34

1K 72 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*



              3⃣4⃣


        Amatullah ba ita tasamu kanta ba sai wuraren asuba, wahala kam ta shashi a hannun Deen banda kuka ba abinda takeyi.



      Shiya gyarata ya mata wanka ba jimawa ta koma bacci shikuma ya zauna yana kallonta har aka kira sallah.



     Saida ya sake alwallah sannan ya dawo ya tasheta yace taje tayi alwallah. Tashi  tayi amma a daddafe take tafiya har ta shiga bathroom din, gabadaya sai ta bashi tausayi dan shi kanshi yasan be kyauta mata ba.



     Koda sukayi sallah tea ya hado mata mai kauri yace tasha ya bata magani, da kyar ta shanye sannan tasha maganin ta koma bacci bayan tagama mishi sabon shagwaban da ta tsiro dashi.




       Sai karfe tara suka tashi daga bacci sukayi wanka, Deen ya shirya cikin shaddanshi sky blue wanda yasha aiki, itakuwa gimbiyar wando jeans tasa da dan top dinta ta kama gashin ta ba abinda ya dameta (na kalli shamsiyya nace "wayaga amaryar zamani").



      Koda Deen ya ganta murmushi yayi ba tareda yace komai ba sukaji ana buga kofa ya juya yace " kisa hijab in zaki fito", da haka ya fita koda ya duba abinci aka kawo musu daga gida ya karba tareda sallaman maishi ya koma ciki.



  
        Abinci sukaci suka zauna parlour suna kallo suna hira Amatu sai zuba shagwaba takeyi tana narke mai a jiki, shi kuwa shiru ya mata dan Amatu ba'a tabo ta ba ya aka kare bare kuma an tabota.



       Abdul ne ya fara tashi da yaji kiran sallah seda ya mike yaje yayi alwallah sannan ya dawo ya tashe ta.



       Alwallah tayi sukayi sallah sannan ta jingina kanta da bakin gadon tana kallon Abdul dake karatu, har cikin ranta taji dadin yanda yake karatun amma wannan baisa ta sake fuska ba.




      Yana idarwa ya kalleta tace "Yaya ina kwana", yace " lfy lau, ya jikin?", tace "da sauki", yace " toh Allah ya kara sauki", tace "ameen". Da haka sukayi shiru chan yace " swthrt", tace "uhmm" yace "are u still angry wit me", shiru tayi batayi magana ba yaci gaba da cewa " yanzu bazaki hakura ba dan Allah", batare da ta kalleshi ba tace "yaya bacci nakeji, kabari inna tashi munyi magana", da haka ta tashi ta koma ta kwanta shikuma ya bita da ido.




       Gani ba wannan bane zai fishe shi ba seya tashi ta nufi dakinshi yayi wanka ya shirya cikin jallabiya ya kwanta kan gado yana tunanin ta ina zai shawo kan Marwiyya, da haka har bacci ya dauke shi.




  
       Tara da en mintina ya tashi, ya shiga bathroom ya sake wanka sannan ya fito, koda ya shiga dakin Marwiyya bata ciki haka kuma bata bathroom saboda haka ya sauka zuwa parlour nan ma bata nan.



       Mostin mutum yaji a kitchen wanda hakan yasa shi nufan kitchen din, ganin ta yayi a gaban fridge tana dube dube ya karasa a hankali ya rungumeta ta baya tareda dora habanshi kan kafadarta.




         Lumshe ido tayi ta mishi shiru tanajn yanda yake zagaye hannunshi a waist dinta wanda ba karamin effect yake dashi a kanta ba.



        Katse ta yayi da cewa " swthrt me kike nema haka", a hankali tace "inaso na dora abinci ne amma basan me zan dora ba", bude baki yayi zeyi magana yaji ana danna door bell wanda wannan  yasashi sakinta yace " ina zuwa", sannan ya fita ya duba, abinci aka kawo musu ya karba ya shigo dashi sannan yace mata "swthrt ga abinci an kawo", plate da spoon ta dauko, potatoes ne da kwai se farfesun kaza wanda yaji kayan kamshi.




        Tea ta hada musu ta zuba musu abincin amma Abdul kwakwata hankalin shi ba akan abincin yake ba, kallonta kawai yakeyi yanda taci kwalliya cikin atampha dikin riga da skirt ta kashewa kanta dauri.




          Tasowa yayi ya zauna kusa da ita yace.......





TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now