29

1K 86 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

            2⃣9⃣ 


        Abba ne ya fara fito da kafarsa waje sannan ummi, Mumy, da kuma Dady, bayan sun fito su Amatullah ma suka fito nan suka bi gidan da kallo yadda duk yayi ba kyan gani

        Tin da Abba ya fito yake karewa gidan kallo, ganin yadda ginin  gidan ya fara fashewa, gashi babu ko kofa sai labule da akayi da buhu, hawayen da yake boyewa ne suka zubo mashi,


       Cikin tashi hankali Dady ya karasa inda yake tare da goge mashi kwallah dake yawo a kuncinsa, suka yaran gaba daya jikin su sanyi yayi ganin yadda mahaifin nasu ke zubda kwallah, da kyar Abba ya tatara nutsuwarsa ya shiga cikin gidan yaran suka goya mashi baya



       Zaune suke a tsakar gida mata ne su biyu sai yaran su su kusan shida zaune, sai wata tsohuwa da fuskarta ta tartare da tsufa, jin sallamar mutane yasa suka amsa tare da mikewa cikin tsoro,


       "Bayin Allah ina kuke nema Allah yasa ba kwace mana gida zakuyi ba dan shi kadai ya rage mana, wata mata ta fada cikin tashn hankali, kan suyi magana wasu dattijawa su biyu suka shigo duk kayan su sun yage riga da ban wando da ban

       Cikin girmamawa Dady da Abba suka gaida su, cikin fargaba da tsoro suka amsa salaman 

        Daya daga cikin tsafafin yace " bayin Allah bamu shaidaku ba, murmushin karfin hali Dady ya kirkiro yace "kawu Adamu daga nesa muke muna bukatar wajen zama kan kuji labarin m......."

       Maganarsa ce ta makale sanda ya hango tsohuwan zaune wadda da duk kan alamu bata ko Iya tafiya babu sanda

      Tabarma aka dakko masu katuwa aka shimfida a tsakar gidan, a kyamace Abdul da Ama suka zauna, wata sabuwar gaisuwan suka karayi, sannan suka gaida tsohuwan ta amsa


       Abba ne yace "kawu Adamu, kawu Ahmad nasan baku gane mu ba, da farko dai ni sunana Abubakar, sannan kuma umar yaran kanin ku Usman, jin an ambaci Usman yasa gaba daya suka razana musamman tsohuwan

       Kawu Adamu ne yace " Abubakar daman kuna raye kune kuka zama haka, ku duba girman Allah ku yafe mana" ya karasa maganar cikin kuka kawu Amadu ma kukan yake

     Murmushi Abba yayi yace "kawu da bamu yafe maku ba da bazaku ganmu ba" ajiyan zuciya kawu ya sauke wadan nan fa a ina kuka smo su" ya fada yana nuna su Ama"

      Abba yace wannan mata tace, sai kuma wannan matar umar ce, ya fada yana nuna Mumy, wannan sunan sa Zahradin, yaron wajena ne, sai Abdul jalil yaron Umar, Marwiyya kuma ta wajena sai kuma autar su Amatullah ta wajen umar"

       Jinjina kai kawai sukeyi musamman tsohuwar da kyar ta furta Ku yafen yaran nan hakkin kakarku da babanku ke bibiya....." Kukan ta ne yaci karfi ta kasa karasawa "Dady ne yaje ya rike hanunta haba amaryar mu banda kuka komi ya wuce" gaba daya sukai dariya

Abba yay gyaran murya yace "kawu dalilin zuwan mu shine zancen auren yara ne ya tashi mukaga dacewar nuna masu dangin mu muma" gyada kai kawu Adamu yayi "to masha Allah a ina mazajen nasu da matayen nasu suke" Kawu hadin gida zamuyi Zahradin da Amatullah sai kuma Abdul jalil da Marwiyya"

        Murmushi jin dadi sukayi tabbas hakan yayi Allah ya kara hada kanku, kuma munji dadin yadda kuka manta sharrin da muka muku Ku ka rama mana da alkairi, Allah yay muku albarka" Amin kawu"


