PAGE 11-12

151 16 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼



                PAGE:11-12

  Ahankali na bud'e idanuna tareda saukesu akan fuskar ummu,tasaki karamin murmushi sannan tace"ki tashi lokacin sallah yayi".saina miqe zaune Ina cigaba da kallon ta sannan nace"Meyasa ake Cigaba da shirye shirye bayan dr shuraim ya fasa aurena?bayan ya wulakanta rayuwata, abinda yafaru tabonsa baze taba barin zuciyah ta ba,dr shuraim ya cuce ni"nafada hawaye masu zafi na sauko min.

Ummu tace"kada ki damu,haka Allah ya qaddara,kiyi hakuri sultana,Zakiga ribarshi,musamman yadda daddy da gwaggo ke iya bakin kokarin su wurin ganin sun samo miki mijin dazakiyi alfahari dashi,mijin bugawa ajarida wanda zai riqe ki tamkar rai,ki ajiye batun so agefe for now,da aurenku zakuyi soyayyar ban mamaki".

Hawaye basu daina zubomin ba nace"bazan butulce ma zabin iyayena ba,amma wa kike ganin zasu aura min?".

Tace"ke kanki kinsan wa zasu baki"na dan waro idanu waje kadan sannan nace"Aliyu"tace"nima Aliyu nake tunani,haka kowa na gidan ma yake tunani duk da gwaggo bata yanke hukuncin karshe ba,amma alamu sun nuna shi zaki aura".

Ahankali na sauke ajiyar zuciyah sannan nace" Allah ya tabbatar mana da alheri "sannan na shiga toilet na daura alwala,sallar la'asar na gabatar tareda jero addu'oi kala daban daban.

Cikeda b'acin rai Abba ya fito daga part dinsa,ya shiga mota yana danna uban horn kamar zai tashi sama,cikeda nustuwa Umar ya bud'e masa gate sannan ya kira d'aya daga cikin detectives din dake biye da dukkan wani alamuran Abba,yasaki karamin murmushi sannan ya kira Hakeem bayan ya shiga dakinsa.

Akwance Hakeem yake kan doguwar kujera ya rufe idanunshi da tafin hannunshi,gabadaya ranshi babu dadi kuma babu sukuni,saboda gajiyar daya kwaso,awanshi biyu kwata kwata da dawowa daga kasa mai tsarki,yana cikin wannan tunanin yaji karar wayarshi dake kan centre table,kamar bazai motsa ba daga farko sai kuma ya miqe zaune ya na kallon screen din wayar,ganin sunan Umar yasa yajawo wayar ya daga tareda miqe kafafunsa ya lumshe idanu.

"Sojan sama ya gajiyar hanya?"yace"alhamdulillah,any progress?".Saida umar yayi karamin murmushi sannan yace "there are lots of progresses,domin yadda kake tunanin lamarin gabadaya bahaka bane,nikaina yabani matukar mamaki mara fasaltuwa,amma karka damu,hakar mu na gab da cimma ruwa".

Deep breath Hakeem ya sauke sannan yace "Allah ya tabbatar mana "da haka sukai sallama saiya dora wayar akan kirjinsa tareda lulawa duniyar tunani wanda ke saka zuciyar shi yin zafi dakuma quna,tunanin dake kashe masa duk wata kwarin gwiwarsa,ba akan kowa yake tunanin ba sai Heekmah,she's his only hope amma abubuwan gabadaya sun canza.

Saiya miqe yana amsa kiran daddy,bayan sun gaisa daddy yace"yaushe zakazo kano?"yana shiga bedroom dinshi yace"gobe insha Allah "Allah ya kaimu cewar daddy sannan ya katse wayar,kayanshi ya shirya kala biyar kasancewar flight din safe ne sai tsarabar dayayi mai yawan gaske.

Washegari karfe goma na safe flight dinshi ya sauka,kamar yadda sukayi Aliyu ne yaje daukosa,da mamaki yake kallon yadda Aliyu ke cikin tsantsar farin ciki dakuma annashuwa,yace"Aliyu kana cikin farin ciki,tabbas akwai abinda yafaru wanda banda masaniya akanshi".

Ya washe baki sannan yace"kwarai dagaske,Kasan an fasa auran sultana da dr shuraim ko?"ya dan waro idanu waje sannan yace"banida labari".Sai Aliyu ya jinjina kai sannan yace"he was accusing her ,Abin  dai babu dadin ji,haka ya dauki lefen shi ya tafi bayan already an buga invitation card,shine fa daddy yace aure babu fashi".

SULTANA...Where stories live. Discover now