24

1K 82 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

              2⃣4⃣


     Washe gari da wuri suka wuce office ko break fast basu zauna sunyi ba kasan cewar suna da ai yuka a office.



        Karfe sha biyu Marwiyya ta shiga kitchen dan hada masu lunch, Amatullah na parlour tana kallo.


       "Sisto ki ta so muyi girki ki koya sai an miki aure kizo kuna fada da yaya akan girki ko?" Marwiyya ta fada lokacin da ta zo wajen Amatullah.




      "Idan munyi auren ya sake ni ko kuma ya kara aure saboda ban iya girki ba bazanyi ba" ta karasa maganar tana hararta.




       Zaro ido Marwiyya tayi "Allah ya baki hakuri ki kuma maida wukan dan ba rigima nake nema ba nikan" ta karasa maganar tana dariya kasa kasa.


       Ganin Amatullah bata da niyyar kara tanka mata yasa ta koma kitchen tana hango yadda zaman auren su zai kasan ce tsakanin Amatullah da yayan nata, kawar da tunanin tayi bayan ta masu addu'ar fatan alkairi ta cigaba da girkin ta.




       A gajiye suka dawo gida hakan yasa kowa yayi dakin sa da yin wanka.


      Abdul ne ya fara fitowa yayi falo, yana sanye cikin kananan kaya riga da wando, babu sallama ya shiga, Marwiyya da Amatullah, Mumy da kuma Ummi ne zaune a falon.

       Iyayen su ya fara gaidawa yana zama kusa da Marwiyya,  Amatullah ta mashi sannu da zuwa ya amsa cikin fara'a ciki tace sannu da zuwa yaya, fuskarsa dauke da murmushi yace "yawwa baby, kin wuni lpya?" Lpya ta fada a takaice kan yayi magana Zahradeen ya shigo fuskarsa a hade bayan yayi sallama ya gaida iyayen nasa, kan dining ya wuce ya fara cin abinci saboda yinwar da yake ji.


      Marwiyya tace "yaya kaje ka ci abinci mana ko baka jin yinwa ne" da ina jin yinwa sosai amma ganin ki kawai da nayi yasa naji na koshi".

      "Abdul bar wajen tinda kai baka da kunya ita tana dashi" Mumy ta fada fuskar ta a daure.

        Dariya yayi ya tashi ya nufi dining shima ya zubo abincin yaci.



          Da daddare bayan sun gama dinner, Dady yace "Abdul yaushe zaku je hado laifen ne tinda kunce baza kuyi a Nigeria ba".


     Dariya Zahradeen yayi yace "Dady bakin hadawa zamuyi anan ba zamu hada a nan kawai dai so muke mu nemo wasu kayan ne sababbi wanda basu zo nan ba" toh yaushe zakuje" sabon watan nan zamuje insha Allah" toh Allah ya kaimu.



Bayan Abdul da Zahradeen sun fita, kowa ya nufi dakin sa, Zahradeen ya hau gado, tunanin Ama dinsa ya fara, daga karshe ya yanke zuwa dakin ta, tana kwance bisa gado yayi sallama tare da shigowa dakin ciki ciki ta amsa mashi.

      Gefen gadon ya zauna ya hade rai itama ta bata fuska kamar bata taba dariya ba.

      "Ke baki iya bawa mutum hakuri ba in kin mashi laifi ba ko?" Murguda bakin ta tayi tace "bayan hakurin da na baka jiya sannan kace baka hakuri ba, korata fa kayi" ta karasa maganar cikin shagwaba.


       "Au shine dan jiya kin ban hakuri shine akace miki yau karki kara bani ko, kina kallo na shigo ko kallo ban isheki ba bare kuma kice min sannu koh" nan dai yayi ta mata fada, daga karshe suka shirya sannan yayi mata sallama ya fice.



         Washe gari Dady yace su Marwiyya su shirya zasu je suyi regstrn na jamb, tin da aka ambaci jamb ran Ama ya baci dan a duniya idan da abinda ta tsana bai wuce karatu ba".


         Bayan su Dady sun fice aka ce Ama ta shirya Ama fur taki ita wai baza tayi ba, ganin da gaske bata da niyyar yi yasa Mumy ta kira Zahradeen ta shaida mashi saboda tasan halin Ama.


      Sanda Mumy ta shaidawa Zahradeen ya nemi alfarma ya baro office ransa a bace ya nufo gida.




TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now