18

1.1K 86 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


               1⃣8⃣



         Washe gari kamar yadda Abdul yace shi ya tashi Zahradeen daga bacci, masallaci suka wuce, anan suka tadda su Dady suka gaida su har suka shaida masu takwas zasu fice kar su koma bacci, toh suka ce sannan kowa yayi dakin sa.





      Abdul na kwanciya bisa gado yayi dialing number Marwiyya.




     Tana zaune bisa sallaya tana adduo'i, hasken wayarta da ta gani yasa ta dakko wayan ganin mai kira yasa tayi dariya kan ta daga wayan ya katse, zata kara kira kuma sai ga kiran ya kara shigowa dauka tayi tare da karawa a kunnen ta.




      "Aminci Allah ya tabbata a gare ki" tare da kai ta fada cikin sanyaysr muryarta mai dadin sauraro.




      "Kin tashi lpya?" Lpya lau kai fa?" Nima haka" yau baka koma baccin bane" ajiyar zuciya ya sauke ban koma ba kinsan da wuri zamu fita inji Su Abba bayan mun dawo daga masallaci suke shaida mana".




     Hira suka dan taba cike da so da kauna, sannan sukayi sallama dan ganin gari ya fara wayewa.




      Karfe bakwai Mumy da Marwiyya sun gama jera komi a dining, wanka ta shiga daki dan tayi, bata wani jima ba ta fito doguwar riga ta saka bayan ta shafa mai kawai ba tare da tayi kwaliyya ba ta dauro hijab, dan suyi break fast.




      Babu kowa a falon sai Amatullah da take zaune bisa kujera, "sisto ke ce da sassafe haka yau kin riga kowa fitowa" Marwiyya ta fada tana zama kusa da Amatullah, murmushi tayi tace "bari kawai yinwa ce ta fito dani haka kawai naji ciki na kamar me ba shiri na fito" dariya tayi zatai magana Ummi da Abba suka fito gaida su suka yi sannan suka wuce dining suna zama Mumy da Dady ma suka shigo, nan suka gaggaisa.

 

    Sanye suke cikin bakar suit sai faman sheki take  sai shirt din ciki kuma blue, takalmin kafar su ma black, gashin kansu ya kwanta luf, yana ta faman sheki idan ka gansu sai ka rantse ba yan nigeria bane sosai sukayi kyau.




     A tare suka shigo falon tare da yin sallama, ido gaba daya suka bisu da shi saboda yadda sukayi masifar birge su, Amatullah kar da ido take bin Zahradiyn ko kiftawa batayi har yazo ya zauna kusa da ita, sai da ya dan zungure ta ta ankara, murmushi tayi tare da gaida shi ya amsa fuskarsa a sake a hankali ta furta "yaya kayi kyau sosai" murmushin jin dadi yayi yace "nagode".




     Marwiyya kan tin da taga sun shigo ta bisa da ido ganin zata rasa nutsuwarta yasa tayi saurin dai daita kanta tare da daina kallon sa, sanda ya zauna kusa da ita bayan ya gaida su Mumy, ta gaida shi ba tare da ta kalle shi ba.




      Abinci kowa ya fara ci, Abba ne ya lura da Abdul ba ya ci yasa yace "Abdul lafiya naga baka cin abincin kowa ya fara ci" turo bakinsa yayi kamar karamin yaro, "ba komi Abba" murmushi Abba yayi yace "a'a da komi fah ya za'ayi kace ba komi bayan ga damuwa ta bayyana akan fuskarka,



     "Abba babu wanda yace munyi kyau ko dai bamuyi kyau ba, gwamma brother ma Ama tace yayi kyau ni kuwa baby ko kallo na batayi ba" ya fada cikin sigar shagwaba.




      Girgiza kansa Abba yayi dan gaba daya Abdul ya bashi dariya, a zuciyarsa yace yaran yanzu ba kunya wai baby, a fili kuma yace "kayi kyau mana sosai ko Ummi ya fada yana kallon Ummi, murmushi tayi tace "sosai ma".




     Marwiyya kan mutuwar zaune tayi dan gaba daya Abdul ya gama bata kunya, shi ko kunyar nan ta surukai bai iya ba, lalai zata sha fama, kila ma in akayi auren a gaban kowa zaina rungumeta, ita kadai ta dinga zance zucinta.


 

   "Abba to......." Harar da Dady ya makawa Abdul yasa  shi kin karasa me zai ce, kaga malam ka mana shiru kaci abinci, in kai baka da kunya toh ita tana dashi" Dady ya fada, ba shiri Abdul yayi shiru ya fara cin abinci.


   

        Bayan sun gama cin abinci su Dady suka fice matan su suka tafi yi masu rakiya kan suma su shirya su taho Zahradeen da Amatullah ma suka mike ya rage saura Abdul da Marwiyya.


  

      Mikewa tayi zata bar wajen Abdul ya riko hanunta "haba baby na me kuma ya faru da sassafen nan, kinsan fushin ki zai iya bata min wannan ranar tawa" kafa ta bubuga kamar karamar yarinya "ba kaine sai kana ban kunya gaban su Mumy ba" toh ya isa bazan karaba ki dan mun murmushi kinga ana jirana".

     Murmushi tayi tare da furta "kayi kyau sosai" dariya yayi ta rakoshi har kofa ta shige daki dan ta shirya saboda suma goma zasu tafi.




      Zaune take gaban madubi taga shirin ta tsaf cikin atamfa pink mai ratsin baki tayi daurin dan kwalinta yayi sosai dinkin ya zauna a jikin ta riga da skirt.



     Amatullah ce ta turo kofar ba tare da sallama ba tace "sisto daura min dankwali" wow Ama kinga yadda kika yi kyau kuwa" rungumeta Amatullah tayi tare da furta godia.



     Gefen gado ta zauna Marwiyya tayi mata daurin dankwali mai kyau, sosai Amatullah tayi kyau cikin wata atamfa an mata dinkin doguwar riga green mai ratsin orange, dan karamin mayafi orange ta saka sai takalmi orange hotuna sukai ta dauka.



Bayan sun gama hotunan suka sakko falo, anan suka tadda ummi da Mumy ma sun shirya, rufe ko ina suka yi sannan suka fito suka shiga mota driver ya jasu suka tafi.








TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now