PAGE 32

508 25 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

                        PAGE:32

Kwanan mu biyu a asibiti suka sallame mu bayan sun tabbatar da babu wata matsala,Sosai iyayena maza da mata ke iya bakin kokarin su ganin na samu wadatacciyar kulawa dani da twins,ga mai gayya kuma mai aiki yaya Hakeem,shine a sahun gaba wurin nemo min abinda nakeda muradi.

Ammi na zaune a bedroom dinta yaya Hakeem ya shigo,lokacin ina toilet Ina wanka twins kuma anyi musu wanka har ma sunyi bacci,ya zauna yana fadin"Ammi kayan fitar suna fa?".Ammi tace"nagama da wannan,shine amatsayin gudunmawata ".Cikeda farin ciki yace"ALLAH ya saka da alheri Ammi, ALLAH yabamu ikon biya ".ta dan harare shi sannan tace"sai batun suna,shikuma daddy da baba sun dauki nauyin sa,ni so nayi su bar ka da hidimar ".hawayen farin ciki ne suka zubo masa,Ba komai yake ma hawayen ba sai iyaye nagari da ALLAH ya azurta shi dasu,yace" ALLAH ya saka da alheri,nasa an kawo abin yanka,shanu biyu da raguna biyu,sunyi haka?".

Dariya Ammi tayi tace"sunyi daidai baban twins,ALLAH ya raya Amir da Amira".Yace Amin yana sosa qeya alamar kunyah,adaidai lokacin na fito daga toilet jikina daure da babban towel,idanu yaya Hakeem ya zuba min ganin wani irin kyau dana qara,su Ammi kullum sai sun magantu da maganar kyan da jego yamin mara fasaltuwa,nima kallonshi nayi tareda sakin karamin murmushi sannan na zagaya ta dayan Gefen na zura hijab dina dogo ina kallon Amir da Amira cikeda sha'awa dakuma birgewa.

Ranar suna tun asubah kowa na gidan ya tashi banda ni da yaran damuke ta faman bacci abin mu,acikin bacci naji an kama lips dina yana kissing dinshi passionately,ahankali na bud'e idanu tareda saukesu akan fuskar mijina wanda yake sakar min murmushi mai birgewa,na miqe zaune Ina cigaba da kallonshi,yace"good morning baby maman twins".na danyi karamin murmushi nace"morning baby daddy "yace"tashi ki shirya mai hoto yazo".kamar yadda yafada na miqe na shiga wanka,shima fita yayi daga dakin yakoma part din gwaggo ya yi wanka ya shirya cikin wata farar shadda kamar yadda nima nasaka farin lace,yaran ma fararen kaya Ammi tasa musu,afalon daddy aka mana hotunan masu bala'in kyau,har gajiya nayi da canza kaya,amir da amira kuwa da kuka aka gama.

Dakin Ammi nakoma na cire kayan sannan na zauna Ina shayar da Amira,wayata dake gefe na dauka Ina pressing,shigowar yaya Hakeem ce tasa na daga ido na sama ina kallonshi hannunshi riqe da wasu documents,ya zauna yana murmushi yace"Amira chop chop".
Nace"ai kai ta gado".ya dan waro idanu yana kallona sannan yace"bakomai mama na kiyi komai Ba komai,babanki ya tsaya miki"yafada yana shafa kan Yarinyar,hannu nasa na karbi documents dinda ya miqo min,yace"na bud'e musu account tun ranar da aka haife su,sannan na zuba musu hannun jari masu yawa ,zan miki bayani ina da ina nan gaba Insha Allah,na siya musu filaye sai kuma ke na sai miki mota amatsayin kyautar haihuwa ".wani hawayen farin ciki mai zafi ne ya zubo min,na ajiye amira agefe na rungume yaya Hakeem iya karfina,yace"karki damu ,sultana Ina son muryar ki ta zamto abu na farko dazan ji akowacce safiya Idan na tashi a bacci,ina son nazama cikin tunanin ki akoda yaushe,a kullum kuma akoda yaushe inason naji kince kina sona da muryar ki mai ratsa zuciyah wacce take sani shiga duniyar masoya batareda na shirya ba ,Ina son ki tabbatar min da Ni ne ma'anar soyayya domin kece ma'anar soyayya awurina,zan so nazama acikin kowani alamura naki dan haka komai zakiyi komai qanqantar shi ki fadamin kamar yadda nake fada miki,Nayi alqawarin zan so ki zan kuma kaunace ki tamkar raina saboda na aminta da soyayyar mu nada matukar karfi ,kuma kishi,tsanani,wuya da duk wani banbancin dake tsakanin mu bazasu karya ta ba,Idan har na taba bata miki rai ko yaya ne kifada min domin na baki hakuri kuma kema Ina fatan zakiyi hakan,wannan ne kadai zai sa tarayyar mu tazama raina kama da saura, ALLAH yakara mana zaman lafiya yaraya abinda muka haifa da wanda zamu haifa nan gaba".

