PAGE 18

166 17 0
                                    

GUGUWAR ZAMANI🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wattpad @Zaynab_Yusuf

PAGE;18

       Kwanan bakin Ciki da takaici nayi wanda ban taba irinsa ba,na dade banji b'acin rai irin haka ba,da tunanin Al'ameen kala daban daban na lumshe idanuna,bacci mai dadi ya dauke ni.washegari yakasance ranar daurin aure,Ina ganin sunata kaiwa da komowa nai musu banza ko motsawa banyi ba,shigowar gwaggo uku dakin tana ganina a kwance,ana hudun ne tace"ke lafiyar ki?"
Nace"aa bana jin dadi ne ",ta rausayar da kai alamar tausayawa sannan tace"sannu Allah ya baki lafiya".kaina yafara ciwo ahankali,tun ina sharewa na fara gumi Sosai sabida fever data riqe ni babu wasa,na runtse idanu ina jin sanyi sanyi hakan yasa ni shigewa cikin bargo ina jan numfashi sama sama,wasa wasa sai ciwo ya rufe ni batareda kowa yasani ba,nayita ambatar sunan Allah ina neman dauki dakuma taimakon sa,"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alul hazna iza shi'ita sahla "adduar da bakina ke fada kenan ina juyawa side by side,kaina da cikina ke murdawa na cize lips din kasa cikeda azaba,kamar kowani lokaci ina cikin wannan yanayin wani wahalallan bacci ya daukeni,na fada duniyar mafarki,wanda akoda yaushe shine sanadin tashin ciwona akowani lokaci(zaune nake a falon ummu sanye da doguwar riga pink color,nayi nude makeup ina sakin murmushi kasa kasa,cikeda murnar zuwan abin kaunata Al'ameen,message yatura min ya sanar min isowarsa,sai kuma naji hayaniya mai firgita tunani dakuma natsuwar dan adam,nafita da sauri naga an zagaye mutum ayashe a kasa,mutanen wurin sai kuka suke,kallo daya naima fuskarshi hankali na yayi tsananin tashi,tayi kaca kaca,jini na zuba ta ko'ina,Ammi na durkushe akasa idanunta sun kafe gabadaya ta kasa koda motsi,zuwan wata mummunar halitta amatsayin ambulance ce ta firgita ni matuka,Irin halittar dana gani a mafarkai na dasuka gabata,bakinta na zubar jini tafara takowa inda nake,ahankali nake ja da baya ina girgiza kai hawaye masu zafi na zubomin,wani irin cafka ta kawo min na kurma uban ihu wanda yajawo hankalin gabadaya 'yan bikin,na miqe zaune gumi ya wanke min fuska,zuciyah ta da kirjina na duka mai tsanani,jikina na rawa yayinda idanuna ke zubda hawaye,ummu ce tafara bayyana ta rungumeni hawaye na zubo mata,Saina fashe da kuka mai tsanani,mai cin rai dakuma karya zuciyar mai sauraro,sannu kawai nakeji a voices din mutane mabanbanta,afuskokinsu naga tsantsar tausayina wanda yayi tasiri azukatansu,Nayi dauriyar daga musu kai duk da naukewar numfashin daze iya riskata akowanni lokaci,zuwan daddy yasa mutane ficewa daga dakin aka bar iya family members,cikeda tausayi daddy ya ce"sannu sultana, Allah zai baki lafiya,Jameela samata kaya mu wuce asibiti ".

Cikin kuka ummu tace"anya ciwon sultana na asibiti ne?sai na ke ganin kamar ayi mata maganin hausa".juya kai nayi ahankali domin nikadai nasan irin azabar danakeji ajikina,kamar ana kona ni ta ciki,halin danake ciki yasa daddy cewa"afara na asibitin yanzu,shima zai taimaka,zamu san abinyi daga baya".

Asibiti aka wuce dani lokacin na gama galabaita,fuskar Hakeem kawai nake hasashenta wacce tai kaca kaca kamar yayi dambe da damisa saboda ciwuka,jikinsa na zubar da jini ta ko'ina,wani bala'in tsoron shi ne yayi tasiri agareni na runtse idanu ahankali Ina juya kai,ummu kadai aka bari tare dani,saita riqo hannuna tana fadin"fasbir sabran Jameela,kiyi hakuri hakuri mai kyau,domin ladansa baya misaltuwa,ki yadda da kaddara aduk yadda tazo miki,nasan kinyi hakan domin ni shaida ce,amma kiyi hakuri,komai mai wucewa ne watarana sai labari"
" hakika Rayuwar ki gabadayanta nacikin rudani dakuma hargitsi,rayuwa ce wacce baka isa ka fahimci me kike ciki ba har sai mutum yanada kusanci dake,kuma rayuwace wacce mutane kalilan ke tsintar kansu acikinta,saboda yadda take da tsanani,akan hanyar ki ta tafiya akwai tudu da gangare,da ramuka masu matukar zurfi,wanda Idan kika fada daya daga cikin su fitar ki zaiyi matukar wahala,banyi karatun halayyar dan Adam ba amma nayi tunani dakuma research mai zurfi akanki,rashin kulawar mahaifiyar ki shiya taka muhimmiyar rawar gani acikin rayuwarki,rashin kusancinku ne yazama kamar katanga atsakaninku,uwa itace wacce tafi kowa muhimmanci arayuwar  'ya'yanta,amma mamanki ta watsar da rayuwarki,gashi kina paying price of her actions,dama the victim is always the one suffering".
"amma kinada ummu,dan haka kinada komai,bazan gajiya ba,zan nemo miki magani aduk inda yake,da gumina,da zufata,da kuka na,da kudi na,da karfi na harma da jinina ".

SULTANA...Where stories live. Discover now