PAGE 19

161 18 0
                                    

Guguwar Zamani 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wattpad @Zaynab_Yusuf

PAGE;19

Cikeda dakewa yashiga ciki wuta na lasoshi yana runtse idanu cikeda azaba,ga hayaki dayake kokarin rufe mishi idanu,awahalce yake numfashi har ya shiga dakin Asal lokacin ta dade da suma,jini na zuba daga jikinta,da wani mahaukacin sauri ya matsa fankar dake ci da wuta ta fado kasa,yay jarumtar dauko ta kamar baby yafito,bakin kofar ke kara ci da wuta kamar ansaka fetur,cikeda tashin hankali ya waiwaya baya,Gumi masu zafin gaske ke zubo mishi,domin gabadaya wuta ce ke ci gaba da baya,ya runtse idanu yana tunanin shikenan karshen su ne yazo,ya sadakar mutuwa zasuyi gabadaya,hayaki ne ya shaqeshi yafara tari hawaye na fita daga idanunshi,ya lumshe idanu yana ambatar sunan Allah madaukakin sarki yana mai dogaro da imani agreshi,"ya Allah da kai kadai na dogara,ya Allah ka zaba min abinda yafi alheri domin kaine keda ikon komai "ya bud'e idanu da mamaki yake ganin yadda wutar jikin kofar ta dauke tamkar daukewar ruwan sama,saide ta baya na kara ci Sosai,ya miqe cikeda hanzari ya tokari kofar waje,sannan ya dauki Asal yafito da ita,yana fitowa wutar ciki ta karaso bakin kofar,sassanyar ajiyar zuciyah kowa ya sauke,lokacin har masu kashe gobara sunzo,cikin lokaci kadan wutar ta mutu,saide basu tsira da komai ba.

Yana fitowa da ita shima yafadi kasa,Kanshi ya bugu da dutse yafara zubar da jini kadan kadan,asibiti aka wuce dasu cikeda tashin hankali mara fasaltuwa,gabadaya yan gidanmu sun wuce bandani dake falon ummu dakuma Ammi dake bedroom din ummu tana baccin wahala.

Kallon wuri daya yakeyi batareda ya kifta ba,ya daga hannun shi ya dora kan dressing din dake kanshi,ya sauke sassanyar ajiyar zuciyah yana dora nazarin sa kan mizanin hankali,ya fara tunani mai zurfi gameda abubuwan dasuke faruwa agidansu masu kamanceceniya da juna ta wata fuskar,hakika shi musulmi ne kuma yayi imani da kaddara,saide akwai abubuwan dasuka faru wanda suke daure mishi kai suna siyayar da ruwan kanshi,abu nafarko shine rasuwar Nurain wacce tafi kyau adora ta akan scale,gawar Nurain batayi kama da wacce mota ta bige ba,tafi kama da wanda aka cakawa wuqa a ciki,sannan aka mishi lahani a fuska da sauran sassan jikinshi,idan hasashen shi ya zama gaskiya,who's behind his brothers death?miqewa yayi zaune yana nazari gameda halin sultana,tabbas baya san halinta kuma baya son magantuwa da maganar ta,sai de ya zama dole yayi nazari akanta dan tabbas akwai lauje cikin nad'i,ciwonta kadai ya isa ya tabbatar mishi da hakan,domin yafi kama da sihiri kamar yadda yake tunani tun farkon lamarin ,ya kara sauke ajiyar zuciyah yana tunanin who's behind this also?waye yakeda hannu akan abubuwan dake faruwa da sultana?na uku da hudu sune gobarar dasukayi yanzu wacce ta lashe makudan kudin daddy masu yawan gaske,wanda yake son saka hannun jari a wani multinational company dasu,burin daddy akullum shine ya zamto daya daga cikin shareholders din kampanin,sannan baida maganar data wuce hakan,sai kuma Asal wacce aka caki gefen cikinta,ga kuma jinin dake zuba ajikinta,abun daya daure masa kai shine ko kadan wutar bata tab'a taba,hasalima shine yafi shan wahala acikin gobarar,abinda ya dad'a birkita mishi lissafi shine yadda Asal din tafarka kamar sabuwar mahaukaciya,dakuma yadda doctors suka tabbatar musu tayi loosing memory dinta,yanzu komai ya dawo mata sabo..
Miqewa yayi zaune yana sauke kallonshi ya dora akan fuskar Ammi da anty,sai ya tsura musu idanu yana kallon yadda sukayi wani iri gabadaya basa tareda nustuwar su,agefen gadon suka zauna ya kalli Ammi yace"ya jikin Asal?".
Hawaye masu zafi suka zubo mata tace"da sauki alhamdulillah,ya naka jikin?".
Yace" Allah yakara lafiya nikam ai na warware ".
Anty ce tace" Allah ya baku lafiya ya kiyaye faruwar nagaba".
"Amin"kawai yace yacigaba da kallon amminsa cikeda tausayawa.
Sau hudu Ina zuwa asibitin saide koda wasa ban shiga inda yaya hakeem yake ba bare namishi ya jiki,Ammi ce kawai ta lura da hakan amma batace min komai ba,saide lamarin bai mata dadi ba kwarai dagaske.
Ranar da aka sallameshi Ina falon gwaggo na miqe akan doguwar kujera Ina waya da Al'ameen kasancewar ba kowa a part din,abakin kofa ya tsaya yana kallon falon,ganina yasa tamkar ya fasa shiga domin shima baya son hada idanuwa dani Ko kuma ya hadu dani,sai da ya d'age kai sama sannan ya shigo tareda yin sallama wacce Idan bakayi dagaske bazaka jiba,muryarsa tasa nakara had'e rai Sosai,na kashe wayar tareda kifa kaina acikin kujera Ina jin wani abu na taso min,cikin takunsa mai saka mara jin magana nustuwa ya shigo yana d'an dube dube ko zaiga gwaggo,kitchen yafara shiga yafito ya wuce dakinta nan ma bata nan,dakinsa ya shiga ya zauna tareda buga uban tagumi domin abubuwan dake kanshi sun mishi yawa,ga matsalar gida ga kuma convocation dinsu dake gabatowa nan da lokaci kadan,yunwa yakeji mara fasaltuwa,sai ya miqe ya fito falon har yanzu Ina kwance saide fitowar shi tasa na miqe kafafuwana na hardewa na fita daga falon,kitchen yashiga bai tarar da komai ba,sai ya shiga store ya dauko indomie guda biyu zai dafa,muryar gwaggo yaji tace"patient kaine a kitchen?"
Yace"ehh,yunwa nakeji kuma naga ba kowa agidan".
Tace "aa ga sultana a tsakar gida,barin kirawota"batareda yace komai ba tafita shikuma yacigaba da dafawa domin ko ta dafa baci zaiyi ba,Ina zaune akan kujerar tsugunno ta same ni "sannun babbar mara kirki,wallahi ki kiyaye ni acikin gidan nan,kina kallo yayanku ba lafiya bace dashi amma kika kasa dafa masa indomie,ko ba yanzu naga fitowar ki daga bangaren nawa ba?"
Bance mata komai ba sai had'e rai danayi inajin haushi mara fasaltuwa,kamar bazan miqe ba na tashi ta bi bayana muka shiga kitchen din lokacin har ya zuba indomin tana dahuwa,gwaggo tace"koma ka zauna ta karasa".
Yace"aa zan iya"abinda yafada kenan,araina nace kayi ma kanka gwaninta dan wallahi da da bazata ciyu ba inde nina dafa,da karamin murmushi nabar kitchen din gwaggo na bina da rakiyar idanu.

SULTANA...Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz