PAGE 2

527 36 0
                                    

Guguwar Zamani🌺🌺🌺*

      PAGE:2


Guguwar zamani free book ne,just share domin wasu su qaru dashi,kuskuren danayi Allah ya yafe min,my inbox is open for corrections & comments,sannan masu business zasu iya turamin nayi musu advert,just message this no  +918905718352

 

Afirgice ahmadu yafado tsakar gidan yana kiran sunanta cikin d'aga murya,soso da sabulun datakewa ayan wanka dashi ya fadi daga hannunta,ta dafe kirji tana jiran karasowarsa,Tabbas ba qaramin abu ne ke shirin faruwa da ita ba,domin kallo daya zaka masa kaga tsantsar fushin dayake yawo asaman fuskarsa,gabanta sai fad'uwa yakeyi,sunan Allah madaukakin sarki kawai take ambato,katse mata tunanin yay da fadin

"Gargadinki nakeyi Wannan yazama nafarko kuma nakarshe,kika kara kuwa abakin aurenki,domin bazan dauki wannan d'ibar albarkar ba,bazan rashin daraja da halin banza ba,bazan dauki qarya da qazafi ba,shashasha kawai sakara,zakiyi dana sani mara amfani aduk lokacin dawani ya qara tarata da maganarki,sannan zan shayar dake mamakin da zaki deb'i shekaru kina yinsa,ba BUK ba kitafi birnin sin ba damuwata bace,damuwata daya itace bazan dauki halin akuyanci ba".

yana kaiwa nan ya fice daga gidan gabadaya yana me cigaba da bambaminsa.

Ayan dake Tsaye yasanya hannushi ya toshe kunnuwansa yayinda hawaye ke zubo masa,Hakan ce takasance ga Aliyu wanda alokacin yafara jin haushin Ahmadu matuka,tambayoyi yake ma kansa mabanbanta,meyasa babansu baida burin daya wuce sa maminsu kuka,?meyasa yake cin mutuncinta da cin zarafinta akowacce daqiqa na rana?meyasa baya ganin kyautatawar ta?,meyasa baya ganin hakurinta dakuma jajircewarta?meyasa yake ma maminsu haka?meyasa?meyasa?meyasa?he couldn't think of something positive,wani kuka mai cin rai yafara mai ratsa zuciyar mai sauraro,kansa yake bugawa da bango azuciye yana kuma dukan bangon da hannunsa,yanayin Hakan ne kozai samu saukin radadin da zuciyarsa ke masa.

Tabangaren Zainab kuwa durkushewa tai qasa wasu zafafan hawaye na zubo mata, wani irin cin mutunci ne wannan ? wani irin cin fuska ne? wani irin rashin tausayi ne?wani irin rashin tunani ne?wace irin rayuwa ce wannan?a lokaci daya take jin zuciyarta na tafarfasa,rana ta farko datakejin bazata iya qara minti goma agidan ahmadu ba,rana ta farko data ji tsananin haushi sa na yawo azuciyarta,rana ta farko tada qudurta aniyar bar masa gidansa koda zata kwana a titi bare ko bata da iyaye tanada siblings da dangi dakuma aminan arziki,miqewa tai tayi hanzarin karasa MA Ayan wanka tashirya shi tsab,ta jawo boxes guda biyu manya tacika kayanta dasu,tashiga dakin su Aliyu ta hada musu nasu.da kallon mamaki suke binta batareda sunce komai ba,

Kallon Aliyu tayi tace "samo mana napep".

Yace"toh "sannan yafita,babu jimawa yadawo,mai napep din ya taimaka mata suka shigar da kayan sannan yace Ina zamuje,?

Tafada masa sunan unguwar yayinda takejin wata masifar fargaba,ta dafe zuciyarta wacce beats din ke qaruwa da sauri da sauri,ta juya gefenta tana kallon Aliyu wanda ke zubda hawaye tun faruwar lamarin,tausayinsu na ratsa zuciyarta,tanajin takaicin tasowarsu acikin irin wannan rayuwar,rayuwa mai cikeda tsantsar sarkakiya,qunci dakuma baqin ciki,tanajin tamkar ta gaza wurin samar musu uba nagari wanda zasuyi alfahari dashi.

A kofar gidan Yayanta kabir suka tsaya,takalli mai napep tace ".dan Allah bari nashiga nakarbo kudin"

Wani kallon banza ya watsa mata yace"ke mallama karki raina min hankali mana,haka mukai dake kafin na dauko ki?ki bani kudina kafin na miki rashin mutuncin da baki tab'a tunani ba".

Huci Aliyu keyi zuciyarshi na tafarfasa,ya duro daga napep din idanunshi sunyi jajur tamkar garwashi,ya d'aga yatsanshi manuniya yace"babu mahalukin daya isa yaciwa mamina mutunci matukar Ina Numfashi,kayi kadan,koda kuwa duk duniyar nan zasu tsaya maka suzama gatanka saina maida kai abin kwatance kuma dole ka tsaya akarbo kudin ".yana gama fadin haka yajawo Zainab da Ayan yace"shiga ki fito ki barni dashi".

SULTANA...Where stories live. Discover now