PAGE 24-26

216 20 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

BOOK TWO (2)

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

Exquisite writer's forum.

  
                   PAGE;25-26

   Kuka Sosai gwaggo keyi na baqin ciki dakuma nadamar abubuwan data aikata a baya wanda suka cutar dasu cuta mai tsanani,sai ta dafe kanta tana me jin kunyar abinda ya faru,domin tabbas itace ummul aba'isin faruwar komai,itace ta tilasta ma Daddy da baba qara aure ba ason ransu ba,itace ta uzzura musu har ya kai su ga zab'an tumun dare,suka auro mata marasa tsoron Allah da manzon sa masu shuka fasadi a doron kasa,shiru kowa yayi domin babu wanda yasamu courage din yin magana,saboda tsananin mamaki,Ammi da daddy na kuka Sosai haka mama,domin ta tabbatar itace tabada gudunmawar abubuwan dasuka faru da sultana,Ina cikin halin shock naga ta zub'e agabana tana kuka mai karya zuciyar mai sauraro.

"Ni mahaifiyarki ce sultana,amma na cuce ki cuta mai tsanani,na wulakanta ki na kuma wofantar da rayuwarki batareda hakkin ki ba,dan Allah ki yafe min 'yata,even though banyi deserving hakan daga wurin ki ba,but I'm so sorry"ta fada cikeda tsantsar damuwa,bakin ciki,da kuma takaicin Kuskure daya datayi sakamakon son zuciya, tana jin daman she can go back in time and punch herself for being so heartless,hawayen nadama ne suka fara zarya abisa kuncinta,saina durqusa na rungume ta iya karfina ina jin wani weakness atattare dani.

Muryata na rawa nace"nothing is a mistake,and nothing is something you should regret,it all happens for a reason,there's a purpose for and behind everything,na yafe mi ki mahaifiyata,na yafe miki tuntuni domin baki Komai ba,nima ki yafe min mamana,ummu ta cuce ni,ta cuci rayuwa ta,kin ji abinda tama na ko?"

Daddy ne yayi jarumtar fara magana"Hakika kunyi mana cuta mafi muni,kuma ba mu kadai kuka sab'a mawa ba,kun sab'awa ALLAH madaukaki kuma mabuwayin sarki,gagara misali,azzawajalla"ya saki karamin numfashi sannan yacigaba da fadin "Da farko dai Hadisi ne zan karanta muku Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani."

"BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Karshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.Yazeedur Raqqaashiy ya karbo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa:
Watarana Mala'ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba. Yazo, gaba dayan launin fuskarsa
ya canza. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa "MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA
CANJA HAKA?".Yace "Ya Muhammadu (S.A.W) nazo maka ne
awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta.
Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Kabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa yasamu tsira daga wannan".

Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa "YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA JAHANNAMA TAKE".
Sai yace "Na'am. Hakika Allah madaukakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR.

Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI - FAT!!,Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAKA - KIRIN!!!.
Tana nan har yanzu BAKA KIRIN ce, mai tsananin duhu ce.

Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.Na rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za'a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma'abotan doron duniyar nan sun kone baki dayansu saboda tsananin zafinta.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za'a ratayo tufafi guda daya tufafin 'Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan Ma'abotan doron kasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin Warin wannan Tufafin.

SULTANA...Where stories live. Discover now