsa yace"lafiya kalau,fatan kowa na lafiya?ya Asal takara ji da jiki?"
"Da sauki alhamdulillah,dama akan maganar zuwan mu ne gobe insha Allah".Cewar Ammi tana kallon daddy wanda da alama he is lost in thoughts,lost in the world of his own memories,tace"gabadaya zamuzo,so make better preparations,sannan akwai maganar danakeson muyi gameda daddy".
Tacigaba"nasan abinda yafaru ba bane mai sauki daza mu manta nan kusa,kasancewar yadda muka rasa abubuwa masu yawa acikin gobarar data faru,ciki harda makudan kudin sa,gakuma jarabtar ciwon Asal da Allah ya qaddara,ga rasuwar Nurain wacce har yanzu take kafa sabon gurbi acikin zuciyar mu,amma daddy ya manta da cewar Allah ne ya halicci Nurain ta sanadiyyar mu batareda sanin muba,ya albarkace mu dashi,kuma ya qaddara bame tsahon rai bane,Sannan Allah ne yabashi dukiya alokacin da bamuyi zato da tsammani ba,ya azurtashi alokaci daya,miye dalilin daddy na rashin yadda da wannan kaddarar? bayan Allah SWA dakanshi yace"kuyi hakuri hakuri mai kyau",mutum baya alkhairi ya lalace haka baya sharri yagama da duniya lafiya,dan haka wannan maganar ce zata zama first thing dazaayi discussing muna dawowa gida Insha Allah ".

Ajiyar zuciyah mai nauyi ya sauke sannan yace"gaskiya ne abinda kika fada,kuma Insha Allah zan zauna da daddy kuma zanyi supporting dinshi dari bisa dari,zan Cigaba da taimaka masa a kasuwancinsa da nawa wanda ya dade yana min,kuma Insha Allah he'd be proud of me,domin bazan taba samun hutu ba harse na yaye mishi damuwarshi da yaddar ubangiji "
Hawayen farin ciki suka zoboma Ammi tace" Allah ya tabbatar da hakan,sannan yabamu hakuri dakuma juriyar overcoming every obstacle ".ya ajiye wayar yana kallon gefe,duk da tunanin Heekmah dake damunshi sai ya samu kanshi da kasa kiranta alokacin.

Tabangaren Heekmah kwana tayi tana miqa godiyarta ga Allah da ya sanya soyayyar ta dakuma kaunar ta acikin zuciyar managarcin bawanshi,mai takatsantsan da dukkanin lamuran rayuwarshi,mai kirki mai biyayya ga iyaye,wanda yasan mutunci dakuma darajar mace,acikin kwana daya daya bayyana mata sirrin dake ranshi yasa gabadaya ta rasa nutsuwarta saboda farin ciki,wanda saida Ummiy mahaifiyarsu ta fahimci hakan,suna zaune kan dining kowa na cin abinci banda ita data kurawa wuri daya ido tana sakin murmushi mai kayatarwa,Ummiy tace"sannu Heekmah kin kyauta"
Kallon Ummiy tayi tana jin matukar nauyinta tace"danayi me?".
"tunani mana,fadamin tunanin me kikeyi?"cewar Ummiy tana fahimtar yanayin 'yar tata.
Waro idanu Heekmah tayi tana kallon Ya Umar yana kunshe dariya,ta rasa inda zata saka kanta domin bata saba yiwa Ummiy karya ba,komai nata tasani,saide tana jin nauyin fada mata Wannan maganar.

SULTANA...Where stories live. Discover now