55

1.1K 78 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

  

                5⃣5⃣



         Abdul seda ya sauke ya a sch sannan ya wuce wurin aiki, Zainab ce ta hango Marwiyya ta karasa wurinta tana dariya tace "yau kuma matar liman aka zamane", murmushi kawai Marwiyya tayi dan taji dadin yadda Abdul ya fara kishinta dan ko nikab yace tasa bazatayi mishi musu zatasa.





       Tare suka karasa hall bayan angama lecture suka fito suka zauna jiran Ama, ba dadewa itama ta fito duk ta galabaita, da anganta ansan tanajin jiki, zama tayi tareda dora kanta kan kafadar Marwiyya tareda cewa " jiri nakeji sosai", sannu suka mata tareda bata ruwa tasha sannan suka zauna dan jirin ya sauka kafin su wuce gida.







        Suna zaune wurin har akayi azahar sannan suka tashi suka shiga massalaci sukayi sallah kafin suyiwa Zainab sallama su wuce gida.






*BAYAN WATA UKU*


        Ama ce zaune a baranda tana chatting a wayanta, gabanta kuma chocolate ne kala kala ga cikinta nan daya fara fitowa, karan bude gate taji tayi saurin tashi ta shiga ciki ta boye chocolate din dan Deen ya hanata sha amma bataji, zama tayi kaman ba ita ba tana jiran shigowarshi.






      Shigowa yayi da ledoji niki niki a hannu ya ajiye a tsakiyar parlour ta mike tana mishi sanda zuwa, ya rungumeta sannan suka zauna yace "wash nagaji", sannu tace sannan ta mike ta kawo mishi ruwa yasha, ta zauna tace " My D wannan kayan fa", murmushi yayi yace "kayan baby ne", kallonshi tayi dan tasan basuyi scan ba tukun ballantana susan gender din baby din.







     Kallonta yayi yana murmushi yace " bude ki gani", hannu tasa ta jawo kayan tana budewa, gabadaya kayan mata ne ba na maza, kallonshi tayi da mamaki tace "My D yanaga kayan mata zalla", kashe mata ido yayi yace " saboda jikina na bani mace ce kuma kinsan instinct dina bayamun karya", girgiza kai kawai tayi tareda cewa "ai zamu gani ko instinct dinka na karya ko bayayi".





      Murmushi kawai yayi ya mike tareda mika mata hannu yace " taso muje, wanka nakeson yi", mikewa tayi ya rike hannunta suka hau sama tare.






       Marwiyya ce zaune a gaban mirror ta zabga uban tagumi tana tunani har Abdul ya shigo bataji ba, karasowa yayi inda take zaune yace "baby meya faru kike tunani haka?, inata sallama bakiji ba", dagowa tayi tareda cewa " yi hakuri bansan  ka dawo ba, sanda zuwa", kallonta yayi sosai sannan yajata kan gado yace "fadamin me matsalanki dan na lura kwanannan kina yawan tunani", rasa abinda zatace tayi dan haka tace " ba komai, tunanin exam dinda zamu fara next week nakeyi", kada mata kai yayi badan ya gamsu ba sedan shi kanshi besonjin abinda ze daga mishi hankali dan yafita damuwa da tunani akan abinda take tunani yanzu.







       Mikewa yayi yace "bari na watsa ruwa nazo", kada mishi kai tayi ya fita tasa hannunta duka biyun a fuska  ta sauke ajiyar zuciya tareda cewa " Ya Allah ka kawo min mafita".





       Tashi tayi ta daura dankwalinta dake kan gado sannan ta sauka dan hada dinning, suna gama cin abinci yace ta shirya suje gida, da murnarta ta hau sama mayafi da waya kawai ta dauka ta sauko.






       Suwa zuwa gida su Abba duk suna nan suma suka zauna anata hira dasu kafin Ummi ta mike ta shiga daki, text tama Marwiyya akan tazo daki,ko minta uku ba'ayi ba Marwiyya ta shiga ciki.






          Wani paper ta dauko ta mika mata tace "gashi in anyi ruwan sama ki tara cup ki samu ruwan sannan ki karanta Fatiha - 70, Ayatul kursiyyu - 70, suratul ikhlas da falaqi da nasi duka kafa 70, se ki karanta la ilaha illalahu lahul mulku wa lahul hamdu, yuhyi wa yu mitu wahuwa ala kulli shai'in kadir shima 70 sannan kiyi niyyan na samun rabo, in ke me rabon  ce a duniya zaki haihu bi izinillahi".






      Wasu hawaye ne suka zubowa Marwiyya kaman daman Ummi ta karanci matsalar ta, rungume ummi tayi tace " nagode sosai Ummi", dagota Ummi tayi ta share mata hawaye tace "base kinmin godiya ba, ki rike addu'a sosai dan duk wanda ya rike addu'a baya tabewa", kada mata kai Marwiyya tayi Ummi tace " muje parlour karsuga mun dade", fitowa sukayi ba dadewa su Abdul suka musu sallama suka kama hanyar gida.





TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now