PAGE 19-20

213 20 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.



                   PAGE:19-20



     Bacci mai nauyi dakuma tsantsar gajiya nayi,domin se bayan kiran Sallar asubah na tashi dakyar na gabatar da tawa,nayi addu'oi masu yawan gaske wanda suka sa tunanin mama dawo min ya zauna daram abirnin zuciyah ta,dakuma maganar data min na ban hakuri,dama na lura da changes daga wurin ta tun kafin bikina,da bikin ne na kuma gasgata hasashena,Hawaye masu zafi na zubomin at the same time ina tuna lokacin da ummu suka kaini part dinta domin ta min fad'a,da mamaki na naji tace"kubamu wuri"sai suka fita itakuma ta fuskance ni"Sultana abubuwan dazan fada miki ba masu yawa ba ne,amma masu matukar amfani ne,nasan zakiyi mamaki na kwarai dagaske,ni na haife ki kuma nafi kowa sonki, dan Allah karki manta da hakan".

alokacin kuka ne ya kufce min mai tsanani saide bamai sauti ba.



Cikin rashin zato da tsammani naji tace "kin san wacece mace tagari?"

Ina cikin lullubi na juya kai alamar a'a sannan na cigaba da kukana.

Tace"Mace tagari ita ce wacce Idan Mijinta ya kalleta Zai ji farinciki ya lullubeshi.Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin Mijinta.

Ita ce wacce take mutukar kiyaye duk abinda zai 'bata ma Mijinta rai.Ita ce wacce take dagewa wajen bautar Ubangijinta.Ita ce wacce bata wasa da duk wani Hakki na mijinta.Ita ce wacce duk lokacin da Mijinta yayi fushi,bata samun kwanciyar hankali har sai ta yardar dashi.Ita ce wacce take Kiyaye Duk wani sirrin Mijinta.Ita ce wacce idan Mijinta ba yanan take Kiyaye mutuncin Kanta, da kuma dukiyar da ya bari agida.Ita ce Wacce take kulawa da Tarbiyyan Mijinta da 'ya'yansa koda ba ita ce ta haifesu ba..Ita ce wacce take mutukar girmama Iyayen Mijinta kamar yadda take girmama nata iyayen.. Kuma take kyautatawa 'yan uwansa ba tare da tsangwama ba.Ita ce wacce take zama da Makobtanta da kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa. Koda su suna munana mata.."

Tacigaba da fadin"Yadda zaki mallake zuciyar mijinki! Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba da sauransu , don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa.

Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa baza ki fita zuwa ko ina ba.Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya huta tukuna ya samu nutsuwa.

Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa akan abinda kika ga alamar yana nema ya karaya, hakan zai sa ya zama gwarzo a cikin maza.

Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau dayawa, dayawa dayawa, Aisha رضالله عنها tace Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta qarfin soyayyarta gareshi, sai tace mishi kamar 'zarge' (wato dauri ko kulli wanda bazai kwance ba), sai ya sake tambayarta 'yaya zargen yake'? Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi dake fiye da yadda kike farin ciki dani!.

Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa. Hakan zai sa ya qara dagewa.Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin aikin alheri,Idan yana cikin damuwa ki dan bashi lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai dai.

Ki dinga yi masa godiya akan sama miki abinci da muhalli da yake yi, abune mai girma!

Ki tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi wajen yanke hukunci.Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi haquri kuma ki dena.Kiyi dukkan abubuwan dana lissafo saboda Allah, sai kiga Allah ya sa miki albarka a cikin duk abinda kike yi."

SULTANA...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora