PAGE:21

146 19 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

        Wattpad @Zaynab_yusuf

        Exquisite writer's forum.

                     PAGE:21

   Da hanzari na saka kwayar idanu na cikin nashi Ina kallo cikeda mamakin furucin sa wanda suke gab da zama silar tashin ciwona,na dafe kirjina dake bugawa cikin rashin kakkautawa,rashin darajar tawa takai haka?sannan ma Miye laifina aciki?me namata?nayi tambayar da banida amsar su.

"ke kurmar ina ce?nace ki bar min daki,zaman me kikeyi ?"ya kara wurgo min tambayar data sa na dauke idanuna Daga kan fuskarshi,wacce take kara hura wutar tsanarshi acikin zuciyata,kaina ne ya fara juyawa kadan kadan,sai nayi saurin dafa bango nabar cikin d'akin,Allah kadai yasan abubuwan da zuciyah ta ke raya min mabanbanta.d'akin mu nakoma cikin fushi mai tsanani kuma bayyanan ne,gwaggo dake kishingid'e tana shan fruits ce ta kalleni tareda kawar da kanta gefe,Tak'i  tambaya ta abinda yafaru ne saboda ta tabbatar yaya Hakeem ne ya b'ata min rai.

Kwanciya nayi rigingine Ina danasanin zuwa na kaduna,da irin wulakancin daya min saboda wata banza,Dama I didn't expect him to treat me rightly,nasaki ajiyar zuciyah Ina kallon wayata tana vibrating,kallon gwaggo nakarayi lokacin ta lumshe idanu saide I don't think bacci takeyi,ahankali na sauko da kafata na miqe,Varander naje na tsaya tareda jingina da bango sannan na daga wayar"Al'ameen "nafurta cikeda tsantsar b'acin rai,Sosai kiran sunanshi danayi yabashi mamaki mai tsanani,koda wasa ban taba fada ba sai yau,dan haka ya tabbatar akwai matsala,ad'an birkice ya kara sassauta murya yace"beauty na meke damunki?waya taba min ke?Who dare to do so?".

Nace"yaya Hakeem,mutumin daya kasance mafi girman wanda na tsana acikin duniya ta,shine ya bata min rai sannan ya ci min mutumci".na karashe maganar Ina kallon flowers dake kad'awa ahankali kasancewar yanayin sanyi da ake ciki,garin yayii dadi Sosai,mutane na wucewa nikuma Ina kallonsu ina kuma waya da Al'ameen wanda bai barni ba saida ya yaye min dukkanin damuwar dake raina,ahankali na sauke wayar Daga kunnena ina tunanin ya rayuwata zata kasance Idan ba Al'ameen acikin ta?Kiran da gwaggo ke kwalla min yasani komawa ciki batareda na shirya ba,saide ga mamakina naga mama zaune agefen gado tana kallon hanyar fita,har kasa na tsugunna sannan nace "gani"batareda ta kalleni ba tace"sameni a daki"tana gama fadin haka ta miqe ta fita,kallon gwaggo nayi tareda marairaice fuska,sai naga ta dauke kanta daga gareni tana ma balaraba magana,banida yadda zanyi shiyasa na miqe nabi bayan mama gabana na faduwa,kuma ba ason raina ba,ita kadaice adakin tayi crossing legs tana pressing phone dinta gently,daga bakin kofar nace"gani".

Sai alokacin ta dago ta kalli fuskata tareda sakin karamin murmushi tace"sultana kenan,mai karamar kwakwalwa dakuma gajeren tunani,mara lissafi aduk lokacin da take aiwatar da lamuranta,Ina son na miki wani gargadi ne"zaro ido nayi wanda suka cika da kwalla Ina kallonta,naji wani abu ya ziyarceni wanda na dade ban ji shiba acikin lokaci mai tsaho,kallonta danayi ne ya rage min wasu abubuwa acikin raina,musamman rashin son zuwa wurinta alokuta mabanbanta,shigowar ummu da baba ne yasani komawa gefen ummu Ina sakar mata murmushi mai sanyi,nace"sannu da zuwa"saita jani zamu shiga daki tana fadin"zokiga me na siya miki".

Cikeda b'acin rai mama ta ce"zo nan sultana".
Sai muka tsaya cak tareda juyowa muna kallonta da mamaki,tacigaba da fadin"yau zanga wa keda cikakken iko akanki,zo nan nace".

Sakin hannuna ummu tayi abba ya dakatar da ita"sai yanzu kika san kinada cikakken iko akanta?saboda jameela ta suturtata ta nemo mata gata dakuma daraja a idanun Kowa??sai yanzu kika san da ita?toh bari kiji kin makara,domin yanzu Jameela keda cikakken iko akan sultana".na sauke ajiyar zuciyah Ina gasgata maganar baba,batareda ummu tace komai ba tashiga daki nima nabi bayanta,lamarin daya batama mama rai Sosai kenan,ta kalli baba tana huci tace"nasan ba'a hayyacinka kake maganar nan ba,kana cikin duhun asiri,an baka a abinci kaci,an baka a ruwa kasha,ka kwanta akai kuma tashi akanshi,ba laifin ka bane"tacigaba da cewa,

SULTANA...Where stories live. Discover now