60

2.2K 92 4
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

  

        6⃣0⃣

*Last page*

*Godiya ta tabbata ga Allah da ya bamu ikon kammala wannan littafin cikin lpya, muna Neman afuwa idan da Wanda muka batawa tin daga farkon littafin har karshen sa*

Muna miko gaisuwar mu ga duk members din kungiyar mu

_Autan eloquence, Muhievert India, Na'irah daughter, Maman Bilal, pure green, Khadija s Dogarai, A.y Indabo, Basira Sabo nadabo, Hasad Abba, Aeeshat Abba, Queen Nadiya, Madeena, Janna jay Allah kara hada kanmu_

Gaisuwa ga duk members din *Eloquence writers fans, Aishams novels 1 nd 2 Mzz dady fans, Queen Ayush and Hawwer saleh  da duk sauran groups din writers

Jin jina gare Ku

*Queen Ayush iliasu*
*Fateema Munnira*
*Miss Ayusha*
*Fateema*
*Mzz Adam*
*Da duk wanda ma bamu kira ba*

       Cikin wata rantsatsiyar rigar bacci ta shirya shara shara ta tsaya mata iya gwiwa, jikin ta ta feshe da turaruruka kala kala, litle ta dauka ta nufi dakin Deen

       A hankali ta tura kofar yana tsaye gaban mirrow daure da towel, Sallama tayi ya amsa mata cikin sakin fuska, litle ta kwantar a kan gadon sannan ta nufi inda Deen yake

        Rungume shi tayi ta baya tana shafa duk wata gaba ta jikin sa, nan da nan Deen ya shiga maida mata martani, ganin idanu na basa su jure kalla ba na baro masu dakin

      Kwanci tashi ba wuya wajen Allah, cikin Marwiyya ya isa haihuwa yau ko gobe,

        Kwance take kan cinyar Abdul yana dan mamatsa mata jiki cikin kasalaliyar murya tace "yayana Allah jin bayana nake kamar zai balle ga marata da take yi mun azabar ciwo"

        "Kiyi hakuri baby na da Ina da dama da na maida ciwon jiki na dan ko kadan bana kaunar abinda zaki sha wuya amma insha Allahu komi zai zo da sauki" ya karasa maganar yana danna bayanta

       Lamo tayi jikin sa tana jin dadin yadda yake mata a haka bacci ya fara diban ta kamar wadda aka chokala tayi saurin mikewa tare da sakin wahalaliyar kara

     Cikin tashin hankali yace "Baby jikin ne bari na kira Deen" ya fada yana dauko wayar sa

       Suna zaune suna kallo Amma hankali Deen gaba daya ba a wajen yake ba yana can wajen Marwiyya,

      Cikin kulawa Ama tace sweat heart naga yau kana cikin damuwa tin safe me ya faru ne" ajiyar zuciya ya sauke "Honey tin safe tunanin Marwiyya nak......" Karar wayarsa yasa kin karasa zancen sa

       Ganin mai kiran sa yasa yayi saurin dagawa "Abdul lpya jikin marwiyya ne" eh Deen ka fito da mota bari na dakko ta" toh kawai Deen yace ya kashe wayar

      "Ama dakko hijab mu tafi" bai jira cewar ta ba ya dauki key din motarsa ya fice yana fita Abdul ya fito rike da Marwiyya da kuma karamin akwati a hanunsa,

      Cikin sauri Deen ya bude masu baya suka shiga, Ama ta shiga gaba   ya ja suka bar gida

        Suna isa asibitin aka karbeta cikin gaggawa, gaba dayan su sun kasa tsaye sun kasa zaune, kana ganin su kasan duk suna cikin tashin hankali

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now