4

1.5K 129 6
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


                   0⃣4⃣

        Su Marwiyya aiki suke sosai na gyaran gida da girke girke saboda bakin turai da zasuyi, inda Zahradeen kuma yana daki yana hutawanshi amma duk ya kagu su karaso, sun gama abinda zasuyi sun jera a kan dinning sannan taje tayi wanka ta shirya cikin atampa baki me ratsin ja ajiki dinkin riga da skirt me 8pieces sosai tayi kyau tayi kwaliyya duk da yamma ne sannan tasa mayafi red da takalmi da handbag tafesa turare ta fito abinta se zuba kamshi takeyi.



         Shima Zahradeen ya dau wanka cikin black jeans da white Gucci T shirt yayi kyau abinshi, suna idar da sallan magrib suka fito shida Marwiyya saboda iyayensu sunce su suje su dauko su zasu jira a gida. Suna kaiwa airport ana kiran isha saboda haka sukayi sallah a airport din sannan suka fito suna jiransu, announcing sukaji anayi "the flight coming from California will be landing in 10mins time", dadi kashesu tuni fuskansu ya nuna irin dadin da suke ciki bakaman Marwiyya, suna nan zaune har sukaji landing din jirgin aka fara fitowa seda sukayi 15min sannan suka hango su zuwa, Zahradeen na ganin Amatullah annurin fuskanshi ya canza yaja wani dagon tsaki wanda yaja hankalin Marwiyya zuwa inda yake kallo itama gabanta ne ya fadi ganin Abdul Jalil kaman wani arne, badan yana turo mata hotonshi ba daseta rantse bashi bane wani daban ne, shikuwa Zahradeen tuni fuskanshi ya canza kala idonshi yayi ja saboda wani mugun kishi da takaici da sukazo mishi lokaci daya ganin Amatullah da wasu shegun kanan kaya ga ba dankwali se  wani munafukin face cap.



       Amatullah tana hango Zahradeen ta taho da gudu se kanshi ta rungumeshi kam a jikinta tana cewa " I miss u soooo much yayana", Marwiyya data saki baki tana kallonta batayi aune ba itama taji an rungume wanda seda numfashinta ya daina aiki na 30secs sannan ta dawo hayyacinta tana kokarin tureshi amma ba dama, shikuwa Zahradeen bemayi yunkurin tureta ba dan bakin cikin da yake ciki yafi na rungumar da tamai.



      Jin muryansu Mom ne yasa suka sakesu Mom tace "My daughter babu ko welcoming hug uhmm", se a sannan Marwiyya taje ta rungume ta jiki a sanyaye sannan Zahradeen ya gaishe da Dad suka fito waje bayan an loda musu kayansu a booth suka shiga mota dayake Siena ce duk ta dauke su, suka shiga se gida Amatullah se surutu takewa Zahradeen shikuwa kallonta kawai yakeyi sonta da haushinta duk ya cikashi, bangaren Marwiyya kuwa Abdul zama yayi kusa da ita kaman ze shige jikinta duk ta takure hannunta kuwa ya rikeshi gam kaman ance za'a kwace ta, se wasa da barkwanci yake mata itakum banda murmushin da bekai cikiba ba abinda takeyi da haka suka karaso gida.



        Suna parking su Abba da Ummi suka fito cike da murna Abba yaje ya rungume kaninshi wanda ya kusa shekara shida besashi a ido ba, haka Ummi ma ta rungume Mom se a lokacin ta hango hannun 'yarta cikin na Abdul tana neman cirewa amma rikon da yamata ta kasa, basarwa tayi suka shiga gida Amatullah makale da Abba tana gaya mishi grade dinda takesamu a school shikuma se dariya yakeyi yana cewa " I trust my daughter ai akwai kwakwalwa", da haka suka karasa ciki, Mom tace "amma fa se munyi wanka munyi sallah sannan zamuci abinci", Ummi tace " ba damuwa", suka tashi sukayi bangarensu saboda su watsa ruwa, suna fita Marwiyya tace "Ummi kinga yadda su Amatullah suka komawa kuwa", Ummi tayi murmushi tace " kema dai kinsan dole ayi haka, mutum yayi kusan 6yrs a kasan turawa yaci abincinsu, suje school dinsu, suyi kawance dasu ai kinsan dole a rina", ajiyar zuciya Marwiyya ta sauke  zuciyarta tace "lallai inada aiki indai wannan  za'a aure min, shikuwa Zahradeen shiru yayi yanajinsu daga baya kuma ya tashi ya shiga dakinshi.


          Mom da Dad da Amatullah ne suka fito cin abinci banda Abdul sedai yace a cewa Marwiyya ta kawo mishi, suna zuwa suka zauna a dinning nan Mom tace "Marwiyya daughter kaiwa Abdul abincinshi a can", Ummi bataso ba amma ba yadda ta iya haka Marwiyya ta tashi  ta zubamai ta fita gabanta se faduwa yakeyi, ganin Zahradeen be fito bane yasa Amatullah tace " Ummi bari na kaiwa yaya nashi", itama ta tashi tayi dakin  Zahradeen, Marwiyya na kaiwa bakin kofan daki Abdul ta dinga rafka sallama amma shiru ba amsa seta kwankwasa taji yace "come in", a zuciyarta tace " wato sallaman ne baze amsa ba", shiga tayi taga dagashi se singlet da boxer ta kauda idonta daga kanshi tareda cewa "ga abinci", murmushi yayi ya karba ya ajiye harta juya zata fita taji yace " meyasa bakiyi murna da dawowana ba?", shiru tayi seji tayi yaja hannunta ya zaunar da ita kan gado yace "do u know how happy I was, knowing dat I will b coming back to see my wifey but only to find out dat u ar nt even as happy as I am", kallonshi tayi tace " yaya ba haka bane", yace "toh yane", shiru tayi dan batasan me zatace ba, hannu yasa ya dago fuskanta yana kallonta yana lips dinta tuni gabanta ya fara dukan tara tara, ta bude baki zatayi magana sejin bakinshi tayi cikin nata tana yunkurin tureshi amma takasa daga karshe cizo ta gantsara mishi a harshe, da sauri ra saketa yayi gaban mirror yana kallonshi tongue dinshi da har jini ya fara fita, itakuwa banda hawaye ba abinda takeyi da haka ta fita daga dakin tana sharar kwalla, seda ta kusa shiga gida sannan ta goge ta gyara fuskanta ta shiga ba wanda ta kalla tayi dakin ta sukama hira yasa basuma kula da ita ba.



        Gimbiya Amatullah ba sallama tayi dakin Zahradeen taganshi gaban mirror daure da towel se ta ajiye abincin kan table taje ta rungumeshi ta baya da sauri ya juyo dan ganin waye, yana ganin ya haskata da mari yace " bakida hankali ne zaki shigo min daki bako sallama, kuma bari kiji daga yau kika kara rungumeni sena saba miki, shashasha kawai, zaki fita kusai na kara miki", duk cikin fada yake magana ai ba shiri ta fita tana hawaye da kukan tazo tabi gaban iyayenta ta wuce suka kalleta suna lafiya amma ba wanda ta kula.



        Hmmm lallai akwai kwamacala a nan wurin.



TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now