44

1K 76 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

          4⃣4⃣

       Kamar yadda Abdul yayi alkawari yaje amma da kyar suka shawo kanta ta hakura zatayi karatun ba dan tana so ba

        Tin asuba da marwiyya da ta tashi bata koma bacci ba, break fast ta ke ta kokarin hada masu kasan cewar karfe 8 Abdul zai fita, sai da ta gama jera komi a dining sannan ta wuce daki tayi wanka kasan cewar taga 7:00 yayi

      Zahradin ne ya zage yayi masu break fast saboda Ama bata iya girki ba, har ya gama hada komi bata tashi daga bacci ba hakan yasa ya shige daki dan yin wanka

       Bayan Marwiyya ta gama shirin ta cikin gown din da Abdul ya bata ta saka ranar da abokanan sa zasu zo bata saka ba

     Dakin sa ta nufa lokacin ya gama shirin sa cikin suit wadda sukai masifar yi mashi kyau, da sallama ta shiga tare da tura kofar, amsa mata sallamar yayi yana kare mata kallo saboda yadda tayi masifar yi mashi kyau

      Kusa dashi taje tare da gaida shi, hanunsa ya zagaye kugunta da su, kansa ya daura bisa wuyanta "baby na kinyi kyau sosai" gashin kansa ta shafa "ngde mine kai ma kayi kyau, kamar kar na barka ka fita saboda kar a kalle mun kai"

       Jikin ta ya fara shafawa a hankali "baby na ai ni naji ne ke kadai, babu wadda zan iya so, ke kadai naso tin ban San miye so ba har na sanshi, kinga kuwa ke kadai ce mallaki na" ya karasa zancen yana shafa breast din ta

        Ganin yana Neman wuce gona da iri yasa ta juyo dashi "mine muje kayi break fast kaga 8 ya kusa kar ka makara" turo bakin sa yayi "ni wallahi kamar kar na tafi saboda bansan nayi nisa da ke" dariya tayi "nima bnsan yin nisa da kai amma ya zama dole ne mu tafi, ta fada tana ficewa,

      Da kyar ta samu yaci abincin bayan sun gama cin abincin ta rakoshi har motarsa sannan ta juyo gida Bayan taga tafiyar sa

       Sai da Zahradeen ya gama shirin sa tsaf sannan Ama tazo dakin bayan sun gaisa ta mashi iso zuwa dining suna ci suna shan soyayyar su sanda ta rakoshi mota sannan ta tafi gida bayan ya tafi


       Sanda suka je office ana ta zolayar su, a haka suka shige office din su, yana shiga office din, marwiyya ta kira shi, ranar dai ba wani aikin kirki yayi ba kawai waya suka din ga yi


      *BAYAN SATI DAYA*

         Abdul ne kwance kan cinyar marwiyya tana shafa mashi sumar Kansa, idon sa a lumshe ga dukkan alamu yana jin dadin abin da take mashi, cikin kasalaliyar muryar sa yace " baby ki shirya anjima da daddare zamu gida" cikin jin dadi tace "haba" kai ya daga mata alamar "eh" sosai tayi farin ciki

        Da daddare kamar yadda Abdul yace haka suka dunguma sukayi gida, sanda suka isa gida a falon ummi sukayi ma kan su masauki, sosai iyayen suka ji dadin ganin yaran nasu, ranar basu bar gida ba sai wajen goma

        Sosai Marwiyya take karatu dan yau ko abincin kirki bata ci ba tana ta karatu kasan cewar gobe ne zasu zana jamb din su,

       Bangaren Ama kuwa tin jiya zahradeen yake fama da ita kan tayi krtu tace ta yi, ita bata masantawa kanta, sai da yayi mata da gaske sannan tayi karatu

      Tin da sukayi sallar asuba basu koma ba kasan cewar 8:30 zasu shiga exams, karfe 7 sun gama komi har break fast sannan suka dauki hanyar airport road, zahradeen da Ama ne a baya kasan cewar ita za'a fara saukewa, Abdul da Marwiyya kuma a gaba, tin da suka shiga mota Marwiyya addua kawai take Allah ya basu nasara Ama kan danne danen waya takeyi

       Kusa da ita ya matsa kamar zai koma cikin ta yace "swt hrt ki ajiye wayan nan ki dinga addu'a ba danna waya ba" tura baki tayi "yaya addu'a fa nake yi" murmushi kawai yayi dan bayasan suyi rigima

     Sai da suka sauke su sannan suka wuce, bayan Abdul ya kai Marwiyya sun shiga ya nemi gu ya zauna yana jiran fitowar ta, Ama ma sai da Zahradeen ya tabbatar da ta shiga sannan ya zauna zaman jiran ta

       Sai wajen 11 suka fito daga exam din kasan cewar 9 suka shiga, a zaune Marwiyya ta tadda Abdul cikin fara'a ta karasa inda yake zaunen ta zauna, hanunsa ya dora kan kafadar ta "baby ya exam" murmushi tayi ta dora kanta a kirjin sa "yayi sauki sosai kamana  adduar samun nasara, insha Allah zaki ci, hanunta ya kama suka nufo motar su

     Ran ta a hade ta nufo inda yake, yana ganinta ya taso, hanunta ya ruko " baby ya exam" alhamdulilah tace, kan yay magana su Abdul suka zo hakan yasa ya hanunta suka shiga mota


TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now