        Hindatu  (matar kawu Adamu), tashi ki zubo masu abinci, toh mai gida, ta fada tana mikewa "sani ga kudi ka siyo pure water leda daya" ba musu ya karba ya fice

     "Kawu ya akai kuka dawo nan kuka baro gidan baya?" Abba ya tambaya "bari kawai Abubakar tin bayan barin Ku garin nan muka fara shiga damuwa, komi namu ya kare, ga zagin da muke sha a unguwa mun kasa rike yayan kanin mu amma mun cinye masu dukiya, haka mukai ta dai rayuwa watarana abincin da zamuci ma gagarar mu yake,

       Wata rana muna zaune wani mai kudi a unguwar can kasa damu ya nemi mu saida mashi gidan mu muka ki, shine yazo da tawaga aka kwace gidan munaji muna gani muka tattaro muka dawo gidan nan da zama" girgiza kai kawai sukeyi  Kawu yace "niko kun hadu da abokin Abban ku Alhaji Nazifi dan Kwana 2 da tafiyar ku yazo, ko da yaji bakwa nan yaji takaici ba kadan ba dan dai ba yadda zaiyi ne ya hakura"

       Murmushi Abba yayi sannan yace "eh mun hadu nan ya basu labarin yadda suka yi gwagwarmaya har suka hadu da Alhaji Nazifi, mai dakina ma itace yarsa" nan sukai tayin jimami dai ana bada lbrn bayan haduwa daki hudu aka gyara a cikin kasan cewar gidan da akwai  dakunan gidan daya Marwiyya da Ama daya aka sa masu katifar yaran gidan mai dan girma, daya kuma Zahradin da Abdul aka samasu katifar samarin gidan, daya Mumy da ummi aka sa masu katifar kawu Ahmad daya kuma Dady da Abba aka sa masu katifar kawu Adamu duk ba da sanin su Dady ba

        Sanda aka kawo masu abincin basu ci ba nan aka aika aka siyo masu taliya Zainab matar kawu Ahmad ta dafa masu da kyar suka ci kadan



       "Wai sisto a dakin nan zamu Kwana gaskiya da takura, bazan iya Kwana hudun da su Abba suka ce ba" toh miye a cikin dakin dan Allah Ama ki nutsu kar ki nuna masu kyama baza suji dadi ba da la'asar yaya Zahradin sai ya kaimu mall muyi siyaya har muci abinci" da kyar Ama ta yadda sannan suka fadawa iyayen nasu basu masu musu ba sukace Allah ya kaimu yamman


Da yamma suka shirya cikin dogayen riguna bayan sunyi wanka bandakin ma a kyamace sukayi wankan suka fito

     Sallama sukayiwa iyayen suka fice kawu Ahmad na tsokanar su kar su bata Zahradin yace baza su bata ba

      Wannan karan Zahradin da Ama ne a gaba sai kuma Marwiyya da Abdul a baya, suna tafe suna tambaya har aka nuna masu wani hadaden mall wajen cin abinci suka nufa suka zauna bibiyu nesa da juna Zahradin da Ama na ta hira


        Marwiyya da Abdul kuwa sunyi shiru ba wanda ya kula wani sai dai in sun hada ido ya balla mata harara, tin yana bata haushi har ya ma fara bata dariya, ganin tana dariya yasa yace "wa kike wa dariya" bata fuska tayi "kai nakewa" kwafa yayi dawa kike waya dazu har da yi mashi dariya" mur guda baki tayi "ina ruwanka" zaro ido yayi ni kike wa haka saboda kin raina ni koh" yi hakuri toh kaga muna makaranta nice head gurl to shi kuma shine head boi, toh shine ya Kira yayi mun murna wai yaji na kusa aure  ajiyan hrt Abdul ya sauke toh ban hakuri laifin jiya" dariya tayi yi hakuri amma ka daina fishi baka kyau dariya yayi suka cigaba da shan hirar su basu bar wajen ba sai wajen mangariba sannan suka ma iyayen siyayya da matan gidan suka nufi gda




TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now