Hawayen farin ciki suka zubo min,alokacin kalamai sukai min karanci,sai kawai nayi owning lips dinshi kissing him with all I got,sunan su Amira suna ne wanda ya amsa suna na gaske wanda ya tara manyan mutane da matan top government officials,kayan da dasuka samu dakuma gifts bazai misaltu ba,sun samu halartar mutane dayawa ciki harda dr shuraim da jidda wacce take dauke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe,ansha shagali kamar biki haka mutanen yola suka zo,munyi kyau nagani nafada haka suna ya tashi sai san barka.

4 YEARS LATER....

Sanye nake da farar long gown wacce akama ado da florals,kafata sanye da white color high heels as well,na dauko graduation gown dina na dora akai,Ina cikin gyarata yaya Hakeem ya shigo hannunshi duka biyun riqe da amir da amira yan shekara uku da rabi,yaran masu qiba gwanin ban sha'awa suka shigo suna fadin"mummy we're done,let's get going ".Murmushi na musu tareda dora motar board ina kallon yaya Hakeem wanda yake kallona cikeda birgewa,pictures yamana clicking masu yawa yana shafa pregnancy bump dina dan wata hudu wanda ya b'ullo kadan,direct wurin graduation din muka wuce sai video call mukeyi dasu Ammi,awannan ranar na kammala medicine and surgery na fito da first class honour.mun sha pics musamman su amira da kowa ke son daukar su,baban su ne ke hanawa sometimes saboda bakin mutane.

Gagarumar walima su Ammi suka hada mana a kano,washegari muka wuce,Aliyu ne baban ayman da ayma yazo daukar mu,nan suka hadu dasu amira suka fara kiriniya,a babban falon gwaggo muka tarar da iyayen mu azazzaune,ga qannen mu dake kasa suna ta murmushin ganin mu,muka zauna daddy ya ce"Alhamdulillah da ALLAH yakawo mu wannan rana mai cikeda alheri dakuma albarka,hakika mun shiga cikin yanayin rayuwa amma alhamdulillah yanzu yazama tarihi,fatana shine mu qara riqe junan mu hannu bibbiyu,familyn Muhammad modibbo yazamto tsarkakekken family wanda za a riqa koyi dashi,tareda yaduwar zumunci ta hanyar aure tsakanin junan mu,ALLAH ya daukaka Muhammad Modibbo family".muka ce Amin,yayinda muka cigaba da gabatar da taron cikeda tsantsar so dakuma kaunar juna.





*Alhamdulillah nan nakawo karshen littafin Guguwar Zamani,kuskuren dake ciki ALLAH ya yafe min,ALLAH ubangiji yasa  alqalami na yazama tsarkakekken alqalami wanda zai amfane mu dani daku baki daya,Labarin Guguwar Zamani is fiction,ni na qirqiresa dakaina,dan haka Idan yazo daidai da rayuwar wani hakan yafaru ne bisa ajizanci na dan Adam,fatana shine abinda na rubuta ya amfane mu gabadaya.*🤝🤝🤝

*Wannan Labarin gabadaya sadaukar wa ne ga SAFIYYA MAHMOUD, ALLAH ya saka da alheri,Nagode kwarai da so da kuma kauna, ALLAH ya raya areef da sauran qannenshi masu zuwa nan gaba Insha ALLAH *🤝🤝🤝

*Godiya Ta musamman ga MEENAAJOOH,Alherin ALLAH ya kai miki a duk inda kike,nagode kwarai da so da kauna🤝🤝🤝*

*Jinjinar ban girma ga GUGUWAR ZAMANI FANS,da bazar ku na taka rawa,ALLAH ya saka muku da mafificin alherinsa yabar mana zumuncin mu na har abada*🤝🤝🤝

*Dole na ambaci SAFIYYA UMMU FAISAK,AMRATH AMRATH,FATY MB,AMINA,na Guguwar Zamani fans,da kuma MMN YUSRAH(ta Sadnaff novels).Nagode da so da kauna*🤝🤝🤝🤝

*Masu posting a groups daban daban ina godiya Sosai da Sosai,musamman RUKY JEGA,ALLAH ya saka miki da mafificin alherinsa.*🤝🤝🤝




*✍🏼ZAYNAB MOHD YUSUF 🤝🤝🤝ke muku fatan alheri,sai mun sake haduwa acikin littafi na mai suna MATAR MUTUM....labari ne wanda salonsa da kuma tsarin sa ya fita daban da saura,a very unique story line,labarin mai dogon zango ne,tafiyar mai tsayi ce,mai girma ce dakuma fad'i,nabar ku lafiya.*🤝🤝🤝

SULTANA...Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