14

1.1K 99 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

              1⃣4⃣

      Hanun ta ta janye daga nashi, kwanciya tayi bisa gadon sannan ta lumshe idanun ta, a zuciyar ta take addua Allah yasa ya canza, Allah kuma ya bata juriya da hakurin kasan cewa dashi.


     Maganar sa ce ta katse mata tunani "babyna bacci zakiyi?" Ya tambaya yana dora hanunsa bisa nata.

 

     Bude idanunta tayi ta sauke su akan nasa, "no ba bacci zanyi ba kawai dai na kwanta ne".

     "Na dameki koh, shiyasa zaki kwanta, ko kuma dai fushin kike har yanzu baki hakura ba".

     Murmushin takaici tayi tama rasa me zata ce mashi maganganun sa ne na jiya suka fara dawo mata, ba tayi aune ba hawaye suka fara wanke mata fuska.


    Cikin tashin hankali yayi saurin goge mata hawayen "baby jikin ne, ko kuma nine na maki abu".



      "Yaya dan Allah ka kyale ni na samu nutsuwa tukunnah ban san hayaniya yanxu kar ka dameni da magana".


     Jiki a sanyaye yayi shiru yana kallonta, mikewa tayi, qur'anin da ta gani a gefenta ta dauka, karatu ta fariyi a hankali wanda ita kadai takeji, tayi haka ne ko zata samu nutsuwa a cikin zuciyar ta, dan jin tsanar Abul take a ranta.

      Bayan Zahradeen ya sauke su Ummi dakinsa ya shiga yayi wanka ya janza shigarsa zuwa wani hadaden yadi brown yana ta faman sheki.

    A falo ya tadda Ummi, Mumy da kuma Amatullah, suma duk sunyi wanka, Amatullah ta shirya cikin wata doguwar riga red, kanta babu dan kwali, tana kwance a bisa kujera kan ta kuma na cinyar ummi.


       "Na tafi asibitin zan koma" Zahradeen ya fada yana kokarin fita, cikin sauri ta mike "yaya nima zani" girgiza kansa yayi "a'a ki zauna kawai ai ba jimawa zamuyi ba kuma kinga itama jikin nata da sauki".


      Kwabe fuska tayi kamar zata yi kuka tace "plssssss" hararta yayi ya yi ma su ummi sallama ya fice.

      Yana fita ta saka kuka, da kyar su ummi suka rarrasheta tayi shiru.

      Zaune suke babu wanda yake kula wani, Marwiyya kuma na ta karatun ta.

    Turo kofar akayi tare da sallama, kasan cewar ta kai kan aya yasa ta amsa sallamar tare da rufe qur'anin.

Murmushi tayi ma yayan nata tare da furta "sannun da zuwa yaya" shima murmushin ya maida mata "yauwa kanwata ya jikin naki" ya fada yana zama kusa da ita a gefen gadon.


       "Jiki da sauki, ya hanya" alhamdulilah" kallon sa ya maida ga Abdul ya ganshi cikin damuwa a ransa ya furta "bata hakura ba kenan".

       A fili kuma ya furta "Abdul ya mai jikin" murmushin karfin hali ya kakalo "jiki da sauki".


      Hira suka dinga yi sama sama, rabin hirar kuwa Zahradeen da Marwiyya ne ko kuma Abdul da Zahradeen, indai Abdul yayi magana Marwiyya bata cewa komi shi yasa ya ja bakin sa ya tsuke, Zahradeen na lura da su amma ya share.


      Karfe shida likita ya kira Zahradeen ya bashi sallama, godiya yayi ma likitan ya koma.

     Sanda yaje ya tadda su Dady da Abba sun je, nan ya shaida masu an bada sallama toh suka ce su suka wuce sannan su Zahradeen ma suka tafi a motarsa shi da Abdul a gaba sai kuma Marwiyya a baya.


     Su Dady sun rigasu komawa sanda suka koma basu tadda su a falo ba, Amatullah ce kawai zaune.

     Marwiyya ta taso ta rungume sannan suka zauna, Zahradeen ne ya kalli Amatullah yace "Baby ina su Ummi" banza tayi dashi kamar bata ji ba, murmushi yayi dan yasan dalilin fushin.

      "Abdul ga kiran sallar magariba nan, taso mu wuce masallaci, ba musu ya tashi, alwala suka farayi sannan suka fice masallaci.

      Bayan an idar da sallah sun fito daga masallaci Abdul ya kalli Zahradeen yace "Deen, baby fa fushi take dani nasan zai yi wuya ta yafen kuma har sharadi ta samun kuma nace zan gyara amma ko magana bata mun, wallahi ina san ta kaima ka sani, kuma bazan iya rayuwa babu marwiyya ba" ya karasa maganar hawaye na zubo mashi.

     Kafadar sa Deen ya taba "kar ka damu Abdul, kasan halin Marwiyya bata da ruko zata yafe maka amma ka dinga kokarin nisantar abinda bata so, ko baka rage duka ba ka rage wasu".


    Hawayen fuskarsa ya goge yace "Insha Allah zan rage, ka tayani bata hakuri" karka damu ai zata hakura" a haka suka karasa cin gida.



      Sai da suka gama dinner gaba dayan su suka hadu a falo, Dady da Abba na kujera daya, Mumy da Ummi ma kujera daya Zahradeen da Marwiyya na gefen Dady sai kuma Abdul jalil da Amatullah na gefen Abba".

    Dady ne yay gyaran murya tare da furta.......................................................




TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now