PAGE 27-28

163 16 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

         Wattpad @Zaynab_yusuf

          Exquisite writer's forum.

                  PAGE:27&28

      Ajiyar zuciyah ya saukar mai nauyi yana tattara gabadaya courage dinsa awuri daya,ya ajiye wuqar dakuma papar a inda ya ajiye ta jiya,ya dafe kanshi dake matukar sara mishi,yana nazari mai zurfi gameda Abba,sannan ya dauko halayyar abba ya dora ta akan mizanin hankali,hakika Abba kamar uba yake awurinshi dan haka zai yi iya bakin kokarinsa wurin bashi wannan girman acikin bincinken sa,zaiyi kokarin ganin bai fahimci yana bincike akanshi ba,sannan bazai fadawa kowa komai gameda hakan ba har sai ya gama tabbatar wa.

Amma mecece ribar Abba Idan familyn su ya tarwatse?menene dalilin saran b'oyen dayake musu?Menene dalilin salwantar da rayuwar Nurain,d'an yayanshi wanda suke uwa daya uba daya?mece ce ribarshi Idan arzikin daddy ya salwanta,mecece ribarshi Idan Asal tazama mara Lafiya kamar mai shafar aljanu?sannan Miye hadinsa da ciwon sultana?sai ya dauko gabadaya problems din gidansu yafara analysing,tabbas mutum daya ne keda hannu acikin wannan lamarin,domin Aliyu da Ayan lafiyar su kalau,duk da ya san bawani son su abban keyi ba,amma ai wata kusar tafi wata,sannan amatsayin shi na babansu komai lalacewa bazai so saka  'yaynshi cikin matsala ba,wannan tunanin ne ya bata ran Hakeem Sosai,wato burin Abba shine yagama da 'ya'yan daddy gabadaya,for what reason?me suka tsare mishi?me daddy ya mishi haka da tsauri dayake son ganin bayanshi?me baba ya mishi dayake wahalar mishi da sultana?sannan ita meta mishi akaran kanta dayake wahalar da rayuwarta?

Ya miqe tsaye yana safa da marwa zuciyar shi nacikin rud'ani mai tsanani,abba fa?someone they consider a father kuma jininsu,Innalillahi wainna ilaihi raji'un,ya furta sanda ya tuna asarar rayuka biyu daya musu ta hanya mafi muni,domin ya tabbatar Abban na amfani da aljanu,wata zuciyar tace"ko kuma yana cultism".gumi ne mai tsananin zafi suke zubo masa,yazama dole ya dasa aya akan ta'addancin da abba ke musu acikin gida,amma how?baze iya aikin nan shi kadai ba,sannan bazai so Aliyu ya shiga ciki ba,domin kome zai faru jini yafi ruwa kauri.!

Juyi Aliyu keyi from one side of the bed to the other,bakomai ke damunshi ba sai tunanin sultana wanda ya addabi zuciyarsa da ruhinsa,saboda tsananin sonta daya kama zuciyar sa da dukkan abinda ta mallaka,shigowar Mami cikin dakin ne yasa Aliyu miqewa zaune,sai ta zauna agefen shi tana kallonshi cikeda tsantsar tausayi irin na d'a da uwa,kaunar yaranta na kara kafa gurbi acikin zuciyarta,tace"Aliyu kai d'ana ne mafi kusanci agareni,na dade Ina ganin kana yawo da damuwa,saide nabaka lokaci ne dan naga iya gudun ruwanka,shin har kayi girman dazaka iya boyemin damuwarka?".
Ta jefa mishi tambayar ta sigar data sa jikinshi yayi sanyi,miye amfanin ko kuma fa'idar rashin fada mata gaskiya?bayan baida kamarta aduniya,saida ya sunkuyar da kai kasa sannan yace"Hakika Ina cikin damuwa mai tsanani Mami,saide damuwata nada wahala wurin bayyanawa,musamman agareki".

Tace"ka cire duk wani shakku acikin ranka ka fadamin damuwarka,ni ce na haifeka remember you can trust your mother".
Yace"haka ne"yana sosa qeya alamar kunyah,batayi dariya ba hasalima sai had'e rai datai tace"Ina sauraron ka".
Saida ya miqe tareda juya baya sannan yace "Hakika Allah ya jarabce ni da kaunar sultana,kauna mai tsanani wacce na dade Ina rainonta acikin raina batareda kowa ya fahimta ba,daga farko nayi tunanin shaquwa ce har sai lokacin da Al'ameen ya shigo cikin rayuwarta,nagane ina sonta ne saboda haushin Al'ameen danakeji mai tsanani,dakuma rashin son relationship dinsu,a airport sanda zamuje bikin anty salma na shaidawa yaya Hakeem sirrin dake raina saboda nasan maganar bazata taba fitowa ba,kamar na binne ne akarkashin qasa,alokacin bai bani kwarin gwiwa ba sannan nima nakasa sanar da ita saboda dalilai Kamar haka,Ina fargabar yadda daddy zai dauki alamarin,dubaga yadda take son Al'ameen,na tabbatar zata kawo shi gida ne,shiyasa na dakata Ina ta zullumin meya kamata nayi,acikin wannan lokacin ne Allah ya karbi rayuwar Al'ameen,she's heartbroken shiyasa bana son fada mata yanzu,Cox she'd definitely say no Dukda irin shakuwar dake tsakanin mu,kinji halin da danki ke ciki for years".
Ya karashe maganar tareda lumshe idanu yana jin masifar kunyar Mami na saukar masa.Hannu tasa ta juyo dashi suka fuskanci juna,tace"dama kasan alaqar ta da Al'ameen?"
Ya gyada kai sama alamar ehh sannan yace"nasani".shiru Mami tayi nawani lokaci sannan tace"nafahimce ka Aliyu,sannan na aminta da maganganun ka,domin I can see that they're coming directly from your heart,sannan from your words kana tsananin son sultana,"ta numfasa sannan tacigaba da cewa"azahirin gaskiya naji dadin wannan maganar, na aminta da ita sannan zan bada gudunmawata dari bisa dari sannan zan shige maka gaba har sai na tabbatar da ka samu cikar farin cikin ka, Allah ya tabbatar mana da alheri "tafada tareda fita daga dakin zuciyar ta fess Cikeda farin ciki mara fasaltuwa.

SULTANA...Where stories live. Discover now