PAGE 17

182 24 0
                                    

GUGUWAR ZAMANI🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Written by Zaynab Yusuf ✍🏼

PAGE;17

   Zuciyata ce ta k'arfafa min gwiwa,na kalli fuskar Al'ameen tareda sakar mishi wani irin kallo sannan nace"bye"tareda shiga ciki duk da naji zafin riqe min mayafina dayayi, saina bi ba'asi na kuma ji dalilin yin hakan,da wannan tunanin na shiga bedroom din ummu na kwanta fuskata na kallon ceiling,ban san yadda suka kare da yaya Hakeem ba,ya mishi magana ne Ko kuma bai kula shi ba?na san ma ba magana zai ma Al'ameen d'in ba domin saika damu da abu kake bi takansa.

Kamar yadda tayi nazari haka ya kasance,domin babu abinda Hakeem yacewa Al'ameen saima wucewarsa dayayi tamkar baiga halitta awurin ba,Al'ameen ya sauke sassanyar ajiyar zuciyah sannan ya shiga mota yatafi.bayan mintunan dabazasu wuce ashirin ba Kiran shi ya shigo wayata,dama kadan nake jira nayi picking cikin muryata ta b'acin rai wacce shi kadai yasan da ita.

Yace"ni me ne laifi agareki beauty,amma dan Allah kiyi hakuri,Wallahi ban san yadda akayi  na riqo mayafinki ba,samun kaina nayi da aikata hakan,but I'm really sorry".

Yacigaba"ni ne yakamata nayi hukunci ga duk wanda yay kokarin aikata hakan agareki,dan Allah kiyi hakuri kuma kada kiyi tunanin bana sonki ne,wani abu daban nake mawa,a zahirin gaskiya ke nakeso kuma soyayyahr da zata kaimu ga aure,bazan bata miki lokaci ba beauty".
"Beauty pls say something "yafada akaro na uku,samun zuciyata nayi da gamsuwa da bayaninsa,domin ni shaida ce bai taba min maganar banza ba,da wannan na amince da maganar sa kuma nayi amanna da ita,nace"I trust you my".
Ina jin sanda ya sauke ajiyar zuciyah mai sanyi sannan muka Cigaba da fadawa juna kalamai masu dadi,masu sanyaya zuciya dakuma shaquwa ta hakika.

Washegari tun asubah bamu koma bacci ba kasancewar flight din mu na safe ne,k'arfe 9 from kano to Abuja,saikuma from abuja to yola,k'arfe takwas na safe mukaje Aminu kano International Airport,jikina sanye dawata navy blue gown mai kyau,nayi rolling da black veil sannan na rataya sling bag dina black color as well,dayan hannuna riqe da hand luggage dakuma wayata,cikin lokaci kadan muka gama check in,a departure muka zauna kafin afara boarding...sai na hau whatsApp Ina chatting da Al'ameen,gabadaya hankalinshi ya tashi,

Al'ameen:beauty zanyi missing dinki😞😭😭😭
Sultana;I'll miss you more 🥺
Al'ameen;pls ki kula min da kanki,kuma kar ki manta abinda na fada miki.
Sultana;sure!,bazan manta ba,kai ma ka kula da kanka,banda kallon babes.
Al'ameen;😞,Kinsan you've captured all my veins and nerves,you're my one and true love 💕.
Sultana;😻😻love you my,it's time for boarding,talk later".

Tana kaiwa nan ta kashe data ta rufe wayar gabadaya tana sakin murmushi mai kayatarwa,Aliyu da Hakeem na back seat suna kallon ikon Allah,Sosai zuciyar Aliyu tayi bak'ikk'rin yana jin zafi mara mislatuwa.
Kallo daya Hakeem yamishi yasan yana cikin damuwa,baiyi kasa a gwiwa ba yace"lafiyar ka ?"
K'eyar sultana Aliyu yakalla wanda Hakeem na lura da hakan sannan yace"Ina cikin damuwa,saide lokaci ya kure,babu yadda zanyi, Allah zai yaye min alokacin dabanyi zato da tsammani ba kamar yadda nashiga cikin damuwar batareda na na sani ba".

Jinjina kai Hakeem yayi tareda tab'e baki,kwarai ya fahimci mai Aliyu ke nufi,saiyayi shiru yacigaba da pressing wayarshi,seat no dinshi yakalla 34,yakalli ta Aliyu which is 36,saida ya zauna sannan ya lura ba kowa a 35,nikuma Ina can Ina neman seat 35,Ammi ce tace "kusada Hakeem ne 35"kamar ta watsa min mari haka naji,cikeda b'acin rai da bakin ciki nakarasa,na zauna batareda ya san waye ba,gabadaya I was uncomfortable shikuma ya kawar da kanshi gefe ko sau daya bai kalli side dina ba,naqara hada rai tamkar zan fashe tareda kallon dayan side din nima.

Muna cikin tafiya bacci ya daukeni,mukai landing batareda na sani ba,Hakeem ya wuce abinshi ko kallona beyi ba suka sauka ajirgin,cabin crew ce ta tasheni na farka cikeda mamaki na fita,awaje nagansu sun tsaya cirko cirko suna jirana,abinda yafaru yabaiwa Ammi haushi Sosai,me Hakeem zai ragu dashi dan ya tashe ni a bacci,?ahankali na sauko daga matakalar jirgin gwaggo tace"koni danake tsohuwa ban kaiki kauyanciba,dadi jirgin yamiki haka?".
Bance komai ba muka tafi...sai k'arfe daya jirgin mu ya tashi daga abuja zuwa yola.

SULTANA...Where stories live. Discover now