17

1.1K 107 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

                1⃣7⃣

       Koda suka kai gida Amatullah auna kayan ta dingayi kuma duk mata kyau sun zauna mata das ajiki ita da kanta kayan sun bata sha'awa.


       Bayan ta gama aunawa Marwiyya ta tayata suka jera a closet sannan Amatullah da kanta ta zaba wanda zata gobe indan zasu bude company dinsu Yaya.


      Zama tayi kan gado tana "wash, na gaji", Marwiyya ta kalleta tace " aikin me kikayi", "bakiga aikin da mukasha ba yanzu", dariya Marwiyya tayi tace " amma Amatullah baki da dama, jera kayan ne aiki, lallai kinada aiki nan gaba", murmushi Amatullah tayi tace "iyaka kice Yaya, kuma ni indai akan Yaya ne toh ba zan gaji ba", Marwiyya tace " dama ina zaki gaji, ai mutum in yana tareda masoyin shi babu abinda ke gajiyar dashi".


       Amatullah tayi murmushi tace "haka, wai nikam in tambaye ki mana", Marwiyya tace " inaji", Amatullah  da gulma ke cinta ta gyara zama tace "meya hadaki da Yaya Abdul", hararan wasa Marwiyya ta wurga mata tace " ina wuranki", Amatullah tayi fuskan tausayi tace "plsssss tell me my sweet sisto", Marwiyya ta kalleta tace " abin sirri ne, ba zan iya fada miki bahh", da haka ta tashi tace "kinga ni na wuce nasan su Ummi na kitchen bari naje na tayasu", itama Amatullah ta tashi tace " karki fada din, in tayi wari ma ji ai", da haka suka fita zuwa kitchen dan taya iyayensu aiki.


       Koda sukaje iyayensu sun gama saboda haka sukayi wanke wanke sannan suka fito parlour suka zauna.


       Da daddare bayan sunyi sallan isha duk suka fito zuwa dinning dan cin abinci, yadda suka saba zama haka suka zauna sunacin abinci suna aikawa junansu sakon soyayya ta ido, sudai iyayensu ba bakin magana se kallon ikon Allah.


     Abdul ne ya ajiye spoon dinshi tareda dora hannunshi kan kumatunshi elbow kinshi kuwa na kan table gabadaya ya juya direction din Marwiyya banda kallo ba abinda yake binta dashi, Zahradeen ganin haka seya kirkiro tarin karya saboda ya ankarar da Abdul cewar bafasu kadai ke wurin ba, amma Abdul kaman Allah beyi ruwansu ba.


      Su duka wurin kallon ikon Allah sukeyi banda Marwiyya da takeji kaman kasa ya zage dan kunya, Mom ganin abin nashi ba sauki yasa ta kai mishi rankwashi a kai aikuwa ya juyo yace "Mommmmm! Kin batamin beautiful moment dina", tace " au dama kasan damu a nan, ai nazaci ka manta muna nan ne shiyasa kake kallonta kaman baka taba ganin ta".


      Sosa keya yayi yace "Allah bayan zazzabin da ta danyi ta kara kyau sosai", duka wurin kaman hadin baki sukace " uhmm", dansu dai basuga wani kyaun da ta kara ba bayan wanda take dashi kila shine idonshi ke mishi gizo.


     Da haka suka gama duk suka fara mikewa banda Marwiyya da ta kasa motsa kodan yatsa saboda kunya, Abdul ganin batada niyyar tashi yasa yaja hannunta sukabi ta kofan kitchen sukayi waje zuwa garden.


       "Toh mun fito yanzu fada min me matsalan ki", kallonshi tayi cike da shagwaba tace " toh ba kai bane", ta karashe kaman zatayi kuka har hawaye sun ciko mata, da sauri yace "subhanallah me nayi miki", hawayen da take kokarin boyewa ne yayi nasara zubowa tace " kaine kaketa kallona a gabansu Mom da Daddy, bakaji yanda naji kunya ba kaman kasa ta tsage na shiga", ta karashe tareda fashewa da kuka, in hankalinshi yayi dubu ya tashi, riko ta yayi yace "dan Allah ki daina kukan nan, wlh danasan haka kikaji da banma kalleki ba, amma ni a wurina son kallonki ya zamemin kaman farilla shiyasa kikaga I don't want to lose any chance I get to look at ur beautiful adorable face", ya karashe yana goge mata hawaye.


     Kallonshi tayi tace " dan Allah toh ka rage kallona a gaban su Mom", yace "an gama", tareda kallon lips dinta,  yanaso yayi kissing dinta amma yana tsoron abinda ze biyo baya saboda haka ya riko fuskar ta ya bata peck a goshi tareda cewa " I luv u swthrt, can't wait for u to be mine", murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ta na wasa da zoben hannunta.


       Zahradeen ne zaune a kan gado da waya  hannunshi ya kira Amatullah yace tazo yanason ganin ta, tanajin haka tayi sauri ta dauko daya daga cikin kayan da ta karbo daga dinki tasa riga da skirt sosai kayan suka mata kyau ta fashe jikinta da turare amma ta kasa daura dankwalin saboda haka ta yafa shi kawai ta fito, sanda tazo part dinsu ba kowa a parlour saboda haka ta haura sama ta kwankwasa yace mata ta shigo, shiga tayi da sallama ciki ciki kaman bataso aji, shi kanshi gogan besan tayi sallama ba amma ya share yana kallon yanda tayi kyau cikin suturan da yake sha'awan ganin ta dashi.


     "Wow baby na kin ganki kuwa", cike da rawar kai tace " yaya nayi kyau", yace "sosai ma babayn amma baki daura dankwalin ba", tace " yaya ban iya ba", hannunta yaja ya zaunar da ita kan gado yace "bari na daura miki kigani", dariya ya bata tace " kai yaya yaushe ka iya daura dankwali", yayi murmushi yace "sa ido ki gani".

      Ai kuwa tsaf ya daura mata dankwalin sannan yajata gaban mirror yace " kalli can", kallon kanta tayi a mirror din tace "yaya a ina ka koya, kaga yadda yayi kyau kuwa, kamafi Marwiyya iyawa", yayi murmushi yace " karki damu zan kowa miki kema", juyawa tayi tace "ka kirani, me kakeso", yayi murmushi yace " ke nakeson gani kuma na ganki, zo muje na rakaki gida dare yayi, yau inaso nayi bacci da wuri saboda I have a big day tomorrow ", ba musu ta bishi suka fita.



      Suna fitowa compound sukaci karo dasu Abdul, Marwiyya tace " Ama waya daura miki dankwalin nan yayi kyau", cike da murna tace "Yaya ne", da sauri suka kalleshi shikuma ya dauke kai, Abdul ya tuntsire da dariya yace " dan uwa yaushe kazama dan daudu ban sani ba",cikin ko in kula yace "in dai akan Amatullah ne toh ba dan daudu ba, komai ma zan iya zama" sannan yaja hannunta sukayi gaba suka barsu Abdul a wurin.


       Abdul har daki ya raka Marwiyya,seda ya tabbata ta  shiga sannan ya wuce kaman karsu rabu shima Zahradeen haka. Sanda ya shigo ya tarar Abdul ze fita yace "gwanda kaje ka huta karka makara gobe", Abdul yayi murmushi yace " yadda na tashe ka yau da asuba haka zan tashe ka gobe", Deen yayi murmushi yace "Allah yasa", tareda wucewa ciki shima Abdul yayi bangarensu.


TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now