PAGE 10

218 18 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺

By Zaynab Yusuf ✍🏼


Guguwar Zamani free book ne,just share domin wasu su qaru dashi.

PAGE :10

        Taro yayi taro kasancewar ta  babbar military school wacce  'ya'yan manyan hafsoshi,commanders,generals,lieutenants dakuma sauran ranks ne dayawa a school din,table din da aka tanadar ma special guest ne centre of attraction,domin anan ne zaa gabatar da gifts dakuma certificates of honour ga best students of the year.

da dan damuwa Ammi tace"nifa har yanzu ban hango Hakeem ba"su mami dake d'aga wuya ma suka ce"muma haka".hakura sukayi da ga baya dan ni aganina banga abun damuwa ba,tunda yana nan din ay zasu hadu,bayan manyan manyan jawabai dakuma nasiha da aka ma graduating students akan zama good ambassadors anan gaba,dakuma dagewa akan ambition dinsu domin they're just getting started.

Award na farko dazaa gabatar shine na best student of the year for the whole school,yaron dayafi kowa kokari,hazaka,neatness,girmama teachers da sauran qualities masu kyau,cikin rashin zato da tsammani akace
"the best student na wannan shekarar yayi zarra Sosai,domin an dade baa ga best student irinsa ba,he's the best among sauran best students na previous years,he's none other than Abdul-hakeem mukhtar Muhammad modibbo,ahankali ya dago kanshi yana kallon mc dakuma wurin daaka tanadar wa baqi,kallo daya yayi ma wurin ya kawar dakanshi tareda miqewa lokacin mc na kara fadin"Abdul-hakeem mukhtar Muhammad modibbo come forward ".

Cikin takunsa mai daukar hankali da jan raayin masu kallonshi yake tafiya,tsaho gareshi Sosai Hakan yasa uniform din yakama jikinsa,fari ne Sosai na ajin karshe,kwantacciyar sumar sa datayi luff ita kadai ma abar kallo ce,gabadaya mutanen dake wurin suka zuba mishi idanu cikeda tsantsar birgewa,kowa ya yaba mishi kasancewarsa mai farin jini.

Da murna Ammi ta ke fadin"alhamdulillah "hawayen farin ciki na zubo mata,Hakeem yazama saurayi mai cikeda kyau,kwazo,da hankali,ita kanta tayi mamakin girmansa domin bazaa ce ta haifesa ba,tana cikin wannan tunanin mc yace"iyayensa should come forward ".

Hakika yau rana ce ta farin ciki da annashuwa agaresu,Ammi da daddy suka miqe cikeda birgewa,mamakin ganinsu yayi tareda sakin murmushi alokaci daya,suka karaso suna murmushin nasara,suna alfahari da samun d'a kamarshi.

Gold medal wani babban soja ya rataya mishi a wuyansa,ajikin medal din an rubuta best student of the year,sai certificate da kuma qaton box da gifts aciki,sukai posing akai musu hotuna masu kyau,da murmushi Ammi da daddy suka rungume shi alokaci daya suka ce "we're proud of you hakeem".

Mc ne ya bukaci dasu koma mazauninsu domin gabatar da wasu kyautar,bai karasa zama ba akace"yanzu zamu bada award na best student of each subject ".

Mc ya Cigaba da fadin"our Chemistry best student is Abdul-hakeem mukhtar Muhammad modibbo ".

Ajiye gifts dinsa yayi akan kujera yakoma,Wannan karon gwaggo ce tazo sukayi hoto tana fadin"Ina alfahari dakai Hakeem, duk da naga kazama basamude,Ina zaka kai tsaho haka?toh wallahi ko tsahonka zai kai falwaya baki na bazai mutu ba domin Allah ne ya tsaga min shi".
murmushi ya sakar mata mai sanyi yace"gwaggon mu Kina nan yadda kike"
Tace"da ya kakeson kaganni?"ta tambaya tana riqe haba,dariya tabaiwa kowa na wurin sannan takoma tazauna shikuma ya girgiza kai ya koma mazauninsa.

"Our English best student is....."shiru gabadaya wurin ya dauka yayinda mc ya waro idanu yana kallon direction din hakeem,Saida ya sauke ajiyar zuciyah sannan yace"Abdul-hakeem Mukhtar Muhammad modibbo ".

Ihu da tafi ne ya biyo baya,kowa na mamakin baiwarsa dakuma fasahar shi,mama da baba da ummu ne sukaje akayi musu snapping pictures.

Wasa wasa yaya hakeem ne ya dauki best student ma subjects 7,ana bakwai dinne aka ce naje muyi hoto,saurin kallon daddy nayi bayan yafada haka,na miqe jikina ba kwari Ina kallon yadda hakeem din yazama wani babba,abun ya bani mamaki matuka domin ayanzu yafi kowa tsaho agidan,idanu dasuka min yawa ne yasa na turgude,ikon Allah ne yasa ban fadi ba,ajiyar zuciyah mai nauyi na sauke sannan na karasa gaban su,kanshi na sama ko kallon gefen danake baiyi ba,wani matsifar kyau yakara mai dauke hankalin mai kallonshi,tabbas ya canza matuka,kawar da tunanin nayi daga raina aka mana picture kowa na kallon gefe daban,na dawo ina qunquni shikuma yakoma wurin zamansa suka cigaba da pictures.

Mc ne ya dakatar da maganganun mutane daya cika wurin gabadaya yace"akwai important announcement da zaa gabatar".
Principal din makarantar ya taso wanda yakasance babban soja ya tsaya,saida mc ya daidaita mic din daidai bakinsa sannan yafara magana kamar haka"barkan ku da zuwa wannan taro mai albarka,muna alfahari da iyayen wannan makaranta,muna alfahari da students dinmu matuka,ganin irin dinbin qwazo dakuma hazakar Abdul-hakeem mukhtar muhd modibbo yasa special guest of honor da sauran guest of honours suka bashi kyauta ta musamman,sannan school tabashi nata"

Tafi Sosai akeyi alokacin sannan ya Cigaba dacewa "kyauta tafarko itace wacce hukumar makaranta tabashi scholarship a NDA dake kaduna,makaranta ta dauke hakkin gabadaya school fees dinsa har yagama,sai kuma gift dinsa na biyu wanda aka bashi 1 million naira"wani katon card a dauko Jikin card din dauke da sunan abdul-hakeem dakuma adadin kudin da aka bashi,haka taro ya watse sunata san barka.

K'arfe biyu da rabi muka dauki hanyar kano kowa da tunanin dake ransa,shigar mu gida keda wuya wani abun mamaki yafaru,wanda ko kadan bamuyi zato ba bare tsammani,abunda bamuyi tunanin zai faru nan kusa ba....

SULTANA...Where stories live. Discover now