PAGE 29-30(end of book 1)

187 17 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

         Wattpad @Zaynab_yusuf

         Exquisite writer's forum.

               PAGE;29&30

   Jikina na rawa k'afata na hardewa na karasa inda yake,yayi saurins goge hawayen da fingers dinshi guda biyu batareda kowa ya lura ba,cikeda mamaki nace"Meya faru?miye sanadin zubar hawayenka?"na yi tambayar da Aliyu kadai ne ya jita,bai yi magana ba,sannan bai daga ido ya kalleni ba,hasalima miqewa yayi yashiga dakin gwaggo cikin wani irin yanayi,wanda ni kadai na fahimce sa,hanyar dakin gwaggo nayi naji muryar daddy ta daki dodon kunne na,"Ina zaki?dawo kibamu amsa,ko duk cikin kunyar ce?"yafada cikeda zolaya abinda bai fiye yiba,saina juyo tareda sakin karamin murmushi ganin fuskar daddy akan tawa yana min dariya,rufe fuska nayi nashiga dakin gwaggo inda Aliyu ke zaune ya rafka uban tagumi,hawaye masu zafin gaske na zubo mishi.na zauna daf dashi tareda zuba mishi daradaran idanu na.

Daddy yace" Allah sarki sultana akwai kunyah alamar ta yadda kenan".gabadaya iyayena maza sun dauka abin nan danayi alama ce na cewar na amince da dr shuraim,dan haka babu b'ata lokaci daddy ya amince sannan yaba dr shuraim damar turo magabatansa,amma da sharadin saina yi candy zaayi bikin.Lamarin baima gwaggo dadi ba ko kadan kamar yadda baima Mami ba,ana gama maganar tamiqe jiki ba kwari takoma part dinta cikeda tsantsar damuwa,tuna cewar rabonka baya wuce ka datayi ne yasa taji sassauci acikin ranta,domin Idan sultana rabon Aliyu ce ko mutanen farko dana karshe zasu taru akan basaso aurensu sai ya tabbata,sannan idan ba rabonshi bace ko mutanen farko dana karshe zasu taru su tsaya mishi bazai aureta ba.Saidai zata yi iya bakin kokarinta akan hakan duk da daddy ya amincewa dr shuraim.

Murya na rawa nace"Aliyu fada min damuwarka".ya dago da jajayen idanunshi ya saka su cikin nawa sannan yace"damuwata ba matsalar ki bace sultana,domin da kin damu da damuwata datuni kin samo min mafita".

Tace"a Ina zan samo maka mafita bayan Bansan mecece exact problem dinka ba".
Yace"you're my problem sultana,ke ce matsala ta kuma damuwata".
Hawaye masu zafi ne suka zubo min,nace"taya akai nazama matsala acikin rayuwarka?"

"Ta yadda akai kika sace zuciyata shekarun baya dasuka wuce,ta yadda sonki ya gina shekarsa acikin zuciyata,yake ta kaikawo acikinta,cikin zullumi,da hargitsewar rayuwa,cikin ruwa,rana inuwa zafi dakuma quna,Ina fama da wannan halin kika fara Soyayyah da Al'ameen,wannan lamarin ne yayi  breaking heart dina matuka,haka nayita jigilar sonki dakuma kaunarki,Ina jin haushi dakuma zafi mara fasaltuwa akan relationship dinku,saide babu yadda zanyi,haka na hakura nacigaba da rainon sanki har lokacin da Al'ameen ya rasu,Alokacin danake sa ran samunki ne dr shuraim yashigo cikin rayuwarki,kafin nayi wani kwakkwaran motsi har ya bayyana kanshi,dayake nakasance mutum mara sa'a kuma mutum mara rabo".yakarashe maganar tareda miqewa zai fita,nayi saurin shan gabanshi ina kuka mai tsanani dakuma karfi.

Bakina na rawa nace"Meyasa baka shaida min hakan ba sai yanzu da daddy yagama yanke hukunci?meyasa baka bayyana min sirrin dake ranka ba tun da jimawa?meyasa baka sanar dani ba tun  akaron farko?meyasa kazabi kasaka zuciyar ka acikin qunci da kuma radadin rashi na?kayi kuskure akaron farko sannan ka yi watsi da damar ka akaro na biyu,baka kyauta ba ".!nakarasa fada Ina kuka mai dalili,kukan dana dade banyi ba acikin rayuwata,saboda sam bana son dr shuraim,bana kaunar shi kuma banida muradin zamtowa mata agareshi,maimakon Aliyu ya tsamo ni daga fadawa cikin matsannacin hali,wato ya kubutar dani daga auren dr shuraim ta hanyar bayyana min irin kaunar dayake min,domin ya tabbatar babu ta yadda zaayi nayi rejecting dinshi,he's my first cousin,wanda nake jinshi araina fiyeda gabadaya cousins dina,wanda zan iya aura kobabu soyayyah atsakanin mu,na lumshe idanu tareda budewa Ina kallon Shi,shima kallona yakeyi cikeda karyewar zuciya,yana jin radadin kukan danakeyi har karshen zuciyarshi,yayinda yake tunani mara zurfi gameda ni,nima Ina tunani gameda shi,bakinshi na rawa yace "karki b'ata kyakkyawar fuskar ki da kuka ".

SULTANA...Where stories live. Discover now